Saran Boye Hausa Novel Complete Document Download Now

Saran Boye Hausa Novel Complete

Saran Boye is a fictional Hausa novel story which is written by Billyn Abdul to entertain and educate the Hausa novel readers online. Additionally, the novel was written in the Hausa language. Moreover, Saran Boye Hausa novel is part of the popular novels; it has a high number of supporters (readers) online. Thus, Hausa Cinema recommended you download and read Saran Boye by Bilyn Abdull.

Hausa Cinema Novels have provided free Saran Boye Hausa Novel documents for you in PDF format. Therefore, you can download the complete document of Saran Boye complete in PDF format for free now. And also, after downloading the novel, you can view (read) it offline for free without data usage.

Name Saran Boye
Title Saran Boye Hausa Novel
Author Bilyn Abdull
Group Zafafa Biyar Hausa Novels 2021
Genre Love
Language Hausa Language
Document Type PDF
Size 3.20MB
Words 232,332
Pages 641
Published Date September 2022
Keyword Saram Boye Hausa Novel PDF

[ads1]


Download

Download Saran Boye Hausa Novel Complete

Saran Boye Hausa novel story is written fictionally (created story) based on relationships, and betrayal. Moreover, the novel was added to the popular and trending Hausa novels list for 2021.

The novel Saran Boye is also on the album of Zafafa Biyar Hausa Novels (Zafafa biyar na 2021) which is created with the collaboration of five Hausa novel writers; Bilyn Abdul, Hafsat (Miss Xoxo), Mamu Gee, Safiya Huguma, and Hafsat Rano

Hausa Cinema is here to will help you browse and download the Saran Boye Hausa Novel document in PDF format for free now.

 

How To Download Saran Boye Hausa Novel

To download Saran Boye Hausa novel complete document in PDF, you need to follow these instructions:

  1. Firstly, download a PDF reader on your device.
  2. Secondly, go to the Hausa Cinema website and search ‘Saran Boye Hausa Novel’.
  3. Thirdly, click on the result given on Hausa Cinema.
  4. Finally, proceed to the download page and hit on the download button.

Finally, the PDF document will automatically download to your phone storage in a few seconds. Then, you can be able to view the file offline.

 

Saran Boye Hausa Novel

Rayuwa Ta Shuɗa, Kwanaki Nata Gangarawa, Inda Ake Neman Watanni Na Takwas Kenan Da Lalacewar Auren Nu’aymah Da Abdallah. Tana Cikin Tsananin Damuwa Da Begensa, Kullum Dare Sai Tayi Kuka, Tana Sonsa Matuƙa, Dan Ta Rayune Da Son Nasa. Yawan Damuwar Da Take A Cikine Ya Haifar Mata Da Yawan Yin Ciwo, Saboda Ciwonta Bayason Damuwa Sam. A Duk Sanda Ta Takura Kanta Da Tunani Da Damuwa Yakan Yawaita Motsa Mata Akai Akai, Tana Kuma Matuƙar Shan Wahala.

Gaba Ɗaya A Awatannin Nan Lafiya Taƙi Wadatarta, Haka Taketa Fama Yau Fari Gobe Tsumma. Gashi Baba Malam Kullum Cikin Mata Jan Ido Yake Akan Ta Kawo Ameer Yay Musu Aure. Tayi Kuka Tayi Rantsuwar Akan Ameer Ba Saurayinta Bane Amma Sam Yaƙi Ya Saurareta. Umm Kanta Wannan Al’amari Na Tada Mata Hankali. Amma Babu Yanda Ta Iya Ta Zuba Musu Ido Kawai Taga Iya Gudun Ruwan Mijin Nata.

Recommended PostsTakun Saka Hausa Novel Complete Document By Bilyn AbdullTsantsar Butulci Complete Hausa NovelJiddatul Khair Hausa Novel Complete.

Burin Nu’aymah Cigaba Da Karatu A Yanzun, Amma Baba Malam Yay Banza Da Maganar Karatun Nata, Bayan Kuma Kowa A Gidan Yasan Burinta A Rayuwa Shine Ta Zama Likita Ko Nurse Tun Tana Yarinya. Addu’arta Kullum Itace Baba Malam Ya Haƙura A Sake Nema Mata Makaranta Kafin ALLAH Ya Dawo Da Hankalin Abdallahnta Gareta, Dan Ita Duk Ɗaukarta Abdallah Fushi Yake Da Ita Akan Ta Gudu Ran Aurensu, Shiyyasa Yaƙi Nemanta Koda A Wayama. Ta Dage Da Azumin Litinin Da Alhamis Da Sallar Dare Tanata Gayama UBANGIJI Kukanta.

