Hausa Novels

Shahaab Hausa Novel Document Free Download 2023

Download the Shahaab Hausa Novel Complete Document File By One Of The Hausa Writers, Amnah El Yaqoub. The Story Is Based On Love and Romance.

Novel TitleShahaab
AuthorAmnah El Yaqoub
GroupHausa Cinema Novels
Book TypeRomantic, Love
Book Size0.55MB
Total Pages100 Pages
Total Words100,000 Words
Published Date23 October 2023
KeywordShahaab Hausa Novel

Chamo, Dutse Area (Jigawa State)

Wata tsohuwa ce me kimanin shekaru Sittin da Shida tashiga cikin wani madedecin gida na masu qaramin qarfi, Sai mita take tana sababi “Haba! Wannan aba da’ake ganin darajarta, ake saka mata d’an kamfai, asaka mata siket, sannan ad’aura zani akai,yau itace a wangale wannan Yara na Asbiti Sai leqawa suke”

Ta qarasa maganar tanajan kujera ‘yar tsugunno tana zama, Ummah dake Gefe a zaune tana yanka albasa akan qanzo tace “Sannu da Zuwa Hajja, bade har yanzu bata haihu ba?”

[This Novel Was Downloaded From HausaCinema.Com]

Wadda aka kira da Hajja tace “bata haihu ba har yanzu,wannan yarinya tana ganin azaba, sunce fa tasamu yaga har waje hud’u”

Ummah ta zaro ido tace “Hud’u?”😳

Ta6e baki tayi tace “yaga Hudu Hadiza, wata yarinya tana nan Sai leqawa take, takasa tsinana mata abun Arziqi, nide nataho nabar jummai acan Sai dawurwuri take tana tsoro kar jikarta ta mutu”

“kode wata yarinya ce siririya, zaki ganta ‘yar doguwa itace take kar6ar haihuwar?” cewar Ummah

Hajja tace “itace inajin, tana nan wata Mai kamar Sanda de”

Ummah tace “Hajja tokode Sandar cema?”

Wadda aka kira da Hajja tace “Fad’i kanki tsaye Sandar cema, wannan qirji ashafe, ga uban tsawo, tun dazu take cewa ga kainan yataho Amma shiru kakeji, nikam nataho, idan ta sauka saina koma”

Wata yarinya ce tafuto daga d’akin Hajja,bazata wuce shekara goma Sha takwas ba, fara ce tas Me matsagaicin tsawo, tana Sanye da Hijabi madedeci ajikinta, kasancewar hijabin ba dogo bane hakanne yabawa bajajjan hips dinta damar bayyana, kallon su tayi duka su biyun, ta zabgawa Hajja Harara, sannan ta d’auki buta ta wuce bandaki, cikin ranta tana tunani tabbas zama da mad’aukin kanwa…. Gashi yanzu itama Ummah ta biyewa Hajja suna zagin baiwar Allah, fisabillillah banda sharrin Hajja tayaya za’ayi a cewa mutum Sanda?🤔

Hajja databi Bayan yarinyar da kallo tasaki ajiyar zuciya tace “mesunan qawa da masifa take, tunda tafara qirgen dangi muka shiga uku da saka hijabi acikin gidannan, kullum tana cikin Hijabi kamar abun masifa, d’an girgen dangin ne bataso mugani, inba hakaba mutum yayi ta yawo da hijabi muba had’a dangi mukai da limamai ba, wannan jaraba har Ina, da wannan zafin duniyar mutum zaiji koda yawo da Hijabi ”

Ummah tayi murmushi ba tace da’ita uffan ba, saide cikin ranta tace”kunfi kusa”

Adede lokacin yarinyar tafuto daga bandaki, har yanzu hararar Hajja take, tsugunna wa tayi tafara alwala, saida tazo wanke fuska sannan ta janye hijabin dake jikinta, lokaci d’aya tulun gashinta me santsi da tsawo ya bayyana, gashin har qyalli yake saboda yasha wanki, Hajja ta kalleta ta Ta6e baki sannan ta shige cikin dakinta inda yarinyar tafuto

