Takun Saka Hausa Novel Complete Document By Bilyn Abdull

Takun Saka Hausa Novel

Takun Saka is a fictional Hausa novel book written by Billyn Abdul to educate and entertain Hausa novel readers over the world. Additionally, the novel was written in the Hausa language. Furthermore, the Takun Saka Hausa novel is among the trending Hausa novels people are reading in 2022.

You can download Takun Saka Hausa novel for free now. The novel Takun Saaka is also among the bookmark (album) created by the collaboration of five Hausa novel writers; Bilyn Abdul, Hafsat (Miss Xoxo), Mamu Gee, Safiya Huguma, and Hafsat Rano titled ‘Labaran Zafafa Biyar na 2022’. As a result, the number of readers (fans) is increasing every day.

Thus, Hausa Cinema Novels have provided free Takun Saka Hausa Novel documents for you in PDF format. Therefore, you can download the complete document of Takun Saka complete in PDF format for free now. So, after downloading the novel, you can view (read) it offline for free without data usage.

NameTakun Saka
TitleTakun Saka Hausa Novel
AuthorBilyn Abdul Ce
GroupZafafa Biyar Hausa Novels 2022
GenreLove
LanguageHausa Language
Document TypePDF
Size 2.2MB
Words151,056
Pages480
Published DateSeptember 2022
Keyword Takun Saka

[ads1]

[button color=”primary” size=”medium” link=”https://hausacinema.com/wp-content/uploads/2022/09/takun-saka-hausa-novel-download-from-hausa-cinema.pdf” icon=”fa-download” target=”true” nofollow=”false”]Download Takun Saka Hausa Novel[/button]

[ads2]

Download Takun Saka Hausa Novel Complete

Takun Saka Hausa’s novel story is written fictionally based on love, relationship, and betrayal. Furthermore, the novel listed as the most popular and trending Hausa novel was added in 2022. And also, the novel book was written in the Hausa language to entertain, educate, and motivate Hausa novel readers (fans) around the world.

Hausa Cinema is here to will help you browse and download the Takun Saka Hausa Novel document for free now.

[ads1]

How To Download Takun Saka Hausa Novel

To download Takun Saka Hausa novel complete document in PDF format, you need to follow these steps:

 1. Firstly, you need to install a PDF reader on your device.
 2. Secondly, go to Hausa Cinema and search ‘Takun Saka Hausa Novel’.
 3. Thirdly, click on the first result given by the results on Hausa Cinema.
 4. Finally, proceed to the download page and hit on the download button.

The document will automatically download to your phone in a few seconds. Then, you can be able to view the file offline.

You can also download Jiddatul Khair Hausa Novel Complete.

[ads1]

Takun Saka

Takun Saka Hausa Novel Complete Document By Bilyn Abdull

A Gidan Ummi Komai Ya Canja. Gaba Ɗaya Ya Ranta Sun Bar Walwala. Sun Daina Fara’a. Sun Daina Zaman Hira, Abinci Ma Kaɗan Suke Tsakura. Idan Tai Magana Suce Sun Ƙoshi. Ta Ko Ina Ta Gaza Gane Kansu.

Da Farko Tayi Biris Da Su, Duk Da Kuwa Ta Fahimcesu Tsaf. Sai Dai Ganin Abin Nasu Bana Ƙare Bane Sai Itama Lamarin Ya Fara Damunta. Dan Ita Kanta Sun Jefata A Cikin Kaɗaici.

Hatta Da Hibbah Ƴar Karamarsu Itama Ta Ɗauke Mata Wuta. Saboda Wannan Abun Daya Faru Ma Ta Tattara Ta Koma Makaranta Duk Da Yaya Abubakar Ya Hanata Zuwa Da.

[ads1]

Download Azima Da Aziza Mazizai Ne Hausa Novel Complete.

Duk Da Ta Ɗan Fuskanci Ƙalubale A Wajen Mutane A Ranar Data Koma Saboda Tafiya Da Itan Da Ƴan Sanda Sukazo Sukayi Ranar Haka Ta Daurema Zuciyarta Ta Cigaba Da Zuwa. Bakuma Ta Sanarma Kowa Ba. Dan A Ganinta Da Zaman Gidan Su Tana Cigaba Da Ganin Abba Da Baƙinsa Gara Kallon Da Ƴan Makarantar Zasu Mata.

[ads1]

Download Sakatariya Ta Complete Hausa Novel – Free Download Now

Tunfa Ummi Na Ɗaukar Lamarin Nasu Wasa Sai Ƙara Girmama Ya Keyi. Dan Kwanakin Nan Biyu Ma Basa Dawowa Gidan Sai Sun Dai-Daici Tayi Barci Sannan. Hankalinta Sosai Ya Kuma Tashi. Ga Damuwar Yaranta, Ga Damuwar Auren Da Aketa Ƙulle-Ƙullen Nana Musu Na Son Zuciya.