Ana Cikin Wannan Yanayin Su Baba Malam Suka Gama Shirya Gagarumar Walima Na Saukar Al-Qur’anin Yaransu Na Gidan Marayu, Tare Da Aurar Da Waɗanda Suka Samu Mazan Aure. Wasunsu Anan Cikin Gidan Suka Dai-Daita Kansu. Wasu Kuma A Waje Suka Samu Mazajen Aure Da Mata.

Shirye-Shirye Ake Babu Kaman Hannun Yaro, Dan Shinema Ya Ɗauki Baba Malam Busy Sosai Ya Samawa Nu’aymah Lafiya Daga Takurar Zancen Fiddo Mijin Aure. Duk Da Dama Dai Yana Matane Kawai Dan Hukuntata Ta Cikin Ruwan Sanyi Akan Abinda Ya Faru. Amma Ta Ƙarƙashin Ƙasa Neman Hanyar Ganin Likitan Nan Kawai Yakeyi Da Nema Mata Makaranta Batare Da Ko Umm Ta San Da Hakan Ba.

Ana Saura Sati Ɗaya Su Yusrah Suka Iso, Washe Gari Kuma Su Amal. Hakan Ba Ƙaramin Daɗi Yayma Nu’aymah Ba, Koba Komai Ta Rage Kaɗaicin Da Ta Tsinci Kanta A Cikin A Waɗannan Watanin Ai. Abinda Ya Ƙara Faɗaɗa Farin Cikin Natama Shine Amal Da Yusrah Bazasu Komaba, Dan Zasu Zaunan Zana Jarabawar Ssce Anan. Cikin Kwana Biyu Kacal Da Dawowar Tasu Ta Fara Komawa Cikin Walwalarta.

Tuni Suka Fara Addabar Gidan Da Ƙiriniyarsu Da Bata Ƙarewa, Sauƙinma Babu Adawiya, Amma Hakan Baisa Sun Fasa Abinda Suka Saba Yiba. Tun Ana Saura Kwana Uku Suka Saka Hajjo Ta Roƙa Musu Baba Malam Komawa Cikin Gidan Marayu Har Sai An Kammala Komai. Dan Yawancin Ƴammatan Da Za’aima Auren Duk Ƙawayensu Ne, Duk Da Dai A Shekaru Gaskiya Zasu Girmesu Da Kusan Shekara Bibbiyu Ko Ɗai-Ɗai.

Bai Hanasu Ba, Dan Gidan Marayun Nan Nada Matuƙar Muhimmanci A Garesa Dama Family Ɗin Gaba Ɗaya. Yanda Suke Ƙoƙarin Dagewa Akan Tarbiya Da Karatun Yaransu Haka Suke Dagema Yaran Gidan Marayun Nan Suma. Shiyasa Suma Yaran Suna Tsananin Ƙaunar Wannan Family, Su Suke Ɗauka Danginsu Da Komai A Rayuwa.

“Wai Wannan Akwatin Da Kika Lodama Kaya Duk Na Miye Nu’aymah?”. Umm Data Shigo Ɗakin Nu’aymah Ta Faɗa Tanabin Nu’aymahr Daketa Shirin Kaya Da Kallo.

Ɗagowa Tai Ta Kalli Umm Cike Da Ɗoki, “Umm Yo Na Bikine Mana, Sati Guda Zamuyi A Can”.  “To Lallai, Ashema Kune Iyayen Bikin Kenan?”. Dariya Nu’aymah Tayi Dajin Zancen Umm, Umm Kam Daga Haka Bata Sake Cewa Komaiba Ta Ajiye Mata Magungunan Ta Tana Faɗin, “Gasu Nan, Saura Kije Kita Wasa Da Shansu Nu’aymah, Dan ALLAH Ki Kula Da Kanki, Duk Abinda Kikasan Zai Zame Miki Matsala Ki Kujesa, Ku Kuma Riƙe Mutuncin Kanku, Na Kira Baba Habi A Sashenta Zaku Zauna Kafin Hajjo Ta Iso Gobe Idan ALLAH Ya Kaimu, Saura Naji Wani Abu Mara Ƙyau Na Shegen Tsiwanki, ALLAH Saina Ɓata Miki Rai”.

