Sirrin Yadda Ake Kasuwancin Data – You Need To Know Now

Yadda Ake Kasuwancin Data – You Need To Know Now

Kanason Fara Kasuwancin Data Ko Kasuwancin Kati Cikin Sauki (Online)? Anan Zaka Koya Da Yadda Ake Samun Kudi Ta Hanyar Sayarda Data Batare Da Kasha Wahala Ba. Nayi Bayani Dalla-Dalla Dangane Da Harkar Kasuwancin Data Da Kuma Kati. Kai Tsaye Karanta Wannan Rubutun A Nitse Domin Fahimtar Komai Cikin Sauki, Kar Kayi Karatun Gaggawa Shafin Hausa Business Tayi Baynanin Komai Dalla-Dalla.

Menene Kasuwancin Data?

Kasuwancin Data Kasuwancine Na Zamani Mai Zaman Kansa Wanda Mutane Sukeyi Kuma Suke Samun Riba A Kai. Farkon Zuwan Kasuwancin Data An Farashine A Shagunan Sayar Da Kati, Daga Bisani Kuma Kasuwancin Ya Zamanto Ana Iya Yinsa Ta Yanar Gizo Kuma A Samu Fita Harda Ribar Da Mutum Zai Iya Rufawa Kansa Asiri Da Ita.

Yaya Ake Yin Kasuwancin Data?

Ana Yin Kasuwancin Datane Kamar Yadda Akeyin Kowane Irin Kasuwanci. Wato Mutum Ya Biya Kudi A Bashi Kaya, Haka Kasuwar Data Itama Ta Kasance, Idan Mutum Ya Aiko Maka Da Kudi, Sai Ka Tura Masa Data Yadda Ya Bukata.

Abubuwan Da Zaka Tanada Kafin Ka Fara Kasuwancin Data

Dolene Ka Tanadi Abubuwan Da Zaka Fara Kasuwancinka Dashi. Kamar Dai Yadda Misali Idan Zaka Fara Blogging Dole Ka Tanadi Kudin Hosting, Kudin Domain Da Sauransu. Shi Kasuwancin Data Idan Zaka Fara Zaka Tanadi Wadannan Abubuwa:

 1. Wayarka Na Kanka Ko Kwamputa
 2. Data/Internet Connection Mai Karfi Kuma Akoda Wani Lokaci
 3. Jari
 4. Lokaci Da Nitsuwa

Wadannan Sune Abubuwan Da Zaka Tanada Kafin Ka Fara Kasuwancin Data.

Yaya Akeyin Register Kasuwancin Data?

Da Farko Dole Zaka Nemi Yaya Zakayi Register? Register Kyautane A Wannan Hanya Dana Kawo Muku. Ba Kamar Wasu Daga Cikin Shafukan Sayar Da Data Ba, Zakaji Ance Saika Biya N1000, Ko N2000, Ko Sama Da Haka Kafin Ka Fara Kasuwancin Ba, A’a Wannan Kyautane Rijista.

Da Farko Zaka Danna Wannan Sunan VTUNetwork, Zai Nuna Maka Inda Zakayi Register Kamar Haka:

VTU Network Yadda Ake Samun Kudi Online

Kai Tsaye Zai Kawoka Wannnan Shafin, Inda Zaka Sanya Sunanka A Farko Wato First Name, Da Last Name, Da Phone Number, Da Kuma Username. (Shi Username Shine Sunan Da Zaka Ringa Amfani Dashi Wajen Login, Karban Kudi, Referring, Da Sauransu. Don Haka Yana Da Kyau Ka Saka Nickname Dinka).

Email Kuma Ka Saka Email Dinka Wanda Kake Amfani Dashi. Password Kuma Ka Saka Wanda Bazaka Manta Ba.

VTU Network Kasuwancin Data

Bayan Ka Gama Register, Ka Cike Bayananka Kamar Yadda Suka Tambayeka. Zasu Nuna Maka Cewa Suna Tayaka Murna Acount Dinka Ya Budu. Kawai Ka Danna OK…

Data Website Registration Succesfully

Bayan Ka Danna OK, Zai Nuna Maka Nan Wato ‘Log In’ Page Inda Zaka Shigar Da Bayananka Ka Shiga Cikin Account Din Daka Kirkira. Anan Zaka Saka Username Dinka Da Kuma Password Dinka.

