Hausa Novels

Tsintacciya Hausa Novel Complete Document [Download Now]

Download Tsintacciya Complete Hausa Novel Document for free on Hausa Cinema Novels. On this page, you are going to get and download tsintacciya Hausa novel complete document for free on your phone. Firstly, if you are to download tsintacciya welcome to Hausa Cinema, a website that brings you the latest Hausa novels in PDF formats for free to download. In addition, all the novels on this website are complete and well complied. Likewise, tsintacciya novel is among the best and complete Hausa novels we have on our list.

NameTsintacciya Hausa Novel
AuthorNimcy Luv
GenreLove, Relationship
PublisherHausa Cinema
Number Of Pages
Book Size
Date Published03 October 2022
LanguageHausa Language
Adult ContentNo
KeywordsTsintacciya Hausa Novel

Tsintacciya Hausa Novel

Tsintacciya Hausa Novel is a paid Hausa Novel written by Nimcy Luv. The novel is among the best and popular Hausa novels in 2022. You can now find and download free tsintacciya Hausa novel complete on Hausa Cinema Novels.

How To Download Tsintacciya Hausa Novel

If this is your first time visiting Hausa Cinema Novels, you need to know that all our novels here are 90% in PDF format. Therefore, you need to get a PDF Reader which can help you open and view the complete novel from your phone. If you don’t have WPS go here and Download PDF Reader Apk Pro Version for free.

Tsintacciya Complete Hausa Novel

Tsintacciya Hausa Novel Complete Document

Faɗawa Jikinsa Tare Da Sakin Wata Gigitacciyyar Ƙara Wacce Ta Sanya Akeem Saurin Ware Narkakkun Idanunsa Tare Da Sauke Ganinsa A Kanta, Wani Irin Murɗewa Jikinta Yake Tamkar Ba Mutum Ba, Ga Wani Rawa Haɗi Da Kyarma Da Ɓari Da Naman Jikinta Ya Shigayi Kana Ganin Akeela Kasan She’s Not On Her Right Sense, Irin Something Is Fishy Ɗin Nan, Tsintacciya Complete Hausa Novel.

Recommended: Tantiranci Ko Karuwanci Hausa Novel Complete Download Now

Gajiyayyun Idanunsa Kawai Ya Sauke Akanta Yayinda Zuciyarsa Ta Shiga Wani Irin Masifafan Harbawa Fuskarsa Babu Walwala Ko Kaɗan, Baƙin Ciki Da Haushin Yadda Ta Faɗa Masa Jiki Yafi Masa Komai Ciwo, Cikin Ɓacin Rai Bai Ba Duba Condition Ɗin Da Take Ciki Ba Ya Wani Irin Miƙewa Tsaye Da Sauri Tare Da Sanya Hannunsa Ya Fisgota Haɗi Da Mannata Jikin Bangon Parlon Nasa, Idanunsa Na Wani Irin Ruwan Zallar Bala’i Ya Mannata Da Jikin Bangon Tare Da Sanya Hannunsa A Wuyanta Ya Shaƙeta Yadda Jikinta Ke Rawa Haka Nasa Ke Rawa, Yama Kasa Magana Saboda Tsananin Ɓacin Rai, Tsintacciya Hausa Novel.

Cikin Tsananin Ɓacin Rai Ya Buɗe Bakinsa Cikin Wata Kakkausar Murya Yace “You’re Mad Jakaness, Jikina Sa’anki? Eh? I’ll Killed You Village Gal” Ya Faɗa Jijiyoyin Kansa Sun Fito Sunyi Raɗa Raɗa Idanunsa Yay Wani Mahaukacin Jaaa Gaba Ɗaya Ya Fita A Hayyacinsa Ba Zaka Ɗauka Mai Hankali Bane Saboda Yadda Yake Huci Kamar Kumurcin Maciji.