Wanda Tsaf Ta Gama Fahimta Da Gane Ina Hakan Ya Dosa. Sarai Ta Gane Manufar Abbah Akan Son Ƙulla Auren Ƴaƴanta Da Nashi, Manufar Kuma Duk Ɗaya Ce Tsakaninsa Da Hajiya Mama.

Download Yar Yadikko Hausa Novel Complete PDF Document.

[ads1]

Gaba Ɗaya Ta Rasa Ina Zata Saka Kanta Taji Sanyi, Babu Uwa Babu Uba, Babu Abokin Shawara A Cikin Ƴan Uwa, Babu Wanda Zata Kaima Ƙara Ya Duba Matsalarta Ya Share Kukanta. Gudun Abinda Zaije Ya Dawo Kuma Ke Sakata Kwaɓar Ƴaƴanta Akowane Lokaci. Bata Son Abinda Zai Rabata Da Su. Bata Son A Cutar Mata Da Su. Dan Sune Hope Ɗinta, Sune Murmushin Fuskarta.

Sune Masu Share Hawayenta Da Tun Tana Ƴar Ƙanƙanuwarta Suke Kwaranya A Bisa Kumatunta. Tasan Nuna Ƙarfinsu Ya Kawo Kuma Zai Iya Zama Sanadin Da Komai Abba Zai Iya Aikatawa A Garesu Domin Samun Cikar Burinsa, Kuma Kamar Yanda Yasha Faɗa Koda Ya Salwantar Da Rayukansu Babu Mai Yarda Shine Ya Aikata. Wasu Hawaye Ne Masu Zafi Suka Silalo Mata Saman Fuska.

Wata Banzar Dariya Abba Da Ke Shigowa Cikin Sashen Ya Shiga Tuntsurawa Yana Tafa Hannaye. Cike Da Izgili Ya Dubeta Sheƙeƙe Yana Faɗin, “Kuka Kuka Kuka! Ai Kuwa Yanzu Kika Fara Kuka Asiya. Yo Ina Jarumtar Taki Ne Yau? Shin Har Kin Fara Zuwa Ƙasa Ne Tunkan Ma A Ɗaura Auran Manufarsa Kuma Ta Tabbata?. Tunda Har Kikace Ni Ban Isaba Asiya, To Wlhy Kema Bazaki Taɓa Isa Ba.

Yau Ina Wanda Kike Gadar Da Shi? Ya Tafi Tamkarma Ba’ayisa Ba. Abinda Kika Hanashi Yay Mana Ta Hanyar Zagon Ƙasa Ya Dawo Hannunmu A Lokacin Da Ko Ido Baki Isa Ɗagawa Akai Ba. To Suma Ƴaƴa Mazan Da Kike Ɗagawar Kin Haifa Masa Zasu Mamaye Komai Tafin Hannunmu Zasu Cigaba Da Zama Ballagaza Kawai. Zaki Iya Tashi Kuma Mu Shige Ciki Dan Ina Bukatar Haƙƙina. Inba Hakaba Kuma Zan Ƙwata Anan Cikin Falon Babu Ruwana….”

[ads1]

Download Jarababben Namiji Hausa Novel Document.

Hanyar Bedroom Ɗinta Ya Nufa Yana Gama Faɗa Alamar Ta Biyosa. Ummi Da Ke Jin Wani Ƙullutun Abu Yazo Ya Tokare Maƙoshinta Ta Shiga Karanto Duk Addu’ar Da Tazo Mata A Saman Harshe Saboda Jin Numfashinta Na Fita A Gwagwgwame. A Hankali Sanyi Ya Rinƙa Shiga Cikin Ƙashinta, Yayin Da Jikinta Ya Fara Wani Irin Rawa, Har Haƙwaranta Na Haɗuwa Waje Guda.

Hannu Takai Domin Lalubo Wayarta Da Ke Saman Centre Table. Sai Dai Hakan Ya Gagara Sakamakon Gushewar Gani Da Ta Risketa A Lokaci Ƙanƙani. Hannunta Ya Goce Da Ga Lalube Wayar, Sai Gata Ƙasa Wanwar Da Ga Saman Kujera…..

A Dai-Dai Wannan Lokacin Hibbah Ta Shigo Tana Masifar Bibiyarta Da Kullum Shuraim Keyi Babu Fashi Balle Nuna Gajiyawa Duk Da Yarfatashin Da Take Yi A Kulum. Data Fita Da Ga Gida Zuwa Makaranta Yana Biye Da Ita. Hakama Idan Ta Dawo Sai Ya Rakota Har Gida Ta Hanyar Bibiyarta. Zuwa Yanzun Tun Lamarin Nasa Na Bata Mamaki Har Ya Koma Takaici Da Al-Ajab.