Log In Vtu Network Data Selling Website

Bayan Kayi Log In, Kai Tsaye Zai Kawoka Ga Dashboard Dinka, Wato Inda Zaka Fara Harkar. Amma Kafinnan Zasu Nuna Maka Cewa Ka Kirkiri PIN Guda Biyar Wadanda Zaka Ringa Transactions Dashi. Wato Kenan Anan Kowane Data Mutum Zai Saya Ko Kati (Ga Masu Kasuwancin Kati) Sai Ya Saka Wadannan PIN Din Saboda Karin Tsaro. Anan Hoton Ya Nuna Zaka Sanya PIN Din Da Kakeson Amfani Dashi, Ka Sake Sakawa Saika Danna ‘Save Pin’.

Create Transaction Pin On Vtu Network

Bayan Ka Danna Save Pin, Zai Nuna Maka Cewa ‘Ka Kammala’. Ka Lura Saka PIN Dinnan Ya Zama Dole, Koda Baka Saka Ba Idan Zakayi Wani Abu Zasu Sake Nuna Maka Ka Saka.

Transaction Pin Created Successfully

Abu Na Gaba Kuma Anan Shine, Kamar Yadda Kake Gani Nan Shine Duka Tsarinsu: Kasuwancin Kati, Kasuwancin Data, Biyan Bill Din NEPA, Biyan Startimes, GOTV, Ko DSTV (Sauki Ta Samu Zaka Iya Rechearging Din Startimes Dinka Daga Gida, Kuma Ka Ringa Yiwa Mutane). Zaka Iya Buga Kati, Sa’annan Kuma Zaka Iya Mayarda Katinka Su Koma Banki.

Buy Data Anan Zaka Ringa Sayan Data, Bayan Ka Danna, Zai Baka Zabin Layi. Idan Na MTN Ne Ko Airtel Saika Zaba Duk Wanda Kakeso, Zai Kaika Ga Adadin Da Kakeso.

VTU Network - Yadda Ake Kasuwancin Kati

Wadannanma Wasu Daga Cikin Services Na VTU Network Ne, Kamar Yadda Kake Gani. Scratch Card Shine Sayan Katin NECO Ko WAEC Batare Da Bata Lokaci Ba, Kuma VTU Network Yana Da Arha. Ga Tsarin Bulk SMS Wanda Kamfanine Take Amfani Da Wannan Wajen Tura Sakwanni Ga Kwastomomi. Ga Bonus To Wallet, Inda Idan Ka Samu Bonus Zaka Dawo Dashi Asalin Cikin Account Dinka. Ga Wallet Transfer, Shikuma Ba Sai Nayi Bayani Ba, Tura Kudi Kenan. Na Kusa Da Karshe Shine Transactions, Anan Zaka Kalli Duk Wani Saya Da Sayarwa Da Kayi. Koda Ace Mutum Ya Nuna Baiga Data Ba, Anan Zaka Shiga Kayi Masa Screenshot. Na Karshe Kuma My Refferals, Anan Zaka Kalli Adadin Mutanen Da Sukayi Regsiter Ta Link Dinka.

VTU Network - Yadda Ake Samun Kudi Online

Bayani Akan Ribar Da Ake Samu A Kasuwancin Data

Ana Samun Riba Fiye Da Tunaninka Domin Kuwa Abun Sai Ka Ganewa Idanunka. Kowane 1GB Idan Zaka Sayar Dashi A N300 To Kana Da Ribar N50, Idan Kuma N350 Zaka Sayar Kana Da Ribar N100. Kaga Kenan Idan Kana Samun Customers Masu Saya Akai-Akai, Wannan Sana’ar Ma Kadai Ta Isheka, Zata Iya Rike Ka. Wallahi Ni Lokacin Dana Fara Kasuwancin Data A 2020, Ribar Dana Hada Cikinta A Wata Daya Ya Kai N45,000 Har Da Yan Kai. A Hakanma Kuma Ban Dukufa Kan Kasuwancin Ba, Bana Bashi Lokaci, Ban Mayi Tallarsa Ba.

Duba Kaga Shaida Da Kanka, Anan Zaka Ga Irin Kudaden Dana Samu Gabadaya A Cikin Asusuna Na Data Kimanin N300,000. Don Haka Karka Yaudari Kanka Kace Kasuwancin Data Wahalace, Ko Wace Irin Sana’a Kake Zaka Iya Hadawa Da Kasuwancin Data. Musamman Ma Sana’ar Zaman Shago, Bazaka Rasa Datar Da Zaka Ringa Yin Amfani Da Ita Ba.