“Umm Insha ALLAH Bazakiji Komaiba Ma”. “ALLAH Yasa”. Umm Ta Faɗa Tana Juyawa Ta Fice Daga Ɗakin..

You Can Also Download Sani Ahmad Soyayya Hausa Music Mp3 Download.

Bayan Sallar Azhar Su Nu’aymah Sukai Sallama Da Kowa Suka Wuce, Yah Abubakar Ne Ya Kaisu. Da Yake Shima Irinsu Ne Ɗan Taraliya Saida Ya Kaisu Sukai Shopping Sannan Ya Wuce Dasu Gidan Marayun.

Ƙaton Gaske Ne, Sannan An Ƙawatashi Ta Ko Ina Babu Makusa. Akwai Makaranta Da Asibiti Da Duk Ma Abinda Masu Rayuwa Da Iyayensu Suke Samu. Makarantarsu Ta Fara Tun Daga Noziri Har Zuwa Sakandire. Ana Koyar Da Boko Da Arabic, Idan Kaji Yanda Yaran Ke Larabci Da Turanci Sai Kasha Mamaki Da Al’ajabi. Rayuwarsu Suke Cike Da Farin Ciki Da Jin Daɗi Wadda Ko Wasu Masu Iyayenma Basa Samu. Gasu Da Tarbiyya Abin Birgewa.

Ɓata Lokacine Zama Bayyana Muku Yanda Gidan Marayun Nan Ya Ginu Da Tsari Mai Ƙyau, Kusa A Ranku Kawai Ya Haɗu. Dan Sosai Su Baba Malam Ke Samu Taimakon Manyan Mutane Dama Masu Mulki Game Da Riƙe Gidan. Ga Kuma Suma Kansu Masu Nemane Basu Zauna Jiran Na Sadakaba. Kaso Mafi Yawa Na Ɗunbin Dukiyarsu Yana Tafiyane Wajen Tattalin Rayuwar Marayun Nan Da Kulawa Da Su. Shiyyasa Alhmdllh Da Wahala Ace Sun Nema Abu Sun Rasa. Sai Dai Ace Yau Da Gobe Sai ALLAH, Komai Arziƙinka Dama Wani Abun Sai Ya Gagareka.

A Yanda Su Nu’aymah Suka Sami Tarba Zai Tabbatar Maka Da Sanannune A Gidan, Kuma Ba Wannanne Farkon Zuwansu Su Kwanaba. Dan Rigima Aka Shigayi Musamman Ga Sa’anninsu, Kowa Na Faɗin Sashinsu Su Nu’ayma Zasu Sauka. Bayan Ansha Taƙaddama Dai Kowa Ya Haƙura Zasu Zauna A Sashen Da Amare Suke, Wato Sashen Baba Habi Da Umm Ta Faɗama Nu’aymah Tun A Gida.

A Yau Kowa Ya Kalli Nu’aymah Yasan Tana Cikin Farin Ciki Sosai, Haƙoranta Sun Kasa Rufuwa. Tsiyarsu Sukaita Tsulawa Uwa Ba Kwaɓa Uba Babu Tsanani, Dan Suna Son Suga Sunzo Gidan Nan, Shiyyasa Wani Lokacin Baba Malam Da Kansa Yake Cewa Suzo Suyi Weekend Ɗinsu Anan, Dama Anan Duk Yaran Gidansu Ke Karatunsu Tun Daga Noziri Har Zuwa Sakandire, Shiyyasa Sukeda Shaƙuwa Sosai Da Yaran Gidan Marayun Fiye Da Zaton Mai Tunani.

Recommended Post: Macijine Shi Complete Hausa Novel Download Now.

Washe Gari Nanah Tace Suma Gasunan Zuwa Ita Dasu Suhailat, Hakan Yasa Bayan Sallar La’asar Ana Tsaka Da Musu Ƙunshi Dan Ranar Itace Suka Saka Ranar Ƙunshin, Nanah Ta Kira Wayar Yusrah Ta Sanar Musu Gasu A Bakin Titi Suzo Su Shiga Dasu Dan Baza’a Barsu Su Shigaba Kai Tsaye.

