Yadda Ake Rubuta Wasika Da Hausa – You Need To Know Now
Ultimate Guide To Letter Writing In Hausa Language

Table Of Contents
Koyon Rubuta Yadda Ake Rubuta Wasika Da Hausa
Kanason Koyon Rubuta Wasika Da Hausa, Insha Allahu A Wannan Rubutun Zan Nuna Maka Hanya Mafi Sauki Da Zaka Rubuta Letter Cikin Kankanin Lokaci Batare Da Kasha Wahala Ba, Yadda Ake Rubuta Wasikar Hausa.Idan Kai Dalibine Ko Malami Ko Kuma Mai Bincike Na Musamman, To Wannan Makalar Zata Amfaneka Sossai Wajen Sanin Yadda Ake Rubuta Wasika Da Hausa.
Ita Wasika Hanyace Ta Musamman Ta Sadarwa. Domin Tana Daga Cikin Ire-Iren Hanyoyin Sadarwa Manya Da Muka Sani A Zamanin Yanzu. Hakanne Yasa Kowane Mutum Ya Dace Ya San Wannan Hanyar Domin Zata Taimaka Masa Matuka Wajen Neman Aiki, Wajen Kai Korafi Zuwa Gwamnati Ko Wani Babban Ma’aikaci Ko Ma’aikata. Haka Zalika Ta Hanyar Wasika Ana Iya Yin Abubuwa Da Dama Wadanda Zuwa Da Kai Ko Kira A Waya Bazaiyi Ba, Dole Saida Wasika. To Ashe Kenan Yana Da Kyau Ka Koyi Yadda Ake Rubuta Wasika.
Ire-Iren Yadda Ake Rubuta Wasika Da Hausa
Muna Da Ire-Ire Ko Ince Nau’in Rubuta Wasika Da Hausa, Wato Yana Da Kyau Ka Fara Sanin Wani Irin Wasika Kake Son Rubutawa Kafin Ka Fara, Saboda Bazaka Dauki Wannan Katurawa Wancan Ba, Hakan Zai Iya Jayo Maka Matsala. Ga Su Anan Na Kawo:
1. Formal Letter
Shi Formal Letter Nau’i Ne Na Wasika Da Ake Rubutawa Manyan Mutane. Wato Shi Formal Letter Ana Rubutashine Ga Wasu Masu Matsayi A Gwamnati Ko Hukumance, Ko Kuwa Dai Wata Sarauta, Ko Mukami. Sa’annan Yawanci Ana Iya Amfani Da Nau’in Rubutun Formal Letter Ne Wajen Rubuta Wasikar Neman Aiki (Kalli Samfurin Rubuta Wasikar Neman Aiki). Haka Zalika, Mutanen Da Ake Rubutawa Formal Letter Sun Hada Da Gwamnoni, Sarakuna, Minista, Kwamishina, Shugaban Kasa, Chairman, Shugaban Makaranta, Kamfani, Babbar Mai’aikata Da Sauransu.
2. Informal Letter
Shikuma Informal Letter Nau’i Ne Na Wasika Da Ake Rubutawa Yan Uwa Da Abokan Arziki. Wato Kenan Shi Informal Letter Ana Rubutashi Ne Ga Mutanen Da Muke Da Alaka Dasu Ko Kuma Dai Muke Gudanar Da Rayuwarmu Tare Dasu. Hakan Na Nufin Shi Informal Letter Ana Rubutashi Ne Daban Da Yadda Ake Rubuta Formal Letter. Bugu Da Kari, Ana Iya Rubuta Informal Letter Zuwa Ga Baba, Mama, Yaya, Kawu, Goggo, Aboki, Makwabta Da Sauransu.
3. Semi-Formal Letter
Semi-Formal Letter Ya Banbanta Da Sauran Nau’ukan Wasikun. Haka Zalika Shi Semi-Formal Letter Yana Alaka Da Formal Letter Da Kuma Informal Letter Gabadaya. Ana Rubuta Semi-Formal Letter Ne Ga Mutanen Da Ake Kasuwanci Dasu Ko Wata Kyakkyawar Alaka Ta Kasuwanci. Hakan Na Nufin Shi Formal Letter Ba Lallai Bane Sai Ka San Wanda Zaka Turawa Sossai Ba Ko Sanin Sama-Sama Kayi Masa Zaka Iya Tura Masa. Bugu Da Kari Ana Iya Turawa Landlord, Malamin Makaranta, Abokin Cinikayya Da Sauransu. Amma Mutanenmu Na Yanzu Basu Fiye Amfani Da Wannan Na’in Wasikar Ba, Shiyasa Yawanci Ba’a Santa Ba.
Yaya Ake Rubuta Wasika Da Hausa
Ana Rubuta Wasika Da Hausa Kamar Yadda Ake Rubutawa Da Turanci. Kuma Yadda Ake Rubutun Duka Babu Banbanci, Domin Dokoki Daya Ake Bi. Domin Shima Yaren Hausa Kamar Yadda Kowa Ya Sani Yarene Kamar Kowane Irin Yare, Duk Abinda Ka Samu A Turanci Zaka Iya Mayar Dashi Zuwa Hausa. Bugu Da Kari, Shi Rubuta Wasika Da Hausa Yana Da Kyau Idan Za’ayi Shi Ga Sarakuna Ko Masu Mukamin Gargajiya Yafi (Musamman Ma Masarautar Hausawa).
Dokokin Yadda Ake Rubuta Wasika Da Hausa
Ya Danganta Da Irin Wasikar Da Kake Son Rubutawa, Kowace Kalar Wasika Da Yadda Ake Rubutawa. Yadda Ake Rubuta Wasika Suna Suka Tara, Idan Wasika Zuwan Ga Manyan Mutane Kakeso Kaga A Bayaninmu Na Baya Dole Ka Koyi Formal Letter. Idan Kuma Kanason Ka Koyi Rubuta Wasika Zuwa Ga Masoyiya, Mahaifinka, Mahaifiyarka Ko Wani Da Kuke Alaka Kusa Dole Ka Koyi Informal Letter. Haka Zalika Idan Kanasone Ka Koyi Rubutawa Landlord Dinka Wasika Ko Abokin Kasuwancinka, Kana Da Bukatar Sani Akan Yadda Ake Rubuta Semi-Formal Letter.
Danna Nan Ka Koyi – Yadda Ake Rubuta Formal Letter Da Hausa Tare Da Dokokinta
Danna Nan Ka Koyi – Yadda Ake Rubuta Informal Letter Da Hausa Tare Da Dokokinta
Danna Nan Ka Koyi – Yadda Ake Rubuta Semi-Formal Letter Da Hausa Tare Da Dokokinta
Don Haka Kowace Kalar Wasika Tana Da Dokokinta, Don Haka Yana Da Kyau Ka Fara Sanin Wane Fannin Kake Son Fara Rubutawa Tukunna.