Kalli Yadda Ake Rubuta Wasikar KorafiDownload GB WhatsApp Apk Pro 2022 Free.

Yadda Mutum Zai Gujewa Yan Damfara

Akowace Sana’a Ba’a Rasa Wasu Mutanen Da Suke Kawo Cikas. Wadanda Su Hakan A Jininsu Yake, Shiyasa Mukayi Bincike Mai Zurfi Akan Yadda Mutum Zai Guje Musu Ya Rabu Dasu. Ga Hanyoyin Da Mutum Zai Bi Domin Kaucewa Sharrin Yan Damfara;

 1. Kada Ka Kuskura Ka Turawa Mutum Data Batare Da Ya Saka Maka Kudi A Account Ba.
 2. Idan Mutum Yace Ya Tura Maka Kudi Kuma Kai Baka Gani Ba Ka Umurceshi Da Yayi Maka Screenshot Na Debit Alert Dinsa, Idan Babu Ka Rabu Dashi Dan Damfara Ne.
 3. Akwai Masu Cewa ‘Katura Min Datar Kafinnan Na Shiga Application Na Tura Maka Kudin, Kada Ka Yarda Dasu Idan Ba Dai Kasan Mutumin Bane Kut-Da-Kut.
 4. Idan Mutum Yace Bai Ga Data Ba Kaje Wajen Transactions Naka Ka Dubi Nashi Kayi Masa Screenshot Don Ya Tabbatar.
 5. Akwai Kuma Masu Turo Kudi Short, Wasu Suna Turo N500 Suce Zasu Cika, Amma Bazasu Cika Dinba, Wasu Kuma Zasu Tura Maka Complete Suce Ka Kara Musu Zasu Sake Turowa.
 6. Kada Ka Kuskura Ka Baiwa Wani Password Dinka Da Username, Matukar Ba Saninsa Kayi Ba, Kuma Ka Yarda Dashi 100% Kafinnan.

Wadannan Sune Manya-Manyan Hanyoyin Da Yan Damfara Sukebi Suke Damfarar Masu Kasuwancin Data.

Yadda Zaka Ringa Samun Customers Da Wuri

Idan Kana Biukatar Masu Sayan Datarka Dolene Sai Ka Ringa Tallata Shi. Bawai Kamar Crypto Currency Yake Ba, Zaka Ringa Baiwa Yan Uwanka Da Abokanka Suna Saka Maka A Status Nasu, Zaka Ringa Sharing A Facebook, Idan Da Hali Ka Samu Facebook Page, Zaka Ringa Daura Tallan A Instagram, YouTube, Telegram, WhatsApp Group Da Sauran Wuraren Da Jama’a Suke Hallaruwa.

Matsalolin Da Masu Kasuwancin Data Suke Fuskanta

Wata Matsalar Idan Aka Juyata Ta Wata Fuskar Bazata Zama Matsala Ga Wani Ba. Shiyasa Bakowane Matsala Muka Lissafo A Wannan Shashi Ba, Amma Zamu Lissafo Manya-Manya Wadanda Suka Kasance Barazana Ga Yawancin Masu Kasuwancin Data. Wadannan Matsaloli Suna Janyo Mutum Ya Daina Kasuwancin Data, Ko Jarinsa Ta Karye Ya Ringa Asara Maimakon Riba.

Matsala Daga Wajen Abokai Da Yan Uwa

Sau Dayawa Zaka Samu Idan Ka Saka Tallan Data Sai Kaga Wasu Yan Uwanka Suna Kokarin Rokonka, A Ciki Harma Da Wanda Kakejin Nauyinsa Bazaka Iya Hanashi Ba. Wani Yakan Canja Salon Rokon Ya Nuna Maka A Takure Yake Bashida Mafita.

Dayawa Yan Uwa Zaka Samu Basu Biyan Kudin Data Complete, A Madadin A Baka N300, Sai A Baka N250 Ko N200, Wanda Hakan Shima Babban Matsalane.

Rashin Yarda Daga Masu Saya (Customers)

Idan Ya Kasance Sana’arka Ta Online Ne Dole Ka Samu Kwatomomi Wadanda Bazasu Yarda Da Kai Ba. Musamman Lokacin Da Ka Tura Musu Account Number Kace Su Turo Kudi, Sai Suga Kamar Damfararsu Zakayi. Don Haka Yasa Yawanci Kasuwancin Data A Online Yake Lalacewa.

