Yadda Ake Rubuta Wasikar Neman Aiki – You Need To Know Now

Yadda Ake Rubuta Wasikar Neman Aiki Cikin Sauki

Mutane Dayawa Suna Tambayata Akan Yadda Ake Rubuta Wasikar Neman Aiki, (Yadda Ake Rubuta Application Letter Ko Job Letter) Wai Yaya Ake Rubuta Wasikar Neman Aiki Batare Da Ansha Wahala Ba, Shiyasa Nace Zan Kawo Wannan Rubutun Na Musamman Domin Taimakawa Yan Uwana Hausawa Da Hanya Mafi Sauki Da Mutum Zai Bi Wajen Rubuta Wasikar Neman Aiki A Saukake. Dalibine Kai, Malami Ko Kuma Dai Mai Bincike Na Musamman To Da Yardan Allah Wannan Rubutu Da Nayi Zai Matukar Taimaka Sossai, Sunana Aliyu Saidu Jauro, Dalibi Kuma Masanin Yanar Gizo Da Fasahar Zamani.

Yadda Ake Rubuta Wasikar Neman Aiki

Yadda Ake Rubuta Wasikar Neman Aiki

Shi Wasikar Neman Aiki Ana Rubutashine A Nitse Kuma Nau’ine Da Wasika Da Ba’a Bukatar Wasa Ko Kuskure Cikinsa. Haka Zalika, Shi Wasikar Neman Aiki Yana Karkashin Formal Letter Ne (Shiga Nan Ka Koyi Yadda Ake Rubuta Formal Letter Da Dokokinsa). Formal Letter Kuma Wasika Ce Da Ake Rubutawa Manyan Mutane, Kama Daga Minista, Kwamishina, Gwamna, Sarakuna Har Shugaban Kasa. Bugu Da Kari, Ana Iya Rubutawa Manyan Ma’aikatu Da Masana’antu Domin Neman Wata Dama, Shigar Da Korafi, Ko Kuma Neman Aiki Kamar Yadda Zan Nuna A Wannan Shafin.

Rubuta Wasikar Neman Aiki

Shi Rubutun Wasikar Neman Aiki Ya Banbanta Da Sauran Wasikun, Domin Shi Yafi Wahala. Kafin Ka Rubutashi Kana Bukatar Kayi Bincike Akan Kamfanin, Kamar Dokokinsu Da Tsare-Tsarensu. Sa’annan Yana Da Kyau Ka San Sunan Wanda Yake Daukan Aikin Wato Hiring Manager. Yana Da Kyau Kuma Ka San Abubuwan Da Suke Bukata Wajen Qualifications Da Skills Ko Ilimi. Idan Da Hali Ma Kasa Nemi Sanin Awards Din Da Kamfanin Ta Samu Kafin Ka Rubuta Wasikar. Ka Duba Da Kyau Kaga Yadda Ake Rubuta Wasikar Neman Aiki Yanzu Ka Samu Da Yardar Allah.

Abubuwan Da Zaka Tanada Kafin Ka Rubuta Wasikar Neman Aiki

Kafin Ka Fara Rubuta Wasikar Neman Aiki Farko Ya Kasance Kana Da Wadannan Abubuwa:

 1. Sunan Kamfani Ko Sunan Wanda Yake Karban Aikin.
 2. Adireshin Kamfani Ko Adireshin Wanda Yake Karban Aikin
 3. Adireshinka
 4. Curriculum Vitae (CV)
 5. Ssce Result, Fslc, Da Sauran Results
 6. Passport

Abubuwan Da Ake Bukata Wajen Rubuta Wasikar Neman Aiki

Dole Kana Bukatar Wasu Ilimi Kafin Kasan Yadda Ake Rubuta Wasikar Neman Aiki. Wadannan Ilimi Zasu Taimaka Maka Wajen Rubutawa Akoda Yaushe. Sa’annan Wadannan Abubuwa Su Zaka Ringa Lura Dasu Akoda Yaushe Idan Kana Rubuta Wasikar Neman Aiki.

