Yadda Ake Rubuta Formal Letter Da Hausa – You Need To Know Now

Yadda Ake Rubuta Formal Letter – Yana Da Kyau Ka Sani

Kanaso Ka Koyi Yadda Ake Rubuta Formal Letter Da Hausa, Shima Formal Letter Yana Daga Cikin Nau’ukan Rubuta Wasika, Domin Shine Jagora. Idan Ka Kasance Tare Da Ni Aliyu Saidu Jauro, Da Yardar Allah A Wannan Shafin Zanyi Maka Bayani Dalla-Dalla Akan Formal Letter Writing. Yadda Ake Rubuta Formal Letter, Dokokin Rubuta Formal Letter, Da Duk Wasu Abubuwan Da Yakamata Ka Sani Gameda Formal Letter. Idan Kai Dalibi Ne, Ko Malami Ko Kuma Dai Mai Bincike, To Ina Tabbatar Maka Da Cewa Wannan Rubutu Da Nayi Akan Wasikar Formal (Formal Letter) Zai Taimaka Maka Sossai Wajen Karin Ilimi.

Menene Ma’anar Formal Letter Da Hausa

Da Farko Dai Normally Idan Akace Formal Letter To Shima Nau’ine Na Wasika Da Ake Rubutawa Da Niyar Sadarwa (Aika Sako). In Addition, Shi Wasikar Formal Letter Ba Ga Kowa Ake Rubutawa Ba, Sai Wanda Yake Da Matsayi Na Musamman Ko Mukami. Shiyasa Ma A Turance Akeyi Masa Take Da ‘Official Letter’. Morever, Formal Letter Yafi Kowanne Wahalar Rubutawa, Domin Shi Ba’a Rubutashi Da Son Ra’ayi Kamar Informal Letter, Wato Ka Rubutashi Yadda Kaga Dama. Shi Wasikar Formal Letter Rubutashi Ake Cikin Dokoki Da Taka Tsan-Tsan Domin Gudun Kuskure. Bugu Da Kari, Shi Formal Letter Ana Rubutawa Mutane Ne Irinsu Gwamna, Minista, Shugaban Kasa, Manyan Masana’antu Da Kamfani, Kwamishina, Shuwagabannin Makaranta, Da Sauransu. Kaga Kenan Rubutun Formal Letter Ba Abu Bane Da Zaka Dauka Da Wasa.

Dalilin Da Yasa Ake Rubuta Formal Letter

Yadda Ake Rubuta Formal Letter Da Hausa

Ana Rubuta Wasikar Formal Ne Bisa Ga Dalilai Dayawa, Wadanda Zan Iya Cewa Abune Mai Wahala Na Iya Lissafasu Gabadaya Dalilan. Amma Na Kawo Wadanda Mu Mukafi Yawan Amfani Dashi A Namu Bangaren Wato Nan Arewa Hausawa Dama Nigeria Baki Daya. Dalilan Rubuta Wasikar Formal Sun Hada Da; Neman Aiki (Application Letters), Neman Gafara, Gayyata, Shigar Da Kara Ko Korafi, Da Sauransu.

Ka Koyi Yadda Ake Rubuta Wasikar Neman Aiki A Wannan Shafin Na Hausa Cinema Education Kyauta.

Iren-Iren (Nau’o’in) Formal Letter – Hausa Cinema

Wadannan Sune Manyan Nau’o’in Formal Letter Wadanda Ake Iya Turawa Manyan Mutane. Wadannan Sune Mafi Rinjaye A Cikin Official Letter Da Ake Amfani Dasu Yau Da Kullum A Makarantu, Ofisoshi, Ma’aikatun Gwamnati Da Kamfanuwa. A Matsayinta Na Dalibi Mai Bincike Yana Da Kyau Ka San Yadda Ake Sarrafa Duka Wadannan:

  • Application Letter (Wasikar Neman Aiki)
  • Complaint Letter (Wasikar Korafi)
  • Order Letter (Wasikar Umarni)
  • Promotion Letter (Wasikar Karin Matsayi A Wajen Aiki)
  • Sales Letter (Wasikar Cinikayya)
  • Resignation Letter (Wasikar Barin Aiki)
  • Invitation Letter (Wasikar Gayyata)
  • Letter Of Apology (Wasikar Neman Gafara)
  • Thank You Letters (Wasikar Godiya)

Yadda Ake Rubuta Formal Letter – Hausa Cinema

Domin Ganin Ka Rubuta Wasikar Formal Letter, Ga Hanyoyi Da Matakai Na Musamman Da Zaka Bi. Zamu Iya Kiransu Da Dokokin Rubuta Formal Letter.

