Hausa Articles

Matan Kannywood Masu Kudi 2023 – [Read Now]

Bayan Dogon Bincike Da Mukayi Tare Da Duniyar Kannywood, Mun Kawo Muku Jerin Sunayen Matan Kannywood Masu Kudi. Wadannan Sune Matan Kannywood Da Sukafi Kudi A Shekarar 2023 A Masana’antar Kannywood.

Manyan Matan Kannywood Da Suka Fi Kudi 2023

A Wannan Makalar Mun Kawo Muku Jerin Sunayen Matan Kannywood Guda 10 Da Yakamata Ku San Su. Sune Matan Kannywood Guda Goma Da Suka Yi Shahara Kuma Suke Tashe A Masana’antar Ta Kannywood.

Kamar Yadda Kowace Masana’anta Take Da Nata Gwanaye, Haka Itama Masana’antar Kannywood Take Da Su. Akwai Gwanaye Mata, Akwai Kuma Maza Gwanaye Da Sukayi Fice Sukayi Shahara A Fadin Duniya Baki Daya.

Mata A Kannywood

Matan Kannywood Masu Kudi

Kamar Yadda Ku Ka Sani, Kannywood Tana Daya Daga Cikin Manyan Masana’antun Shirya Fina-Finai A Africa. Ba Iya Africa Kadai Ba, Kannywood Tana Daga Cikin Masana’antun Da Labarin Su Ya Karade Duniya Gabadaya.

Mata A Kannywood Suna Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Tafiyar Da Harkokinta. Musamman Ma Jarumai Irinsu Rahama Sada, Hadiza Gabon, Nafisat Abdullahi, Da Sauransu. Sun Kawo Cigaba Da Nasara A Bangarori Daban-Daban Na Cigaban Masana’antar Kannywood Ciki Da Waje. Musamman Rahama Sadau, Rahama Sadau Bahaushiyar Da Tafi Samun Cigaba A Africa. Lallai Kuwa Wannan Babban Cigaba Ne Ga Matan Kanywood Gabadaya.

Don Haka Mata Suna Taka Muhimmiyar Rawa Sossai A Duniyar Kannywood, Ta Bangarori Daban-Daban.

Sunayen Matan Kannywood Masu Kudi Guda Goma

Wadannan Sune Matan Kannywood Masu Kudi Da Muka Kawo Muku A Wannan Shafi. Mun Kawo Muku Wadannan Sunaye Ne Bisa La’akari Da Yanwan Fina-Finansu, Shaharar Su A Duniya, Kasuwancin Su Na Bayan Fage (Entrepreneurship, Ambassador, Modelling)

  1. Nafisat Abdullahi
  2. Rahama Sadau
  3. Hadiza Gabon
  4. Hafsat Idris
  5. Maryam Booth
  6. Fati Washa
  7. Teema Makamashi
  8. Aisha Aliyu Tsamiya
  9. Maryam Yahaya
  10. Momme Gombe

Nafisat Abdullahi

Jarumar Da Tafi Kudi A Kannywood Itace Nafisat Abdullahi. Jarumar Tana Daga Cikin Matan Kannywood Da Suka Dade Suna Wasa A Masana’antar Tare Da Bada Gudumawa A Cikinsa. Duk Da Cewa Jarumar Bata Da Farar Fata, Amma Tana Daukan Hankalin Mutane Da Burge Masu Kallonta Akoda Yaushe. Saboda Yadda Ta Iya Salon Shiri Yasa Ta Bayyana A Fina-Finai Da Yawa.

Jarumar A Halin Yanzu Jarumar Tana Zaune A Kasan London, Inda Take Gudanar Da Rayuwar Ta A Can. Haka Zalika Jarumar Wato Nafisat Abdullahi Tana Da Manyan Masana’antu Da Take Samun Kudin Shiga Dasu; