Hausa Tech

Yadda Ake Bude YouTube Channel Har A Fara Samun Kudi 2023

Kana Son Koyon Yadda Ake Bude YouTube Channel, Yadda Ake Samun Kudi A YouTube, Da Kuma Sanin Abubuwa Da Yawa Dangane Da YouTube. Kazo Inda Yakamata, Domin Wannan Rubutu Zai Koya Maka Abubuwa Da Dama Dangane Da YouTube Cikin Harshen Hausa. Tun Daga Yadda Zaka Bude Har Izuwa Yadda Zaka Samu Subcribers Da Watch Time Hours Har A Fara Biyanka.

Assalamu Alaikum Jama’a Yan Uwa Maza Da Mata, Barkanmu Da Warhaka, Barkanmu Kuma Da Sake Kasancewa Daku A Wannan Shafi Namu Mai Albarka Na Hausa Cinema.

A Wannan Shafi Na Hausa Cinema Muka Abubuwan Da Sukan Shafi Computer, Wayar Hannu, Da Kuma Abubuwan Da Suka Shafi Yanar Gizo. Lokuta Da Dama Mukan Kawo Hanyoyi Da Ake Samun Kudi Ta Yanar Gizo Domin Yan Uwanmu Matasa Maza Da Mata.

Menene YouTube Channel?

A Takaice, YouTube Shafine Na Musamman Da Wasu Mutane Uku Suka Kirkira A Shekarar 2005. An Kirkiri Shafinne Saboda A Ringa Kallon Bidiyo Ta Ciki. Ana Kallon Bidiyo Kala-Kala Kama Daga Wasanni, Dogayen Fina-Finai, Labarai Da Sauransu, Amma Saidai Shafin YouTube Ta Hana Kallon Abubuwan Da Suke Da Alaka Da Batsa.

YouTube Channel Kuwa Tashace A Cikin YouTube Wanda Dole Saida Ita Ake Daura Videos, Kuma An Baiwa Kowa Damar Bude YouTube Channel.

Menene Amfanin Bude YouTube Channel?

Amafanin Bude YouTube Channel Suna Dayawa, Domin Zai Mayarda Kai Sananne, Zai Kara Maka Ilimi Babban Abun Kuma Zai Kawo Maka Kudin Da Baka Taba Zato Ba A Rayuwarka. Matukar Ka Tsaya Kayi Shi Yadda Ya Kamata.

Da Gaskene Ana Samun Kudi A YouTube?

Wasu Suna Ji Ana Biyan Mutane A YouTube Amma Watakila Basu Yarda Ba, To Tabbas Ana Biya Kuma Insha Allahu A Wannan Rubutun Zan Nuna Muku Sa’annan Na Tabbatar Muku.

Da Kuma Ba’a Biya Da Bazakaga Mutane Suna Kashe Kudadensu Suna Shiga Ba. Zakaga Dukkan Harkokin Yanzu Sun Koma YouTube. Kamar Fina-Finai, Masana’antar Kannywood, Nollywood Harma Da Manyan Tashoshin Watsa Labarai.

Wannan Yan Kudaden Suna Taimaka Musu Wajen Biyan Ma’aikata Da Sauransu.

Yaya Ake Biyan Kudi A YouTube?

Yadda Ake Bude Youtube Channel

Ana Biyan Kudine A YouTube Ta Hanyar Amfani Da Google AdSense, Ba Lallai Bane Ka Fahimci Google AdSense Dinda Nake Magana Akai Ba. Amma Matukar Ka Shigo Harkar YouTube Ko Kuwa Idan Kana Harkar Website Zaka Sanshi.

A Gurguje Ana Biyane Ta Hanyar Google AdSense Kuma Ana Biyane Kamar Yadda Ake Biyan Ma’aikatan Gwamnati, Wato Kowane Wata Ranar 21 Ake Biya. Idan Kudinka Da Yake YouTube Din Ya Kai Dala $100 Zasu Tura Maka Kai Tsaye Ta Bankinka. A Lalace A Wata Idan Ka Tara Kudi A YouTube Zaka Ringa Fitar Da Dala $100 Wanda A Yanzu Ya Hausa N80,000 A Kudin Nigeria (Black Market).

Wasu Suna Iya Samun Sama Da Miliyan 10 Akowane Wata.

Me Ya Kamata Tanada Kafin Ka Bude YouTube Channel?

