Hausa News

Rahama Sadau: Bahaushiyar Da Tafi Samun Cigaba A Africa

Cigaban Da Hausawa Suka Samu

Nasarorin Da Jarumar Kannywood Ta Samu Rahama Sadau

Bayan Bincike Mai Zurfi Da Shafin Hausa Cinema Tayi, Daga Karshe Dai Ta Gano Cewa Rahama Sadau Tana Daya Cikin Shahararrun Yan Fim Guda 10 Wadanda  Suka Samu Cigaba A Fadin Duniya. Duk Da Cewa Jarumar A Yanzu Take Samun Nata Daukaka, Rahama Sadau Ta Kasance  Tafi Samun Cigaba A Nigeria, Musamman Ma A Bangaren Shirya Fina-Finai.

Wannan Cigaba Da Rahama Sadau Take Samu, Cigaba Ne Da Duk Wani Bahaushe Yakamata Ace Yana Farin Ciki Dashi. Ba Iya Hausawa Ba Hatta Mutanen Arewa Da Fadin Nigeria Baki Daya. Kamar Yadda Muke Alfahari Da Sauran Yan Fim Da Suke Fita Waje Zuwa Hollywood Daga Nan Africa. Haka Zalika Muna Alfahari Da Wasu Yan Kwallo Da Suke Fita Daga Nan Africa Zuwa Manyan Kungoyoyin Nahiyar Turai.

Rahama Sadau Ta Fara Harkar Fim A Shekaru 9 Da Suka Gabata. Kuma Shigowarta Harkar Fim Kai Tsaye Ta Fara Acting Da Manyan Jaruman Kannywood Irinsu Ali Nuhu, Yakubu Muhammad, Allah Ya Jikan Rai Rabilu Musa Ibro Da Sauransu. Ba Tare Da Jimawa Ba Jarumar Ta Zama Producer A Harkar Shirya Fina-Finai, Inda Ta Fara Shirya Fina-Finan Kanta.

Bayan Wadannan Nasarrori Da Rahama Sadau Take Samu A Harkar Fim. Rahama Sadau Ta Kara Samun Daukaka Bayan Ta Aka Fara Gayyatarta Zuwa Shirya Fina-Finai  A Masana’antar Nollywood. Nollywood Daya Daga Cikin Manyan Masana’antu Dake Shirya Fina-Finai A Fadin Africa. Ta Halarci Manyan Fina-Finai Wadanda Akeyi Da Turanci, Kuma Manyan Fina-Finai Ne Da Suka Daukaka Irinsu, Sons OF Caliphate, If I am A President Da Sauransu.

Jarumar Wato Rahama Sadau, Tasha Suka Sossai Musamman Ma A Wajen Wasu Yan Uwa Hausawa Wajen Ganin Ta Cika Burinta Na Shahara. Inda Wasu Ke Binta Da Sharri A Dukkan Lamuranta Batare Da Bincikar Nasu Ko Duba Akan Yanayin Rayuwa Ba (Dama Rayuwa Kafin Kayi Nasara Daya Daga Cikin Abubuwan Da Zaka Shiryawa Shine Zagi, Suka Da Gulma Daga Wajen Mutane). Jarumar Tayi Amfani Da Wadannan Kuma Tana Amfani Da Zagin Wajen Cimma Burinta.

Rahama Sadau Ta Sake Samun Daukaka Bayan Da Aka Gayyaceta Ta Halarci Wani Shiri Na Bollywood. Kamar Yadda Kuka Sani Bollywood Babu Kamarta A Duniya Wajen Shirya Fina-Finai. Jarumar Ta Bayyana Yadda Tun Asali Take Mafarkin Shiga Fina-Finan India Wato Bollywood. Daga Karshe Dai Tun Batayi Nisa Ba Mafarkinta Na Kan Zama Gaskiya. Domin A Halin Yanzu Jarumar Tana Sake Samun Gayyata Zuwa Shirya Fina-Finai A Bollywood.

Kar Kuce Bamu Fada Muku Ba, Zaku Iya Samun Zafafan Shirye-Shiryenmu A Shafin Hausa Cinema. Litattafan Hausa (Hausa Novels), Wakokin Hausa (Hausa Music), Fina-Finan Hausa (Hausa Videos), Hotunan Hausawa (Hausa Photos), Labaran Hausa (Hausa News), Dama Abubuwan Ilimantarwa Ga Mutanenmu Hausawa (Hausa Education).

Akwai Wani Abu Daka Karu Da Wannan Rahoto Na Jaruma Rahama Sadau?

5/5 - 1 Votes

Hausa Cinema

Hausa Cinema The Best Website In Africa Delivering The Latest News, Entertainment, Educational Articles And Many More About The Hausa People.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Related Articles