Ummah ta kalleta tace “AISHA, idan kin idar da sallar ga qanzonku Nan keda Hajja”

Kafin ta amsa mata, Hajja tafuto daga cikin dakinta da robar Vanillah a hannunta tace “A a nikam bazan iyacin qanzon Nan ba, Jikar Jummai tana can a Asbiti rai a hannun Allah, Ina Naga tacin qanzo”

Wadda aka kira da Aisha, ta bude d’an qaramin bakinta Mai launin pink, cikin siririyar muryarta ta kalli Hajja tace “Amma ai gashinan hakan bai hanaki qulla Vanillah ba”

Kafin Hajja tabata amsa wani yaro yayi sallama yashigo yace “Hajja A’i, abani kunun Aya na Hamsin”

Kudin ta kar6a, tabashi kunun ayar tana fad’a masa “kadawo min da jarkar kaji”

Yaron yace “To” sannan yafice daga gidan…

Shahaab Hausa Novel

Aisha ta’idar da sallar, sannan tafuto tsakar gidan hannunta d’aukeda Radio tana kunna wa.

qanzon dake gaban Ummah ta d’auka, ta zauna akusa da Hajja, sannan ta ajiye Radion agefe, tayi Bismillah tafara cin qanzon,had’in qanzon yayi mata dad’i sosai, batasan lokacin data tamiqa hannunta taqara sautin Radion ba, Adede lokacin ne me karanta labarai take cewa”to masu sauraro kuci gaba

Sauraron Freedom Radio dake Nan jihar Jigawa domin samun rahotannin bidiyo da hotuna kan labarun Najeriya da Nijar da ma sauran sassan duniya baki daya,ayau ne Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kafa dokar hukuncin kisa ga duk wanda aka kama da laifin yi wa ƙaramar yarinya fyaɗe, acikin birnin tarayya Abuja kuwa, Shahararran d’an kasuwa, Kuma matashin Shugaban EFCC, Wanda akafi Sani da MAHMUD WAKILI, ya Bawa Yan qungiyar qwallon qafa ta Nigeria kyautar nera million talatin, sakamakon samun nasara dasukai har suka samu kyautar kofun zakarun nahiyar Africa, matashin de yaqware wajan aikin sa, inda yake aiki ka’in da na’in wajan ganin ya daqile cin hanci da rashawa acikin wannan qasar, MAHMUD WAKILI ya kasance….. ”

Cikin sauri takashe radion,batare dataji qarshan labaran ba,qasa tayi da kanta ta zubawa qanzon dake gabanta ido

Batasan meyasa ba kawai taji mutumin bai wani birgeta ba, menene abun birgewa anan da har gidan Radio zasu dinga yayatawa? saboda Allah duk cikin Wanda ya Bawa kudin Nan tasan cewa sunada Hali, ga talakawa barkatai suna buqatar taimako Amma manyan qasar basayi musu, saide a qarawa me qarfi wani qarfin, mutum ne zaka ganshi da ‘ya’ya samada guda shida, Amma bashida cin yau bare na gobe,yanzu Yan Ball za’a dauki kudi a basu har million talatin, jijjiga kanta tayi, cikin ranta tace “Allah yahad’ani dakai ko sau d’ayane arayuwa,a ranar zan manta cewa sunanka d’aya da mahaifina”

Hajja dake Gefe tace “masu abu da abunsu, yawanci zakiga masu suna Mahmud sunada kud’i, Amma ni nawa mahmud din Sai godiar Allah”

Daga Ummah har Aisha babu Wanda ya tanka mata, asalima Aisha ji tayi gaba daya ranta ya6aci Dajin labarin wannan mutumin, d’an qanzon datake ci taji yafita daga ranta, tashi tayi ta shige daki, tasauya hijabi domin shirin tafiya makaranta

Tana jiyo wayar Hajja tayi ringing, Hajjan ta d’auka tace “jummai ya’akayi? Me naqudar tasauka?”

Daga d’ayan bangaren jummai tace “tasauka Hajja, ansamu d’a namiji, yanzu ma gida nazo nadauka mata d’an kunun kanwa, nace ko za’a samu d’an sauran sikari (suger) awajanki zan zuba mata acikin kunun?”