 1. Kayi Amfani Da Salo Mai Kawatarwa
 2. Ka Fadi Sunan Mukamin Da Kake Neman
 3. Kayi Bayanin Dalilin Da Yasa Kakeson Aikin
 4. Ka Bayyana Kwarewarka Akan Aikin
 5. Idan Ka Taba Aiki A Ma’aikata Irinta Ko Kana Da Basira Akan Aikin
 6. Karka Yabi Kanka Yayi Yawa Gameda Qualifications Ko Kwarewarka
 7. Kayi Amfani Da Sakin Layi Guda Hudu Ko Uku
 8. Sakin Layi Na Farko Kayi Bayanin Yadda Aikin Yazo Maka
 9. Sakin Layi Na Biyu Kayi Bayanin Yadda Zaka Taimakawa Kamfanin Ko Ma’aikatar
 10. A Sakin Layi Na Uku Ne Zakayi Bayanin Kwarewarka Akan Aikin
 11. A Sakin Layi Na Hudu Kuma Ka Bayyana Dalilin Da Yasa Kakeson Aiki Da Kamfani Tare Da Nuna Cewa Akwai Document Ko CV Dinka A Jikin Letter Din.

Sample Din Wasikar Neman Aiki Da Turanci

Ga Samples Anan Idan Kana Bukata Zaka Iya Daukawa Kai Tsaye. Wannan Misalin Yadda Ake Rubuta Wasikar Neman Aikine Ga Masu Bukata:

[Sunanka.]

[Adireshinka.]

[Garin Da Kake, Jaha.]

[Kwanan Wata.]

 

[Sunan Mai Daukan Aikin]

[Sunan Kamfanin]

[Adireshin Kamfanin.]

[Gari, Da Sunan Jahar Da Kamfanin Yake.]

 

Dear [Sunan Mai Daukan Aikin]

I Am Writing This Letter To Express My Interest In The Position Of [Sai Ka Rubuta Sunan Mukamin Da Kakeso] At [Sunan Kamfanin]. [Sai Ka Fadi Inda Ka Samu Labarin Aikin, Idan Ma Wanine Ya Baka Labarin Kamfanin Kuma Yana Aiki A Wajen, To Yana Da Kyau Ka Rubuta Sunanshi Anan]. And I Believe My [Ka Bayyana Kwarewarka Wato Skills Dinka Tare Da Qualifications Dinka] Make Me An Ideal Fit To Apply For This Job.

[Sakin Layi Na Biyu: A Wannan Sakin Layi Dinne Zaka Nuna Yadda Zaka Taimakawa Kamfanin, Idan Da Hali Ma Ka Bayyana Musu Wani Shiri Naka Da Kake Dashi A Kasa Wanda Duk Yana Cikin Tsarin Taimakawa Ko Gina Kamfanin].

[Sakin Layi Na Uku: A Gurguje Ka Bayyana Kwarewarka Da Qualifications Dinka, Skills Da Duk Wani Abu Da Kamfanin Takeso Ma’aikatan Su Kasance Suna Dashi Na Ilimi].

[Sakin Layi Na Hudu: Ka Karkare Da Dalilin Da Yasa Kakeson Aiki Da Kamfani, Tare Da Bayyana Musu Cewa Akwai Documents Dinka A Cikin File Na Wasikar].

 

Sincerely,

[Cikakken Sunanka]

Bayan Ka Gama Rubutawa, A File Dinda Zaka Tura Ka Saka Musa CV Dinka Tare Da Passport, Da Result Dinka Na WAEC Ko NECO Tare Da Primary School Certificate Dinka. Amma Duka Wadannan Fa Photocopy Ake Turawa, Wanda Baisani Ba Ya Kiyaye Wannan Akwai Masu Irin Wannan Kuskure.

Idan Baka San Yadda Zaka Rubuta CV Ba, Danna Nan Ka Koyi – Yadda Ake Rubuta CV Da Hausa

Misalin Wasikar Neman Aiki Da Turanci

Wannan Shine Misalin Dana Rubuta Saboda Mai Karatu Ya Fahimta. Na Rubutashine Cikin Hoto Ta Yadda Kowa Zai Gane Cikin Sauki, Don Haka Sanin Yadda Ake Rubuta Wasikar Neman Aiki Ba Abu Bane Mai Wahala. Matukar Kabi Wadannan Matakan To Da Yardar Allah Zakayi Nasara A Wajen Neman Aikinka.

Follow Us On Hausa Cinema Pinterest To See Our Free Samples Letters.

2 thoughts on “Yadda Ake Rubuta Wasikar Neman Aiki – You Need To Know Now”

 1. Pingback: Yadda Ake Rubuta Formal Letter Da Hausa – You Need To Know Now

 2. Pingback: Yadda Ake Rubuta Wasikar Korafi - You Need To Know Now

Leave a Comment

Scroll to Top