Hausa Tech

Yadda Ake Samun Kudi A Online (Yanar Gizo)

Hanyoyin Da Ake Samun Kudi A Yanar Gizo

Hanyoyi Da Yadda Ake Samun Kudi Online (Yanar Gizo)

A wannan rubutu zaka koyi yadda ake samun kudi a online cikin sauki. Sa’annan zamu sanar da kai wasu hanyoyin da zaka bi ka samu kudi a yanar gizo. Kamar yadda ka sani duniyar yanzu yadda ta zama komai ta online akeyinsa, kasuwancin yanar gizo, cinikin yanar gizo, harma da yadda ake samun kudi a yanar gizo. Ka tabbata ka karanta komai a nitse domai ka fahimci yadda abin yake dalla-dalla.

Da farko shi yanar gizo kamar yadda kowa ya sani waje ne da ba’a zuwa batare da na’ura ba. Muna iya zuwa wajen muyi ta rayuwarmu a ciki batare da wata matsala ba. Domin a yanar gizo mutum yana iya aiwatar da abubuwa dayawa da ake aiwatarwa a duniyar zahiri, irinsu karatu a yanar gizo, kasuwanci, sada zumunci, yaki (war) da sauran kananun aikace-aikace. Shiyasa mutanenmu na yanzu da zaran kaga mutum ya rike wayar hannu, yana iya kwashe yini guda batare da ya daga kansa ba. Wannan matakai ne na farko da ake samun kudade a yanar gizo.

To saidai tambayar anan itace; Dame kake morar yanar gizo? Ana cin moriyarka ne? Ko kuwa kai kake cin moriyarta?

Idan har baka moriyar yanar gizo to yakamata ka bude idanu ka karanta wannan rubutu, domin tabbas zai baka kwarin gwiwar da kaima zaka tashi ka tsaya.

Kudaden Da Ake Samu A Yanar Gizo

Yadda Ake Samun Kudi A Online

Wasu suna tambaya; Da gaske ana samun kudi a online (Yanar gizo)? Kuma tayaya ake samun wadannan kudade?

A maganar gaskiya ana samun kudade masu yawa a yanar gizo. Kuma kudaden da ake samu sun zarce miliyoyin kudade. Domin da ace zan lissafa maka irin kudaden da ake samu a yanar gizo, da zan cinye wannan watan ina rubutu ban gama ba!

Saidai zan baka misali da karamar hanyar da ake samun kudi a yanar gizo wadda itace Facebook. Facebook tana kawo kudi sossai, Karanta Yadda Ake Samun Kudi A Facebook. Zaka iya samun a kalla duk lalacinka bazaka gaza Naira dubu dari a wata ba ta yanar gizo.

Hanyoyin Da Ake Samun Kudi Online

Wadannan sune hanyoyin da muka kawo muku da ake samun kudi a online dasu. Kaima zaka iya duba guda daya ka fara daga yanzu.

  1. Content Writing
  2. Kasuwancin Data
  3. Blogging
  4. Cryptocurrency
  5. YouTube
  6. Facebook Business
  7. Instagram Business
  8. Saya Da Sayarwa
  9. Graphic Design
  10. Tallace-Tallace

Content Writing

Wannan sana’ace babba da na yarda da ita, shi yasa na lissafo ta a farko domin tayi min sutura. Ana samun kudi ta hanyar content writing idan aka mayar da hankali akai. Yadda akeyin kasuwancin kuma shine zaka koyi rubutu game da mawaki ko wani mutum da aka sanshi sai ka sayarwa mai website ya wallafa. Shima wannan content writing din koyonsa akeyi, yana da dokoki da kuma yadda ake yinsa. Saboda haka idan kana bukatar ka koyi wannan sana’a ka shiga contact us yanzu ka turo mana sakonka game da yadda kake ra’ayin kasuwancin, za’ayi maka bayani sa’annan a koya maka ta email dinka.

Kasuwancin Data

Yadda Ake Kasuwancin Data

Kasuwancin Data na daya daga cikin manyan kasuwancin da matasanmu hausawa suke samun kudi da ita. Kasuwancine mai sauki da yake kawo kudi, kuma iya mutanenka iya yadda zaka ringa samun riba. Munyi rubutu game da kasuwancin, shiga nan ka karanta yadda ake kasuwancin data.

Kasuwancin Crypto

Kasuwancin crypto kasuwancine da yake kawo mahaukatan kudade. Amma da shike kasuwancine mai kama da caca mutum yana iya rasa kudaden da ya samu a cikin kankanin lokaci. Kasuwancin kiripto yana daya daga cikin manyan kasuwancin da akeyi a yanar gizo a ringa samun kudade dasu. Saidai kuma kasuwancin tana da bukatar ilimi sossai kafin a shigeta, idan baka da ilimin crypto ka shiga to tabbas zakayita zura asara ne. Idan kanason ka koyi kasuwancin crypto, ko kanason kasan yadda ake kasuwancin crypo, kai tsaye kayi mana magana ta contact us zamu amsa maka ta email dinka.