Nu’aymah Da Yusrah Da Biyu Cikin Ƴammatan Gidan Suka Fita Shigowa Da Su Nanah Dansu Ƙunshinsu Harya Bushe Sun Wanke, Nu’aymah Ce Kawai Bata Wanke Nata Ba Amma Ya Bushe. Da Ƴar Tafiya Tsakanin Gate Da Gidajen Yaran, Amma Haka Suka Taka A Ƙasa Suna Hira Har Suka Iso. Suna A Gab Da Fitane Suka Haɗu Da Yaran Gidan Maza Da Bazasu Gaza Shekaru Sha Biyu Ba Kusan Su Bakwai Wai Wajen Ball Suka Tilla Ƙwallon Waje Ta Katanga Shine Zasu Zagaya Ɗakkowa. Security Ɗaya Ne Tare Dasu Zai Rakasu. A Tare Suka Fita Dasu Nu’aymah Da Zasuje Tarbar Su Nanah.

Gidan Marayun Yana Akan Babban Titine, Shiyyasa Sam Ba’a Barin Yaran Fitowa Ko Ina Su Kaɗai Koda Hakan Ta Kama Sai Da Security.

Also Download Yar Dandi Ce Hausa Novel Complete Document Free Download.

Dariya Nu’aymah Tai Ganin Su Nanah Acan Ɗayan Tsallaken Basu Tsallakoba, Tasan Nanah Matsoraciyace Akan Tsallaka Titi Dama, Shiyyasa Yanzuma Abun Ya Bata Dariya Data Tuna. Su Yusrah Ma Dariya Suka Sanya Famhimtar Dariyar Nu’aymah Da Sukayi. Bayan Sun Kalla Ɓangare Biyu Na Titin Babu Mota Suka Sa Kai Zasu Tsallaka. Da Sauri Security Ɗin Daya Rako Yaran Nan Yasa Hannu Ya Fisgo Nu’aymah Dake Ƙarshen Tafiya Saboda Tahowar Wasu Motoci Guda Uku A Jere Cikin Masifaffen Gudu.

Ta Juya Zataima Security Ɗin Masifar Taɓatan Da Yayi Dukda Tasan Hakan Na Halinsu Bane Sukaji Razananniyar Ƙarar Ɗaya Daga Cikin Yaran Wanda Motar Farko Ta Kwashesa Yana Ƙoƙarin Ɗakko Gyalen Nu’aymah Daya Zame Ya Faɗi Lokacin Da Security Ɗin Nan Ke Ƙoƙarin Maidota Baya.

“Ƙuuuuuwww!!!” Motocin Suka Bada Sautin Taka Birki A Tare, Yayinda Mai Napep Dake Bayansu Ya Bugi Motar Ƙarshe Shima.

A Tare Su Nu’aymah Suka Fasa Ƙara Da Rumtse Idanu Kunnuwansu A Toshe Da Hannayensu, Sai Da Sukaji Tsitt Sannan Suka Bubbuɗe Ido Dan Son Ganin Yaya Akayi.

“Innalillahi…. Suka Shiga Ambata Kusan A Tare Saboda Hango Yaron A Kwance Ƙasa Cikin Jini. Sunma Manta A Titi Suke, Suka Tafi Da Gudu Kansa Suka Rufu Masa. Sunkai Mintuna Uku Akan Yaron Nan Suna Kuka Da Jujjuyashi Amma Ko Mutum Ɗaya Bai Fito Daga Motocin Nan Uku Ba Balle Kai Tunanin Sunsan Ma Abinda Suka Aikata. Cikin Tsananin Fushi Da Zafin Zuciyar Gado Nu’aymah Ta Rarumi Wani Dutse Dake A Gefen Titin Ta Nufi Motar Tsakkiya Dake A Saitinta, Wadda Kuma Tafi Kowacce Haɗuwa Da Ƙyau Ta Buga Dutsen Jikin Glass Ɗin.

Ko Gezau Glass Ɗin Baiyiba, Dan Haka Ta Koma Na Gaba Wanda Tasan Insha ALLAH Zata Dace Ta Sake Bugawa Da Iya Ƙarfinta. Aiko A Take Ya Shiga Tsatstsagewa. Ta Sake Ɗagawa Zata Buga Aka Riƙe Mata Hannu. Fisge Hannun Nata Tai Ƙoƙarin Yi Ta Kasa, Dan Haka Ta Juyo Bakinta Cike Da Tsiwa.

Scroll to Top