Hausa Articles

Soyayya – Abubuwan Da Yakamata Ka Sani Akan So 2023

A Wannan Rubutu munyi cikakken bayani dangane da soyayya. Ma’anar soyayya, yadda ake soyayya, sirrin so, illolinta, amfaninta ga rayuwar dan adam. Da duk wani abu da yakamata ka sani dan game da soyayya. Ba iya nan ba ba munyi bayanan ire-iren soyayya da kuma bayanansu da yadda suke.

Don haka yana da kyau ka samu ka karanta a nitse, domin mun inganta bayanin dai-dai da yadda mutum zai fahimta.

Menene Soyayya?

Soyayya Hadaddiyar Motsin Raice dake haddasa wasu halayya, girmamawa, mutuntawa, tausayawa, da kuma kauna ko shaki. Akan shiga yanayi na dimuwa da kan haddasa gushewar kwakwalwa ko hankali a lokacin da soyayya ta kai koluwa. A saukin harshe idan aka ce soyayya ana nufin haduwar ruhi.

Soyayya ce mai sarkakkiyar fuska, mai dimbin yawa da ke zama muhimmin bangare na rayuwar dan Adam. Tana iya kawo farin ciki mai girma da farin ciki, amma kuma tana iya kawo zafi da bacin rai. Duk da haka, ƙauna wani motsi ne mai ƙarfi kuma mai dorewa wanda zai iya taka muhimmiyar rawa a rayuwar mutane.

Ita oyayya ba lallai bane sai ya kasance na saurayi da budurwa, a’a. Shima wannan wanin nau’i na so daban wanda yana daga cikin nau’ukan so wadanda sun kai goma ko fiye da hakan. Ka taba jin kana son wani ko wata haka kawai kaji sun burge ka?

Misali; Akwai wata yarinya da ta hadu da wani saurayi a jami’ar Bayero University Kano (BUK). Sai abota ta shiga tsakaninsu, shi wannan matashi yana mata kallon masoyiya wacce zasuyi soyayya irin ta Laila da Majnoon. perfect watches phone number Ita kuwa ta dauke shi ne a matsayin class mate, da aka hadu kuma za’a rabu, a tsaein soyayya baya ra’ayinta. A gurguje dai daga karshe wannan matashi ya zo bayyana soyayyarsa, tace gaskiya ba zata iya Ba.

Ire-Iren Soyayya

Akwai ire-iren soyayya da dama wadanda dan adam yake fadawa cikinsu. Wasu suna shiga soyayya ba tare da sanin wani iri bane suka shiga, wanda hakan wasu lokutan yakan janyo matsala.

Soyayyar Namiji Da Mace (Romantic Love)

Irin wannan soyayya itace asalin wacce kowa ya sani kuma tafi yawa a cikin al’umma. Bugu da kari itace tafi tasiri a zuciyar dan adam fiye da kowace iriyar soyayya da muke dasu. Wannan soyayya da bature yake kira Romantic Love ta kan gyara rayuwar mutum ko kuma ta lalata shi cikin kankannin lokaci.

Ta hanyar amfani da kalaman soyayya masu ratsa zuciya, kyautatawa, kulawa, tausayawa, da kuma girmamawa za’a iya inganta wannan soyayya na tsawon shekaru. Ba iya shekaru na nan duniya ba, ana iya inganta ta har izuwa bayan rai.

Itace dai soyayyar nan da take sanya mutune suke kashe kawunansu, suke guduwa daga wajen yan uwansu, suke makanta daga ganin baki su koma yi masa kallon far, ko kuma fari ya koma baki. Ita wannan soyayya itace dai ta kan janyo mai kudi zuwa daji, sarki zuwa lungu.

Soyayyar Abota (Platonic Love)

Wannan itace nau’in soyayya ta biyu da take da tasiri a rayuwar mutum. Itama wannan nau’i na soyayya tana da dadi kuma tafi inganci fiye da soyayyar Namiji da Mace. Haka zalika itama tana iya hallaka rayuwar mutum ko kuma ta gyara rayuwarsa. Ta hanyar soyayyar abota mutum yana iya zama mutumin kirki, ta hanyar soyayyar abota mutum yana iya lalacewa ya gagara yiwa rayuwarsa amfanin komai. Irin wannan soyayya tafi karfi, tafi tasiri, kuma tana da illa sossai.

Soyayyar Dangi (Familial Love)

Irin wannan nau’i na soyayya tafi sauran ire-iren soyayya din karfi (tabbas) ko kuma muce Guarantee a turance. Amma da shike yadda zamani yazo mana da wasu abubuwa na sauyi, wasu yan uwa din basu da tabbas.

Soyayyar Kai (Self-Love)

Kamar yadda sunan take ‘Soyayyar Kai’ na nufin soyayya ce da mutum yake yiwa kansa. Ita wannan soyayya bata bukatar yarda da wani, ko kuma tausayawa wani, A’a. Wannan kai zakaji tausayin kanka, ka girmama kanka, ka kuma yiwa kanka duk abinda yakamata, kamar Tsafta, Kula da Lafiya, Da sauransu.

Soyayyar Mutunci Ko Girma (Agape Love)

Wannan soyayya itama tana daga cikin manyan soyayya da muke dasu. Amma sai dai irin wannan soyayya bata da wani tasiri ga rayuwar dan adam. Wato kenan ita wannan soyayya ba zata iya canja launin mutum daga wata kala zuwa wata kalar ba, da wuya hakan. Saboda kalar soyayyace da wani zaiji yana son wani ko wata domin ya kyautata masa, ya girmama masa, ya taimakeshi.

Soyayya

Yadda Ake Soyayya

Zafafan Kalaman Soyayya

Kalaman Soyayya Na Mata

Kalaman Soyayya Na Maurata

Yadda Zaka Gane Mace Tana Sonka

Yadda Zaka Cire Soyayyar Mutum A Cikin Ranka

Wasikun Soyayya Zuwa Ga Budurwa Ko Saurayi 2023

5/5 - 7 Votes

Hausa Cinema

Hausa Cinema The Best Website In Africa Delivering The Latest News, Entertainment, Educational Articles And Many More About The Hausa People.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Related Articles