Cikin Wata Iriyar Murya Mai Tsanani Taushi Da Kuma Amsa Kowa Akeela Ta Buɗe Bakinta Tare Da Faɗin “Mune Zaka Kashe Ko Ita? Duk Abinda Zakai A Yanzu Mu Zakaiwa Domin Ita Ɗin Bata Da Wani Laifi Mune Ne Muka Ziyarce Ka” Wani Irin Kallo Yay Mata Har Zuwa Lokacin Idanunta A Lumshe Suke Suna Zubar Da Ƙwalla, Girgiza Kai Yay Yana Wani Irin Taune Bakinsa Cikin Ransa Yake Faɗin “Za’a Rina Gayyar Aljanu Kawai” Ɗago Idanunta Yay Wanda Sukai Wani Irin Bala’in Jaaa Kafin A Hankali Murya Babu Wasa Yace “Open Your Eyes” Girgiza Masa Kai Tayi Zaka Ɗauka Tasan Abinda Ta Keyi Kafin Tace “I Can’t” Cije Baki Yay Yana Wani Ƙara Shaƙe Mata Wuya Cikin Ɗaga Murya Yace “Open Your Eyes” Da Sauri Itama Ta Sake Girgiza Masa Kai Tace “Ban Mu Iyawa” Kafin Akeem Yay Magana Didi Wacce Ta Shigo Tayi Saurin Faɗin “Tsinannu Gantalallu, To Ubanwa Kuka Ajjiyewa A Jikinta? Wallahi Ii”ilafi Ƙurash, Tub! Tub! Tub! To Basai Kuci Kanku Ba Allah Kurwarta Ɗaci Gareta” Ta Faɗa Tana Riƙe Zani Dake Neman Faɗuwa A Hankali Abbu Ya Shigo Sai Mami Kana Ummi Ta Shigo Sanye Da Hijab Idanunta Akan Akeem Kasa Magana Tayi Dan She Can’t Believe Ace Wai Akeem Yayma Akeela Haka.

Recommended: Fuska Uku Hausa Novel Complete Download Now

Cikin Ɓacin Rai Abbu Yace “Well-Done Abdul-Hakeem Bukar Bello, Well-Done” Ya Faɗa Yana Ƙarasawa Wajan Da Sauri Akeem Ya Saki Wuyan Akeela Tayi Wani Luuu Zata Faɗi Cikin Zafin Nama Abbu Ya Rungome Ta A Jikinsa Yana Ƙara Kwantar Da Ita Cike Da Ɓacin Rai A Kuma Karon Farko Na Rayuwarsa Ya Kalli Akeem Yace “What Nonsense! Eh? Kasheta Zakai Eh Dr Nace Mekai Mata Da Harta Suma Haka Eh?” Shiru Akeem Yay Kansa A Ƙasa Idanunsa A Lumshe Wani Irin Baƙin Ciki Da Kuma Tarin Tsanar Akeela Ya Ƙara Nunkuwa Cikin Zuciyarsa, A Karo Na Farko Na Rayuwarsa Ta Dalilinta A Yanzu Ta Sanya Mahaifinsa Yana Ɗaga Masa Murya A All His Life Har Kawo Yanzu Bari Wannan Bata Haɗa Shi Da Abbu Ba Amma Yanzu Da Girmansa Da Komai Har Ƴar Ajjiye Akan Wannan Yarinyar Mai Kama Da Tsintacciya A Idanunsa  Mahaifin Zai Masa Faɗa, Tsintacciya Hausa Novel.

Ummi Dake Tsaye Tace “Akeem” A Hankali Ya Ɗaga Idanunsa Wanda Sukai Jajirr Ya Kalleta Kamar Bazai Magana Ba Sai Kuma Yace “Ummi..,”

Wata Tsawa Ta Daka Mai Wacce Tunda Yake Bata Taɓa Yi Masa Irinta Ba Kafin Tace “Shut Up! Akeem This Is Not How I Train You Ƴar Uwarka Jininka? Eh Akeem? Where Is Your Heart Da Har Zaka Sanya Hannunka Ka Shaƙe Wuyan Yarinya Nan, U Hate Her Is Your Problem Amma Baka Da Ikon Da Zaka Sanya Hannunka A Kanta Idan Har Ba Kuskure Ta Aikata Ba, Ko Dan Ciwonta Ai Ka Daga Mata Haba, Bata Zo Nan Daka A Wulaƙanta Ta Ba, Baka San Wacece Ita Ba Ko Do You Know What Gal Has Been Through?