Idea

Idan Kanson Kaima K Bude YouTube Channel, Abu Na Farko Shine Ya Kasance Kana Da Idea Akan Abinda Zaka Bude, Wato Idan Kanason Bude Channel Akan Kiwon Lafiya, Ya Kasance Kasan Abubuwa Dangane Da Kiwon Lafiya.

Ilimin Editing

Sa’annan Ya Kasance Kana Da Ilimin Editing Koda Kadanne Domin Idan Kanayi A Hankali Zakazo Ka Kware Watarana. Idan Bazaka Iya Ba Mun Tanadi Group Na Musaman A WhatsApp Da Telegram, Idan Kazo Zamu Koya Maka Cikin Sati Daya. Zamu Baka Applications Da Zakayi Amfani Dasu, Video Elements Da Zakayi Amfani Dasu. Sa’annan Mu Baka Background Music Da Background Images Da Stickers Harda Sound Effects Da Basuda Copyright Akansu, Kaima Ka Fara YouTube Cikin Tsafta Da Kwarewa.

Sunan Channel

Bayan Wannan Kuma Ka Tanadi Sunan Channel Din, Ka Nemo Channel Din Da Ka Tabbatar Da Cewa Babu Mai Amfani Dashi, Ta Yadda Ko Daga Ina Idan Akayi Searching Kai Kadai Ne Kawai.

Na’ura (Waya Ko Computer)

Sa’annan Ya Kasance Kana Da Babbar Waya Ko Computer Da Zaka Ringa Editing A Ciki Kana Daurawa A YouTube.

Kudi

Abu Na Karshe Kuma Ya Kasance Kana Da Dan Kudi A Kasa, Wato Kana Da Kudin Da Zaka Ringa Sayan Data Kana Daura Videos Kuma Kana Kara Bincike Akan Abinda Kakeyi Domin Dole Saida Bincike.

Nawa Ake Samu A YouTube?

Kamar Yadda Na Fada A Baya Ana Samun Kudi A YouTube. Kuma Mutanenmu Dayawa Sanadiyar YouTube Sunyi Arziki, Haka Zalika Wasu YouTube Shine Sana’arsu A Yanzu. Zakaji Ance Mutum YouTuber Ne.

Ku Duba Nan Ku Ga Irin Kudaden Da Mutane Suke Samu A YouTube.

Karanta: Yadda Ake Duba BVN Number A MTN, Airtel, GLO 2023.

Saira Movies

Saira Movies Monthly Earning On Youtube

Kamar Yadda Wannan Hoto Ya Nuna, Adadin Kudin Da Tashar Saira Movies Take Samu Kenan. Wanda A Ciki Ake Sanya Shirin Labarina Series. Idan Akayi Lissafin Kudin Kuma Gashinan Suna Samun Kwatan-Kwacin $1,300 Zuwa $21,600. Wanda Hakan Na Nufin Zamu Iya Cewa Suna Samun Sama Da $10,000 Ko $7,000 A Kowane Wata, Wanda Idan An Mayar Dashi Kudin Najeria Zai Iya Bada Sama Da N8 Million.

Ali Nuhu

Ali Nuhu Monthly Income On Youtube

Idan Kai Bahaushe Ne A Duk Inda Kake Kasan Waye Ali Nuhu. Jarumi Ne A Masana’artar Kannywood (Hausa Cinema) Wanda A Yanzu Shine Sarki (The King Of Kannywood). Daga Cikin Miliyoyin Tashoshin Dake YouTube Shima Ya Mallaki Nasa Mai Suna Ali Nuhu Inda Yake Sanya Fina-Finai Masu Dogon Zango. A Bincike Da Mukayi A Bayan Nan Tashar Tana Samun $500 Zuwa $8,000 Kowane Wata.

Karanta: Yadda Ake Duba NECO Result.

Mamaki TV

Mamaki Tv Monthly Income

Mamaki TV Na Daya Daga Cikin Manyan Tashoshin Hausawa Mallakar Arewa YouTubers. Tashar Ta Dukufa Wajen Kawo Labarai Da Sauransu (Ana Yi Mata Lakabi Da Komai Da Ruwanka). Kamar Yadda Binciken Mu Ya Nuna, Mamaki TV Na Samun Sama Da $100 Zuwa $1,500 Kowane Wata.

BBC Hausa

Bbc Hausa Monthly Earning On Youtube

BBC Dake Da Reshe A Nigeria (BBC Hausa), Sun Mallaki Tasha A Shafin YouTube Domin Sanya Labarai Cikin Bidiyo. Ba Tare Da Bata Lokaci Ba Tashar BBC Hausa Tana Samun Sama Da $400 Zuwa $6,000 Kowace Rana.