Har Tabbayar Kanta Take Shin Baida Aikinyi Ne Ko Mi?. Wannan Takaicin Nasane Ya Sata Yau Ana Saukesu A Napep Taje Tai Masa Knocking Glass. Yana Saukewa Ta Balbalesa Da Masifa Batare Data Yarda Sun Haɗa Ido Ba Dan Karma Yay Mata Kwarjini. Sai Dai Abin ALLAH Wadai Da Takaici, Harta Gama Masifar Tata Ma Bai Nuna Yaji Haushi Ba. Sai Ma Murmushin Da Ya Nema Rikita Mata Lissafi Ya Sakar Mata Yana Wani Narkewa A Cikin Kujera.

Wani Uban Kara Ta Ƙwalla Tana Isa Inda Ummi Ke Kwance Wanwar Tana Wani Irin Tari Dake Fita Da Ƙyar. Kiran Sunanta Ta Shigayi Tana Girgizata Hankali Tashe. Sai Dai Ina Ummi Ta Fita Hayyacinta. Dabarar Rarumar Wayar Ummin Ce Tazo Mata A Rai. Batare Data Nutsu Wajen Ganin Wanda Ta Kira Ba Kawai Tai Dailing Numbern Farko, Dan Tasan Su Ne Dai Kawai Suke Yawan Kiran No Din Ummin Tasu A Koda Yaushe.

[ads1]

“Yaya Dan ALLAH Kazo Gida, Ummi…Umminmu. Na Shiga Ukuna. Ummi Dan ALLAH Ki Tashi. Wlhy Kika Mutu Nima Mutuwa Zanyi. Dan ALLAH Ummi Na Roƙeki Karki Mutu. Wlhy Bazamu Sake Yin Fushi Da Ke Ba. Mun Tuba Ummi, Mun Daina. Mun Yarda Zamu Auresu Ummi…….”

Sambatu Taketa Faman Yi Tama Manta Da Waya A Kunnenta. Kukanta Ya Fiddo Abba Da Ga Ɗakin Ummi Ɗin Wando A Hannu. Dan Harya Cire Kaya Ya Baje A Gado Yana Jiran Jakarsa Ta Shigo Ya Murza A Wulaƙance.

Ido Huɗu Sukai Da Hibbah Da Ke Sake Ƙwala Kuka Tana Kiran Ummi Da Girgizata. Ai Sai Ta Sake Fasa Wata Ƙarar Ganin A Yanda Ya Fito, Saboda Bai Saka Wandon Dai-Dai Ba An Samu Mishkila Wajen Bayyanar Jikinsa.

[ads1]

Sakin Ummi Tai Ta Fita A Guje Da Ga Sashen Baki Ɗaya Jikinta Na Rawa. Tana Da Yayu Maza Manya. Amma Tunda Take Da Su Ko Zama Da Singlet Da Boxers Basu Taɓa Yi A Gabanta Ba Balle A Yanayin Da Abban Ya Fito Wanda Bata Taɓa Ganin Wani Mahaluki A Yanayin Ba.

Jikinsa Ta Faɗa Dai-Dai Maigadi Ya Buɗe Masa Gate Ya Shigo, Dan Hibbah Wayarsa Ta Kira Saboda Shine Na Ƙarahe Da Ya Kira Ummi Yaji Yaya Jikinta? Dan Ya Kwana Biyu Baizo Gidan Ba. Duk Yanda Yaso Ganin Ya Janyeta A Jikin Nasa Hakan Ya Gagara.

Sai Sake Ruƙunƙumesa Takeyi Jikinta Na Rawa, Yayinda Taketa Faman Son Ɓoye Fuskarta A Ƙirjinsa Duk Da Tsahon Nata Gaba Ɗaya Iya Ƙirjin Nasa Ta Tsaya.

Cikin Zafi-Zafi Ya Shiga Tureta Yana Girgizata. “K Muhibbat Nutsu, Muje Inga Ummin Gani Nazo”.

Jin Muryar Da Bata Yayunta Ba Ya Sata Saurin Ja Da Baya Tabar Jikinsa. Isma’il Da Ya Samu Ta Rabu Da Jikin Nasa Da Sassarfa Yay Gaba Abinsa Zuwa Sashensu Har Yana Haɗawa Da Ɗan Gudu-Gudu. Kusan Cin Karo Sukai Da Abbah Da Ya Koma Ya Ɗakko Kayansa Saboda Ihun Da Hibbah Tayi Ya Farga Da Halin Da Yake A Ciki. Duk Da Ya Kuma Ga Ummi A Yashe A Ƙasa Sai Kawai Firgici Biyu Ya Kamashi.