Biya Da Recharge Card (Kati)

Wasu Kwastomomin Basuda Account, Kuma Sai Ka Samu 1GB Sukeso Ba Wani Mai Yawa Ba Ballentana Suje POS. Don Haka Sai A Ringa Tura Maka Kati, Shikuma Wannan Kati Ba Cigaba Bane A Wajenka.

Wadannan Sune Wasu Daga Cikin Matsalolin Da Masu Kasuwancin Data Suke Fuskanta.

Yadda Zaka Magance Matsalolin

Kamar Yadda Na Lissafo Manyan Matsaloli. Yana Da Kyau Kuma Na Kawo Maganin Matsalolin, Wadanda In Allah Ya Yarda Idan Mutum Ya Bisu To Zai Dace.

Maganin Matsalar Yan Uwa Ko Abokai

Ka Guji Nunawa Kowane Dan Uwanka Cewa Ka Wadatu. Sa’annan Kuma A Duk Lokacin Da Mutum Yayi Kokarin Shiga Maka Hakki Yana Da Kyau Ka Fito Fili Ka Zayyana Masa. Ka Nuna Masa Kaifa Gaskiya Wannan Shine Sana’arka Kuma Kudi Ka Cire Ka Saka A Ciki.

Maganin Matsalar Masu Nuna Rashin Yarda

Yana Da Kyau Kasan Kwastomominka, Musamman Ma Ace Kuna Da Wata Alaka Dasu Ta Online. Misali; Wanda Ya Aikoshi Ya Saya Data A Wajenka Ya Sanshi Kaima Ka Sanshi, Kada Ka Zama Mai Kai Tallanka A Wajen Da Baza’a Yarda Da Kai Ba.

Maganin Matsalar Masu Tura Recharge Card (Kati)

Kamar Yadda Na Fada A Baya Wannan Babban Matsalane. Tabbas Hakane, Domin Idan Kati Ya Shiga Wayarka Babu Yadda Zakayi Ka Ciresu Cif-Cif Yadda Suke, Dole Sai Ka Rasa Wasu Kudaden, Wanda Hakan Koma Bayane, Mafita Shine Kada Ka Bari Mutum Ya Turo Maka Kati, Idan Bazaiyi Maka Transfer Ba Ya Daina.

Shawari Ga Wadanda Sukeson Fara Kasuwanci Data

Yana Da Kyau Kasan Cewa Ita Kasuwa Akwai Riba Sa’annan Akwai Faduwa. Sa’annan Ka Tuna Cewa Wannan Sana’ace Babba Wadda Wasu Suke Nemanta Ido A Rufe Don Haka Yana Da Kyau Ka Riketa Hannu Bibbiyu Ka Kuma Kula Da Ita Ta Hanyar Daraja Kwastomominka, Duk Wanda Yazo Da Sunan Kasuwa Ka Bashi Lokaci Komai Kankantar Kayan Da Zai Saya.

Kasancewarka A Online Koda Yaushe Yana Da Matukar Muhimmani Matukar Kanason Inganta Kasuwancin Naka A Yanar Gizo. Ka Zamanto Ative Akoda Yaushe Ta Yadda Duk Wani Mai Bukata Zai Nemeka Ya Samu Akan Lokaci. Kada Kayi Register Idan Ka Tabbata Cewa Bazaka Samu Fita Ba, Ina Nufin Idan Bakada Hanyoyin Da Zaka Tallata Ka Kai Ga Masu Saya. Idan Kana Alaka Da Mutane Kuma Kana Da Lokaci Gaskiya Yana Da Kyau Ka Jarraba Kasuwancin Data, Domin Yana Kawo Kudi Fiye Da Tunaninka.

Idan Kana Downloading Na Fina-Finai Ko Kai Dan Downloading Ne Yana Da Kyau Kaima Kayi Register Domin Ka Ringa Samun Data Cikin Sauki Da Arha. Idan Shagon POS Ne Da Kai Ko Wani Digital Business Yana Da Kyau Ka Shiga Harkar Ko Domin Ka Ringa Taimakawa Kanka.

3 thoughts on “Sirrin Yadda Ake Kasuwancin Data – You Need To Know Now”

 1. Pingback: Yadda Ake Samun Kudi A Online (Yanar Gizo) – Hausa Cinema

 2. Pingback: Yadda Ake Samun Kudi A Facebook – Hausa Cinema

 3. Pingback: Aliyu Saidu Jauro Biography, Education, Career, And Net Worth

Leave a Comment

Scroll to Top