Hausa Articles

Zafafan Kalaman Soyayya 2023 – Read Now For Free

Karanta Zafafan Kalaman Soyayya Na Maza Da Mata

A Wannan Shafin Zaka Karanta Zafafan Kalaman Soyayya Masu Dadi Da Ratsa Zuciya Na Maza Da Mata Wadanda Masoyan Gaskiya Zasu Ringa Amfani Dasu Wajen Kara Inganta Alakar Soyayyarsu Cikin Sauki. Zaku Iya Amfani Dasu Domin Kalaman Sace Zuciyar Budurwar Ne Wadannan Da Zasu Sanya Mace Taji Tana Kaunarka. Sabbin Kalaman Soyayya Masu Dadi A Sarrafe Suke, Kuma Yin Aiki Dasu Zasu Kwantar Da Hankalin Masoya. Kalaman Soyayya Na Iskanci Da Wasu Yan Mata Da Samari Suke Amfani Dasu Wajen Tada Sha’awa Ba. Karanta Kalaman Soyayya Masu Dadi Na Maza Da Mata Sabon Salo.

Kalaman Soyayya Masu Dadi Na Maza Da Mata 2023

Tabbas Soyayya Ruwan Zuma, Sa’annan Kuma Soyayya Da Shakuwa Abune Dake Tafiya A Lokaci Daya. A Duk Lokacin Da Masoyi Yaga Masoyiyarsa Ya Kanji Shauki Da Wani Dadi A Ransa Wanda Ba Za’a Iya Misalta Dadin Wannan Yanayin Ba.

Kalaman Soyyayya Masu Dadi Suna Ratsa Zuciyar Masoyi Ya Gigice Yaji Kamar Shine Sarki. Kalaman Soyayya Na Sanya Mutum Ya Rasa Tunaninsa Saboda Yanayin Da Zai Tsintci Kansa A Ciki. Wasu Kalaman Suka Sanya Masoya Su Shiga Shauki, Suji Tamkar A Wata Duniya Suke Ba Wannan Ba. Wasu Kalaman Soyayya Masu Dadi Idan Ka Turawa Masoyiyarka To Abin Zai Baka Mamaki Domin Yadda Yanayinta Zai Sauya.

Karanta: Download Sani Ahmad Kalaman Soyayya Audio Now For Free.

Kafin Ka Turawa Masoyiyarka Kalaman Soyayya, Ka Tsaya Kayi Nazari Akan Wadannan Kalaman Soyayyar. Shin Kalaman Suna Da Ma’ana? Shin Kalaman Sun Dace Ayi Amfani Dasu A Lokacin? (Domin Kada Kaje Kayi Amfani Da Kalaman Soyayya Na Safe A Madadin Kalaman Soyayya Lokacin Kwanciyar Bacci). Shin Wannan Kalaman Sun Dace Da Ita? Ka Kula, Kada A Yayin Neman Soyayya Daga Wajen Budurwa Kuma Ka Janyo Masifa, Watakila Kalaman Su Bata Mata Rai, Ko Kuma Taga Kawai Karya Kakeyi Mata, Don Haka Ka Kula Wajen Amfanin Da Kalaman Soyayya.

Shiga Nan Ka Karanta 👉 Sabbin Kalaman Soyayya Na Mata.

Kalaman Soyayya

Zafafan Kalaman Soyayya Masu Dadi Na Maza Da Mata - Zafafan Kalaman Soyayya 2023 - Read Now For Free

Wadannan Sune Jerin Kalaman Soyayya Zafafa Sabbi Da Zasu Kara Dankon Soyayya Tsakanin Budurwa Da Saurayi. Hiran Masoya Na Kalaman Soyayya Masu Ratsa Zuciya.

Kalaman Soyayya Masu Dadi

Ga Zafafan Kalaman Soyayya Masu Dadi Da Ratsa Zuciya, Zasu Burge Masoya Sossai. Budurwa Da Saurayi Zasu Iya Amfani Dashi Wajen Hira Domin Inganta Soyayyarsu.

