Yadda Ake Duba BVN Number A MTN, Airtel, GLO 2023

Barka Da Kasancewa Da Wannan Shafin Na Hausa Cinema, Kanason Ka Duba BVN Dinka A Wayarka? A Yau Mun Kawo Hanyoyi Guda Biyu Da Zaka Duba BVN Dinka A Wayarka. Saboda Haka A Wannan Rubutu Zaka Koyi Yadda Ake Duba BVN Number A Layin MTN, Ko Layin Airtel, GLO Da 9mobile (Etisalat). Babu Bukatar Kaje Bank Ka Bata Lokaci Daga Cikin Wayarka Idan Kayi Amfani Da Wadannan Hanyoyi Zaka Kalli BVN Dinka A Sauki.
Idan Misali Kayi BVN Baizo Maka Ba Zaka Iya Dubawa, Domin Ba Ko Yaushe Bane Idan Kayi BVN Zasu Turo Maka Lambobin Ta SMS Ba. Watakila Kuma Ka Manta Da BVN Dinne, Ko Kuma Ya Bata, To Ga Yadda Abun Yake…
MTN Airtel GLO 9mobileTable Of Contents
Menene BVN Number?
BVN Na Nufin Bank Verification Number A Turance, Wasu Lambobine Guda Goma Sha Biyu (11) Da Duk Mai Amfani Da Banki Yake Mallaka. Wannan BVN Din Yana Dauke Da Bayanka Kama Daga Transactions Da Kayi A Dukkanin Bankunanka, Hotonka, Zanen Yatsun Ka, Adireshinka Da Sauran Bayananka.
BVN Tamkar Shaida Ne Da Yake Taimawakawa Mutum Wajen Saukaka Harkokin Transfer (Transactions) Dinsa. Sa’annan Bankuna Suna Iya Amfani Da Wannan BVN Din Wajen Bincike Da Sauransu. Bugu Da Kari, Mallakar BVN Ya Zama Dole Matukar Kana Bukatar Kayi Hada-Hadan Kudi, Ka Bude Bank Account.
Yadda Zakayi Register Din BVN Ka Samu Naka
A Zamanin Mu Na Yanzu Samun BVN, Ko Kuma Ince BVN Registration Abune Da Yake Da Sauki. Matukar Kana Tare Da Bank A Kusa Da Kai Zasu Bude Maka. Ba’a Iya Bank Ba, Hatta Manya POS Centers Idan Kaje Zaka Samu Ayi Maka Cikin Sauki. Kuma Da Zaran Anyi Maka Zaizo Maka Cikin Awowi 24 Matukar Akwai Network Baya Wuce Wannan Lokaci.
Yadda Ake Duba BVN Number A Layin MTN
Idan Kana Da MTN Kuma Ka Manta Kanaso Ka Bincika Ta Layin MTN, Abinda Zakayi Shine Ka Danna *565*0#. Bayan Ka Danna Wadannan Lambobi Cikin Dakika Kadan Zasu Nuna Maka BVN Din. Sa’annan Kuma Duba BVN Ba Kyauta Bane, Idan Zaka Bincika Zasu Cajeka Naira 20.
Karanta 👉 Yadda Zaka Ringa Samun Kyautar Data A Layin MTN, Airtel, GLO, Da 9Mobile.
Yadda Ake Duba BVN Number A Layin Airtel
Idan Kanaso Ka Duba BVN Dinka A Layin Airtel Shima Lambar Da Zakayi Amfani Dashi Shine Ka Danna *565*0# Ka Tura. Da Zaran Ka Tura Zasu Aiko Maka Da Lambar BVN Dinka Cikin Kankanin Lokaci. A Layin Airtek Shima Za’a Cajeka Naira 20 Kudin Dubawa.
Karanta 👉 Abubuwa Goma Dake Tayarwa Mata Sha’awa.
Yadda Ake Duba BVN Number A Layin GLO
Idan Ka Bude BVN Da GLO Kuma Kana So Ka Duba BVN Dinka Da Ka Manta Ko Ya Bata, Kai Tsaye Kawai Ka Danna *565*0#. Za’a Cajeka Naira 20 Sa’annan A Turo Maka Lambobin BVN Din Cikin Kankanin Lokaci.
Yadda Ake Duba BVN Number A Layin 9Mobile
Ka Danna *565*0# Domin Ka Duba BVN Number Dinka A Layin 9Mobile. Bayan Ka Danna Ka Tura, Zasu Nuna Maka Da 11 Digits BVN Numbers Dinka Cikin Kankanin Lokaci. Amma Ba Kyauta Bane Suma, Kamfanin Zasu Cajeka Naira 20 Kudin Dubawa.
Karanta 👉 Best Hausa Radio Stations In 2023 That You Need To Know Now.
Kammalawa

Daga Karshe Muna Fatan Wannan Rubutu Ya Biya Maka Bukata. Don Haka Idan Kanaso Ka Duba BVN Dinka Ka Tabbatar Kana Da Ragowar Kudi A Cikin Asusunka Kamar Naira 50. Sa’annan Kuma Ka Tabbatar Da Cewa Layin Da Kakeson Ka Duba BVN Din Shine Layinka. Domin Bazasu Nuna Maka BVN Ba Idan Bada Layin Kayi Ba, Dolene Kana Bukatar Kayi Amfani Da Layin Wajen Dubawa.
Karanta: Yadda Ake Duba NECO Result.
Gaskiya ni nasa nawa be yiba