Ka Ban Mamaki Baici Ace Kayiwa Jinin Baffa Haka Ba, Da Kasan Waye Baffa Da Bakaiwa Abinda Ya Haifa Haka Ba Wallahi Zan Baka Mamaki” Mami Wacce Ke Tsaye Ranta Duk Ya Ɓaci Domin Har Cikin Ranta Take Jin Faɗan Da Akewa Akeem Wai Kuma Akan Wannan Yarinyar Cikin Jin Haushi Tace “Haba Ummi It Was A Mistake Wanda Kowa Nayi Kunsan Akeem Ba Mai Shiga Sabgar Mata Bane, Inside Of Ku Tambayi Dalilin Zuwan Ta Part Ɗinsa Sai Ku Hau Yaro Da Faɗa”

Da Sauri Didi Tace “A Toh! Yau Ni Naga Ruwan Masifa Ai She Daman Indo Ba Ƙaunar Yaron Nan Kike Ba? Kai Ma Da Laifinka Wallahi Idan Nace Ka Kaf Faɗin Gidan Nan Nine Kawai Ke Sonka To Daman Idan Bani Ba Wazai So Ka Ai Nice Dolenka” Kai Akeem Ya Ɗaga Tare Da Kallon Abbu A Hankali Kuma Ya Kalli Ummi Da Sauri Kuma Ya Nufi Saman Sofa Ya Ɗauki Car Key Ɗinsa Ya Nufi Fita Waje, Cikin Sauri Ummi Tace “Akeem Where Are You Going Ina Ne Zaka Nine Kayiwa Zuciya?”

Recommended: List Of Hausa Novels And Websites To Download For Free 2022

Ko Tsayawa Bai Ba Bare Ta Sanya Ran Cewa Zai Dawo, Hankalin Abbu Ne Ya Tashi Domin Yana Masifar Son Akeem Kamar Ransa, Ya Rasa Adnan Bazai Saken Da Zai Rasa Akeem Ba Salati Didi Ta Fasa Tace “Huuuu! Jama’a Mun Shiga Uku Wanne Irin Gantalallan Bukari Ya Samu Ne? Anya Ba’a Sauya Maka Shi A Asibiti Ba Wannan Baƙar Zuciya Har Ina, To Wallahi Sai Dai Kaci Kanka Tass”  Wani Irin Miƙa Akeela Tayi A Jikin Abbu Bakinta Na Motsawa A Hankali Kuma Tace “Abbu Hamma Akeemmm Kada Ya Fita”

Recommended: Saran Boye Hausa Novel Complete Document Download Now

Da Sauri Didi Tazo Tana Dungure Mata Kai Tace “Annamimiyya Mai Zubin Munafukan Farko Ashe Kina Ji Kikai Shiru Waike Salammiya” Yanayin Akeela Yasa Ummi Saurin Cewa “Abbu Anya Ba Mutanan Ɓoye Bane Kuwa?” Kafin Abbu Yay Magana Akeela Ta Fasa Wata Gigitacciyyar Ƙara Tare Da Zabura Ta Nufi Waje Da Gudu, Cikin Sauri Abbu Ya Mara Mata Baya Yana Faɗin “Akeela! Akeela!!”

Ganin Yadda Take Gudun Kamar Barewa Abbu Bai San Lokacin Da Yace “Babyna, Babyn Abbunta Stop” Daga Ummi Har Mami Babu Wanda Yasan Me Yake Nufi, Cikin Zafin Nama Kuma Akeela Tai Waje Gaba Ɗaya Kasancewar Ƙofar A Buɗe Take Saboda Ficewar Akeem Daga Cikin Gidan, Download Tsintacciya Hausa Novel Document.

Kai Tsaye Gate Ta Nufa Shima Yana Buɗe Gaba Ɗaya Ta Fice Daga Cikin Estate Ɗin Tana Sharara Uban Gudu, Daga Ita Sai Nightgown Gashinta Duk A Zube Tamkar Mahaukaciya A Haka Ta Nausa Kan Titi Babu Ko Slippers.

Fitowa Abbu Yay Zuwa Complete Ɗin Yana Faɗin “Bala, Isa, Rabi’u” Ya Shiga Kiran Driver Da Gatekeeper Da Mai Shukar Flowers, Amma Gaba Ɗaya Babu Ko Wanne Bacci Duk Suke, Jin Shiru Yasa Abbu Komawa Da Gudu Cikin Gidan Dai-Dai Lokacin Kuma Su Afaf Suka Fara Daga Baccin Da Suka Fara Domin Duk Da Wuri Suke Bacci, Tsintacciya Hausa Novel.