Blogging

Blogging itace hanya mafi sauki da ake samun kudi a online da ita. Blogging shine ka bude website kamar wannan ka ringa rubutu a ciki mutane suna shiga kana samun kudi. Shafukan BBC Hausa, DW Hausa, Jaridar Aminiya da sauransu gabadaya suna aiki da website, wanda yana kawo musu makudan kudade ta ciki. Karanta wannan rubutun domin ka koyi yadda ake blogging.

YouTube

YouTube itace hanya ta biyu da yawanci mutanenmu Hausawa suke samun kudade da ita. Wannan bayanin ba sai nayita tayi tsayi ba. Idan ka shiga YouTube zaka kalli yadda manyan tashoshin hausawa suke tashe irinsu HausaTop, DalaTop News, Mamaki TV, da sauransu. A gurguje irin makudan kudaden da ake samune a YouTube yasa masu shirya fina-finai suka koma saka fina-finansu a YouTube saboda ribar da ake samu a YouTube ya wuce wasa. Idan kaima kanason ka fara samun kudi a YouTube, ka fara bude YouTube channel. Shiga nan ka karanta yadda ake bude YouTube channel cikin sauki.

Facebook Business

Nasan cewa kawai mutane dayawa suna yin Facebook ne amma basu san cewa ana samun kudi da Facebook ba. Ka taba tambayar kanka meyasa ake sace account na mutane a Facebook? Ka taba tambayar kanka meyasa mutane suke cewa ayi musu like ko ayi musu sharing a shafukansu? To tabbas kudade ake samu a facebook ta hanyar bude Facebook pages, Facebook groups, sharing na hotuna da sauransu. Ka shiga nan ka karanta yadda ake samun kudi a Facebook.

Instagram Business

Shikuma instagram Business kasuwancine da akeyi a shafin Instagram, inda zaka ringa bude accounts na Insatgram ka ringa janyo mutane da zafafan posting suna following din accounts din, da zaran ya kai adadin yadda ake da bukata saika sayar. Zaka iya sayarwa idan ya kai 10K followers wato mabiya dubu goma, ko 5K ko 1K, wannan bisa ga masu saya ne. Amma a wannan harkar anfison masu followers dayawa saboda yafi kawo kudade.

Saya Da Sayarwa

Saya da sayarwa shima kasuwancine mai zaman kansa a nan Nigeria. Yana daya daga cikin kasuwancin da suke kawo kudi. Shi wannan kasuwanci ana yinsane idan mutum yana alaka da masu sayarda accounts na Facebook, websites, pages na Facebook, TikTok account, Instagram accounts, YouTube channels, da sauransu. Idan ka saya kaikuma saika sayar ga masu saya.

Graphic Design

Shima wannan kasuwancine na matakin farko da yake kawo kudi. Amma saidai ga wadanda suka iya zane, kuma suna iya amfani da wayarsu wajen hada logo, editing na hoto da sauransu. Koyon wannan harkar zai baka wahala idan har baka iya ba, amma idan kana tare da wanda ya iya harkar zaka iya koya daga garesa cikin sauki. Amma zaka iya amfani da applications irinsu Pixellab, Picsart da Kuma Adobe Photoshop.

Tallace-Tallace

Itama wannan hanyace da ake samun kudi da ita a yanar gizo. Sai dai kuma zaka iya samun kudine ta wannan hanyar idan ya kasance kana da mutane a shafinka na sada zumunta (Facebbok, Instagram, TikTok, Whatsapp da Sauransu). Kananun kamfanuwane zasu ringa baka tallan abubuwan da basu saba doka ba kana sayarwa. Za’a iya baka tallan kaya, tallan fim, talllan shafuka da sauransu. Tabbas ana samun kudade sossai ta wannan hanyar idan aka jarraba.

 

Kammalawa

Wadannan sune hanyoyin matakin farko na yadda ake samun kudi a online. Akwai wasu hanyoyi da dama irinsu programming, digital marketing, web design, bug hunting, online tutoring da sauransu. Amma wadannan sune kananu da mutum zai iya farawa dasu kuma yaci nasara, amma dole sai kayi hakuri.

Ga me tambaya ko karin bayani kai tsaye zaka iya mana magana ta comment box dake kasa, zamu amsa maka tambayarka cikin kankanin lokaci, mun gode. Kaci gaba da ziyartar shafin Hausa Cinema.

5/5 - 8 Votes

Hausa Cinema

Hausa Cinema The Best Website In Africa Delivering The Latest News, Entertainment, Educational Articles And Many More About The Hausa People.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Related Articles