Na Farko Kar Wani Yazo Ya Gansa A Yanda Yake Sakamakon Ihun Hibbah A Zata Wani Abu Yaso Mata Har Ummi Ta Shiga Halin Da Take Ciki A Yanzu. Dan Haka Ya Fito Dan Ya Gudu Salin Alin, Idan Hibbah Ta Sako Sunansa A Ciki Kuwa Yasan Ta Yanda Zai Kare Kansa Ai.

[ads1]

Haka Kawai Zuciyar Isma’il Ta Raya Masa Irin Abinda Abban Ke Gudu. Dan Haka Yasa Ƙafa Ya Taɗesa Sai Gashi A Ƙasa Tim. Takan Kafafun Abba Yabi Da Shaggun Takalman Ƙafarsa, Ji Kake Ƙasss Ƙashi Na Bada Sautin Karyewa Ko Tsagewa.

Wata Iriyar Wahalalliyar Ƙara Abba Ya Saki Tare Da Ɗaukewar Numfashi Na Wucin Gadi. Ko Waiwayensa Isma’il Baiyiba Ya Ida Afkawa Cikin Falon Inda Ya Hango Ummi A Ƙasa Itama Babu Alamar Rai Tattare Da Ita.

“Ummi!… Ummi! Ummi!!” Ya Shiga Ƙwala Mata Kira Da Kama Hannunta Yana Girgizawa. Sai Dai Babu Alamar Motsi Tare Da Ita Sam. Mikewa Yay Da Sauri Ya Ciro Wayarsa Yay Kiran Yaya Umar Da Yasan Shine Mafi Kusanci Da Gida. Sai Dai Bai Ɗaga Ba.

Tunawa Ana Sallar La’asar Yanzu Haka Ya Sakashi Cije Lip Ɗinsa Na Ƙasa Ya Cusa Wayar A Aljihu. Batare Da Tunanin Komai Ba Ya Ciccibi Ummi Gaba Ɗayanta Yay Waje. Sai Lokacin Hibbah Ta Nufo Falon Sabida Hango Abinda Isma’il Ɗin Yay Ma Abba.

“Muje Asibiti” Yace Mata Kawai Yana Nufar Hanyar Gate. Babu Musu Ta Bisa Tana Kuka Da Riƙe Hannun Ummi Ɗin Da Ya Ɗakko. Sai Lokacin Kuma Hajiya Mama Ke Fitowa Da Ga Sashensu Itama. Ta Bisu Da Wani Irin Kallo Mai Ma’anoni Da Yawa Saboda Ganin Baƙon Fuska Ɗauke Da Ummi Ɗin.

Dan Duk Zuwan Da Isma’il Ɗin Keyi Gidan Ba Taɓa Haɗuwa Sukai Ba. Wahalallen Ihun Da Abba Ya Saki Ne Ya Fargar Da Ita Halin Da Yake A Ciki, Babu Shiri Ta Runtuma A Guje Kansa Tana Ƙwala Kiran Sunansa.

[ads1]

Tun Kan Su Ƙarasa Asibitin Isma’il Yay Ƙoƙarin Kiran Doctor Bilal. Cikin Sa’a Kuwa Ya Ɗaga Dan Mutuminsa Ne. Bayani Yay Masa Cewar Gasu A Hanya Tare Da Mara Lafiya Su Zam Cikin Shiri. Dr Bilal Yace Babu Damuwa Sai Sunzo.

Cikin Mintuna Kalilan Kuwa Suka Iso Asibitin Saboda Uban Gudu Da Yake Zugawa A Hanya. Kamar Yanda Yay Fata Sun Sami Su Dr Bilal Na Dakon Isowarsu. Babu Ɓata Lokaci Aka Shiga Da Ummi Ciki.

Kuka Sosai Hibbah Keyi Da Son Binsu, Badan Yaso Ba Ya Riƙo Hannunta Yana Ƙoƙarin Dakatar Da Ita. Sai Dai Taƙi Ta Nutsu, Dole Yay Mata Yanda Yasan Zata Nutsun, Ya Jawota Jikinsa Ya Rungume. Da Ƙarfi Ya Rumtse Idanunsa Zuciyarsa Na Wani Irin Bahagon Gudu.

Hausa Cinema Novels

 1. Doctor Eesha Hausa Novel
 2. Lalata Hausa Novel Complete Document [PDF Download Now]
 3. Yar Dandi Ce Hausa Novel Complete
 4. Download Best And Complete Hausa Novels 2022
 5. Fansar Budurcina Hausa Novel Complete PDF Document
 6. Jihadi Hausa Novel Complete
 7. Macijine Shi Complete Hausa Novel
 8. Saran Boye Hausa Novel
 9. Gidan Dadi Hausa Novel Complete Document
 10. List Of Hausa Novels And Websites To Download For Free 2022
Scroll to Top