Recommended: Jiddatul Khair Hausa Novel Complete

Car Key Ya Ɗauka Ya Fito Da Sauri Mami Tace “Ina Zaka At This Time?” Bai Ko Kalleta Ba Ya Nufi Wajan Ɗaya Daga Cikin Motocin Sa Ya Shiga Key Yay Mata Ya Fita Da Gudu Tare Da Barin Estate Ɗin, Kuka Didi Tace “Bukari Ka Kawo Masifar Duniya Gidanka”

Cikin Damuwa Ummi Tace  “Didi Aljanu Ne Da Yarinyar Wallahi Kuma Sune Suka Tashi” Wani Zaro Ido Waje Didi Tayi Tace “Muhammadur Rasulullah S.A.W Shine Ke Kuwa Kikai Min Shiru Itana Da Surutu Yau Na Shiga Wallahi Gidan Zan Bari” Juyawa Mami Tayi Ta Shige Ciki Ummi Ba Haka Da Gudu Didi Tabi Bayansu Har Zaninta Na Faɗuwa.

Akeem Kuwa Yana Fitowa Kai Tsaye Motarsa Ya Nufa Idanunsa A Lumshe Ko Ganin Gabansa Ba Yayi, Wani Irin Zafi Da Tafasa Zcuiyarsa Ke Masa, Yana Shiga Motar Ya Jata Da Gudu Bayan Ya Danna Wani Hargitsastsan Horn Da Dauri Isa Ya Tashi Daga Baccin Da Yake Ya Buɗe Masa Gate Fita Yay Da Motar Yana Ƙara Gudun Motar Tafiya Yay Mai Nisan Gaske Har Yabar Gaba Ɗaya Cikin Rail Way Ɗin Kafin Ya Nemi Hanya Yay Parking Motar, Kansa Ya Kifa Akan String Motar Yana Sauke Wani Zazzafan Numfashi Jikinsa Duk Rawa Yake Amma Har Kawo Lokacin Fuskarsa Bata Nuna Damuwar Da Yake Ciki Ba Sai Idanunsa Kawai Da Suka Sauya Kala.

Akeela Kam Gudu Kawai Take Tana Bin Sahun Motar Akeem Tun Tana Gudu Kaɗan Har Ta Fara Mai Yawa, Kasancewa Gudun Ba Nata Bane Na Iskane Yasa Itama Ta Fice Daga Cikin Rail Way Ɗin, Download Tsintacciya Novel.

Akeem Na Zaune Cikin Motar Yana Sauke Numfashi A Hankali Ya Ɗaga Kansa Dai-Dai Lokacin Da Akeela Tazo Ta Gaban Motarsu Ta Shige, Bayanta Yabi Da Kallo Yana Ganin Yadda Take Gudu Tamkar Mahaukaciya Tun Yana Iya Ganinta Har Ta Ɓace Masa Da Gani, Taɓe Bakinsa Yay A Hankali Yay Baya Tare Da Kwanciya A Jikin Kujerar Motar Yana Maida Numfashi Tare Da Dafe Kansa Wanda Matsanancin Harba Masa.

Duk Inda Abbu Yake Tunanin Ganin Akeela Ya Duba Amma Babu Ita Tashin Hankalin Mara Misaltuwa Ya Sauka Akan Fuskarsa, Yasan Akeem Tun Inda Yake Sai Kula Da Kansa Amma Akeela Waye Ta Sani A Wannan Garin? Musamman Wannan Hargitsastsiyar Unguwar Tasu, Jiki Babu Ƙauri Ya Koma Gida Har Wayewar Gari Basu Runtsa Ba,Didi Data Rufe Idanunta Zata Buɗe Da Sauri Tana Faɗin “Muhammadur Rasulullah S.A.W”

Washe Gari Wajan Ƙarfe 8 Na Safe Lokacin Tuni Abbu Ya Gama Bada Cigiyar Akeela Both Side TV, Radio, A Hankali Motar Akeem Take Shigowa Cikin Estate Kai Tsaye Kuma Gate Ɗin Gidan Su Ya Nufa Yana Zuwa Isa Ya Buɗe Mata Gate Ya Shiga Tun Kafin Ya Fito Daga Motar Cikin Ɓacin Rai Da Kuma Tashin Hankali Abbu Ya Nufi Kan Akeem Gadan Gadan Domin Rashin Akeela Dai-Dai Yake Da Rasa Rayuwarsa…

Download Tsintacciya Hausa Novel Document

Here is the file document of Tsintacciya, click on the download button and download it for free on your phone now.

4.3/5 - 105 Votes

Hausa Cinema

Hausa Cinema The Best Website In Africa Delivering The Latest News, Entertainment, Educational Articles And Many More About The Hausa People.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Related Articles