 1. Kinfi Karfin Mata Dubu A Wajena, Shiyasa A Duk Lokacin Da Nayi Sallah Nake Rokon Allah Da Ya Bar Mini Ke A Matsayin Mata.
 2. A Kullum Zuciyata Tana Farin Ciki Da Samun Sahalewar Zuciyarki, Samunki Babbar Nasara Ce A Rayuwa, Kasancewa Dake Babbar Ni’imace, Kallonki Kuwa Babbar Rabo Ce.
 3. Rayuwa Ta Nuna Mana Cewa Duk Abu Mai Kyau Bashi Da Saukin Samu Kamar Kudade, Aiki, Ilimi Da Sauransu. Haka Zalika Soyayyar Gaskiya, Tabbas Nasha Wahalar Samun Soyayyarki, Shiyasa Nake Da Tabbacin Cewa Ke Alherice A Rayuwata.
 4. Farin Cikinki Farin Cikina Ne, Haka Zaklika Bakin Cikinki. Zan Iya Sadaukar Da Duk Abinda Na Mallaka Domin Ki.
 5. Da Ace Na Iya Rera Waka, Da Na Rera Miki Wakar Da Duk Duniya Zasu So Su Saurareta Saboda Kalamai Da Kirarin Da Zan Sanya A Cikinta.
 6. Soyayyarki Ta Kasance Tamkar Numfashine A Gareni, My Love, Bazan Iya Gudanar Da Rayuwata Cikin Farin Ciki Batare Dake Ba.
 7. Ki Tausaya Min, Na Zama Tamkar Mara Uwa Da Uba Sakamakon Soyayyarki Da Yadda Begenki Ya Mamaye Min Zuciyata.
 8. A Koda Yaushe Ina Fatan Budewar Kofofin Nasara A Tattare Dake, Amincin Allah Su Kara Tabbata A Gareki.
 9. Wani Dalili Nake Dashi Da Zan Rabu Dake? Wane Daliline Nake Dashi Da Zanci Amanarki? Banida Kowane Dalili Da Zan Rabu Dake Ko Naci Amanarki.
 10. Kina Da Kyau, Shiyasa Nake Son Kallonki. Kina Da Murya Mai Dadi Shiyasa Nake Son Jin Muryarki. Kina Da Hankali Da Nutsuwa, Hakan Ne Yasa Nakeson Nayi Rayuwa Tare Dake Har Abada.

Kalaman Soyayya Zuwa Ga Budurwa

Wadannan Sune Zafafan Kalaman Soyayya Zuwa Ga Budurwa Da Saurayi Zaiyi Amfani Dasu Wajen Inganta Soyayyarsa, Zaka Iya Turasu Ta Text Message Ko Kuma Whatsapp, Facebook Da Sauransu.

 1. A Cikin Duniya Akwai Kayan Alatu Da Ababen Burgewa, Harma Da Kayan Alatu Dake Jan Hankalin Mutane. Duk Cikinsu Kece Kadai Kike Iya Daukar Hankalina. Na Zabeki Akan Gold, Na Zabeki Akan Diamond, Wallahi Soyayyarki Tafi Karfin Komai A Wajena Masoyiya.
 2. Kowa Yana Da Abinda Ke Sanya Shi Cikin Farin Ciki, Ni Babu Abinda Yake Sanyani Farin Ciki Sai Ke.
 3. Murmushinki Abun Burgewa, Kalamanki Dadin Ji, Sune Abun Saurari, Fuskarki Kyakkwa Abin Kallo, Muryarki Zaki, Abin Tunawa.
 4. A Kullum Godiya Nake Ga Allah Da Ya Bani Ke A Matsayin Budurwa, Kuma A Kullum Rokon Allah Nake Da Yasa Kin Zamto Matata Ta Sunnah.
 5. My Honey, A Duk Lokacin Da Na Daga Wayata Naga Hotonki Sai Naji Zuciyata Ta Buga. Sai Naji Fuskata Ta Sake Koda Ace A Hade Take, A Lokacin Na Kanji Kuzari Yazo Min.
 6. A Yanzu Soyayyarki Tayi Nisa Cikin Zuciyata Har Bana Iya Numfashi Sittin Batare Da Tunaninki Ya Ketaro Cikin Zuciyata Ba, Kema Kina Jin Hakan Dangane Dani?
 7. A Duk Lokacin Da Muke Musayar Kalamai Tsakanina Dake, Kunnunawana Babu Wani Abinda Suke Saurare Sama Da Muryarki. Har Izuwa Yanzu Ban Taba Jin Mace Mai Dadin Zance Da Murya Sama Dake Ba.
 8. Zaki Iya Yi Mini Alkawarin Cewa Bazaki Rabu Dani Ba Har Abada? Ki Taimaka Kiyi Hakan Koda Sau Dayane Domin Naji Sukuni A Raina.

Kammalawa

Wadannan Sune Zafafan Kalaman Soyayya Da Muka Tanadar Muku A Yau. Ga Masu Bukatar A Hada Musu Nasu Kai Tsaye Sai Kuyi Comment. Karanta Soyayya – Abubuwan Da Yakamata Ka Sani Akan So 2023.

4.3/5 - 32 Votes

Hausa Cinema

Hausa Cinema Language Is The Best Website In Africa Delivering The Latest News, Entertainment, Educational Articles And Many More About The Hausa People. Download Hausa Novels, Hausa Music, Hausa Videos, Mod Apks And Many More.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Related Articles