Two Addresses And Date – (English Letter Writing In Hausa)

Ana Fara Rubuta Kowane Formal Letter Da Adireshi A Sama. Wato Adireshin Mai Turawa Akoda Yaushe Shine A Sama Ta Gefen Hannun Dama. Sai Kuma Adireshin Mai Karba A Kasa Dashi Kadan Ta Hannun Hagu (Da Ratan Saki Layi Daya Kawai) Daga Sama.

No Abbreviations – (English Letter Writing In Hausa)

Sannan Kuma A Wajen Saka Addrehinka Ka Tabbata Ka Saka Sunan Anguwanku, Local Government Din Da Kake, Sunan Jahar Da Kuma Lamabar Wayarka, Da Kwana Wata. (Ka Kula Wajen Saka Address Da Date Ba’a Saka Abbreviation Kamar Haka Lga, Ko Govt, Ko Kuma Oct, Da Sauransu. Ka Saka Komai Complete Babu Batun Abbreviating Na Kalma.

Shikuma Ga Wanda Zaka Turawa Din Ka Saka Cikakken Sunansa A Sama, Idan Yana Title Kayi Amfani Da Title Din. Misali, The Manager… Adireshinsa Daka Sani Complete.

Salutation – (English Letter Writing In Hausa)

Abu Na Gaba Kuma Shine Salutation, Wato Gaisuwa Cikin Girmamawa. Shine Dear Sir, Dear Mr. Shark, Dear Mrs. Joy Da Sauransu. A Wannan Wajen Ana Bukatar Ka Saka Dear Kafinnan Ka Saka Title Na Mutum (Misali Hon., Rev., Mal., Dr., Mr., Alh., Mrs., Ms., Da Sauransu) Sa’annan Kabi Baya Da Cikakken Sunansa. Kamar Haka Kenan Dear Dr. Dahiru Ahmad, (Tare Da Comma A Karshen).

Subject Of The Letter – (English Letter Writing In Hausa)

Anan Ne Sakin Layinka Na Farko, Bayan Ka Bada Rata Daga Wajen Dear Dr. Dahiru. Shi Subject Shine Zaka Kawo Dalilin Rubuta Wasikarka Kai Tsaye. Zaka Fara Janyo Hankalinsa Anan Banagaren, Shine First Paragraph Dinka (Shafin Rubutunka Na Farko). Kar Kayi Shi Mara Fasali Ta Yadda Da Zaran Ya Fara Karantawa Zaiji Bata Da Ma’ana, (Shiyasa Nace Rubutun Formal Letter Tana Da Tsada, Dole Sai An Nutsu kafin Za’a Rubuta Ta, Babban Mutum Ne Zai Karanta Don Haka Yana Bukatar Salo Da Fasaha).

Body Of The Letter – (English Letter Writing In Hausa)

Shi Body Shine Gangar Jikin Kowane Sako, Yawanci Kuma Shi Yake Zama A Matsayin Na Tsakiya (The Middle Paragraph) Wanda Daga Shi Na Karshe. Anan Gangar Jiki Zaka Baje Kolinka Ka Bada Bayani Gameda Abinda Ka Kwadaitar Dashi A Sakin Layi Na Farko Wato First Paragraph.

Conclusion Of The Letter – (English Letter Writing In Hausa)

Sakin Layin Karshe Ana Kiransa Da ‘Conclusion Letter’, Domin Anan Ake Karkare Duk Wani Bayani. Idan Wasikace Ta Bukata Anan Shashin Zaka Tausasa Murya Sossai Ta Yadda Zaka Samu Abinda Kake Nema.

Ending Of The Letter – (English Letter Writing In Hausa)

End Of The Letter, Karshen Sako Kenan. Anan Ake Karkarewa Shima Da Salutation, Zaka Rubuta Your Faithfully, Ko Kuma Yours Sincerely, Can Kasa Ta Gefen Dungun Dama. Ka Rubuta Sunanka Tare Da Sa Hannunka Officially.

A Madadin Sa Hannu Ida Kamfani Kake Rubutawa Ko Jagora Zaka Saka Sunan Kungiyar Ne Kawai.

1 thought on “Yadda Ake Rubuta Formal Letter Da Hausa – You Need To Know Now”

Leave a Comment

Scroll to Top