Hajja tace “wallahi babu jummai, saide zuwa anjima zan siyo”

Jummai tace “to shikkenan” daga Nan takashe wayar

Aisha dake shirin futowa daga d’akin cikin ranta tace “Kai wannan mata da jarabar roqo take wallahi, jikar ki ta haihu Amma kikasa siyan sigan daza’a zuba mata acikin kunu Bayan ba kudin kika Rasa ba?🤔

Sallama tayi musu ta wuce makaranta, tanajin Hajja tana cewa”to me sunan qawa saikin dawo”

Tana fita tahangi qaninta jabir, kana ganinsa zakagano tsantsar kamar dasuke da juna, batace dashi uffan ba tawuceshi, shine yaga yanayinta kamar ranta a 6ace yace”me sunan qawar Hajja antafi ne?”

Share shi, cikin sauri ya qaraso wajanta ya fizge jakar littattafanta, cikin 6acin rai ta Kalleshi tace “JB Bani jakata Dan Allah, wallahi raina ne babu nishadi”

“keda Hajja ne?” yajefo mata wannan tambayar, ajiyar zuciya ta sauke tace “Wacce Hajja? Labari naji a Radio Wai shugaban EFCC MAHMUD WAKILI yabawa Yan qwallo kyautar kudi har million talatin jb, wallahi banason mutumin Nan, haka kawai naji bai kwanta minba”

Kwashewa da dariya jabir yayi yace “toke menene abun damuwa anan? Ke suna qoqari fa Yan Ball din, akwai su Big Brother manyan Yan ball ne,inde sunci ball menene aciki Dan anbasu kyautar kudi? Hakan zaisa su sake dagewa, muje na rakaki makarantar”

Ya qarasa maganar yana Jan hannunta, qwace hannunta tayi tace “yanzu Kai hakan be 6ata ma raiba? Nikam haushi yabani wallahi, Ina laifin ma yabawa talakawa kokuma nakasassu,har yanzu nema muke Asamu atara Maka kud’in registration katafi makaranta ko ‘yar legal Ringim dinnan ne kaima kaje kayi,Amma Yan Ball fa jb, jinake da zan ganshi sainayi masa tatas wallahi, wannan ya wuce kashe kudi saide almubazzaranci”

Dariya jabir yasake yi akaro na biyu yace “Wai wa Zaki Gani? Shi Mahmud din? Ke irin wannan mutanan waye yafada miki suna zama a qasar? Mutumin daya shahara afannin kasuwanci, ga Kuma Babban muqami a Gwamnati shine kike tunanin Zaki Gani a wannan qauyen? To banqi ba in waya Zaki Ara kiyi search din photonsa a opera kigani, Amma inba hakaba Ina muke da hanyar ganinsa”

Cikin masifa tace “in ari waya inyi searching din photonsa me hakan zai tsinana min?”

Cikin murmushi jabir yace “Arziqi zai tsinana miki”

Cikin 6acin rai tace “saide tsiya wallahi”

Suna wannan musun suka qaraso islamiya inda take koyarwa, abakin get din makarantar tahadu da qawarta Walida wadda suke koyarwa tare a makarantar,Walida tace “Aysha Mahmud yaude munzo tare”

Cikin son kawarda 6acin ranta ta amsa mata, sannan suka shige cikin makarantar shikuma jabir yajuya zuwa gida, Wani yaro ne yashigo gidan yace “Hajja A’i abani ruwa na nera goma me Sanyi”.

Download Shahaab Hausa Novel And Read Complete…

More Like Shahaab Hausa Novel

  1. 100+ Maganin Karfin Maza (Free Man Power) 2023
  2. Jarababben Namiji
  3. List Of Hausa Novels And Websites
  4. Gidan Uncle Hausa Novel
  5. Banana Island Hausa Novel

Hausa Cinema

Hausa Cinema The Best Website In Africa Delivering The Latest News, Entertainment, Educational Articles And Many More About The Hausa People.

Leave a Reply

Related Articles