Me Ya Kamata Na Kiyaye Idan Na Bude Channel?

Abu Na Farko Yana Da Kyau Ka Kiyaye Daura Batsa A Shafinka.

Sa’annan Yana Da Kyau Ka Cire Idanunka Daga Videon Wani, Karka Kuskura Kaga Videon Wani Kayi Downloading Kaje Kayi Editing Ka Dawo Ka Daurawa Naka. Domin Idan Kana Haka Ko Shekara Dari Zakayi Bazasu Taba Biyanka Ba.

Idan Kuma Akayi Rashin Sa’a Mai Videon Ya Gani Zai Tura Maka Abinda Abinda Ake Kira Copyright Strike. Idan Kuma Aka Tura Maka Copyright Strike Sau Uku Shikenan Ko Subscribers Miliyan Ka Tara Za’a Kulle Channel Din. Don Haka Ka Kiyaye Daukan Abun Wani Koda Hotone Ana Saka Masa Reused Content.

Bugu Da Kari Ka Kiyayi Zage Zage A Channel Dinka.

Me Ake Bukata Kafin Ka Fara Samun Kudi A YouTube?

Abu Biyu Kawai YouTube Suke Bukata Kafin Su Fara Biyanka.

1,000 Subcribers

Abun Na Farko Shine Dole Saika Tara Subscribers Dubu Daya, Akwai Posting Da Mukayi A Wannan Shafin Idan Ka Duba Zaka Ga Yadda Zaka Samu Subscribers 1,000 Cikin Kankanin Lokaci.

4,000 Watch Time Hours

Abu Na Biyu Biyu Kuma Watch Time Hours. Shi Watch Time Hours Shine Adadin Kallon Da Mutane Suka Kalli Videos Dinka. Idan An Hada Kallon Wancan Da Kallon Wancan, Wancan Yayi Kallon Awa Daya Wancan Awa Biyu Wancan Biyar Wancan Minti Hamsin. Kullum Suna Lissafi, Idan Ya Kai, Su Da Kansu Zasu Fada Maka Cewa Kaje Kayi Applying Ko Ka Shiga YouTube Studio Ka Ringa Dubawa, Idan Ya Cika Kawai Sai Kayi Applying.

Yadda Ake Bude YouTube Channel A Waya

Kalli Bidiyon Yadda Ake Bude YouTube Channel A Waya Cikin Sauki.

Shawara Ga Matasa Maza Da Mata

Kudi Ya Dawo Internet, Kudade Suna Yanar Gizo. Wallahi Akwai Hanyoyi Dayawa A Yanar Gizo Wadanda Idan Kajure Ka Bisu Zaka Ringa Samun Na Rufin Asiri. Musamman Ma Shi Wannan YouTube Din. Dayawa Matanananmu Hausawa Musamman Mata, Suna Tunanin Bazasu Iyaba.

Idan Kin Iya Kitso, Kin Iya Lalle Kin Iya Dinki Ko Kin Iya Dafa Wani Abinci Na Gargajiya Ko Zamani Ko Kwaliya Kika Iya To Zaki Iya Bude Channel Dinki Ki Ringa Nunawa Mutane. Idan Kina Aiki Mai Inganci Zaki Ringa Samun Mutane Daga Fadin Duniya Gabadaya. Cikin Kankanin Lokaci Sai Kiga Anfara Biyanki Kina Samun Abinda Zaki Rufawa Kanki Harma Ki Dauki Wasu Aiki Kina Biyansu.

Kamar Yadda Na Fada A Baya Kudaden Da Ake Samu A YouTube Sunfi Karfin Wasa. Shiyasa Al’amarin Komai Ya Koma Online. Hatta Fina-Finai Yanzu Sai Online Kawai Saboda Duk Kudin Da Aka Kashe Suna Dawowa. Kamar Yadda Muka Nuna Muku Irin Kudaden Da Ake Samu A Baya Kowane Wata.

Anan Muka Kawo Karshen Wannan Rubutu, Muna Rokon Allah Da Yasa Sakonmu Ya Isa Ga Wadanda Muka Aikawa. Idan Kana Da Tambaya Kai Tsaye Kayi Ta Comment Zamu Amsa Maka. Alhamdulillah.

Hausa Cinema

Hausa Cinema The Best Website In Africa Delivering The Latest News, Entertainment, Educational Articles And Many More About The Hausa People.

Leave a Reply

Related Articles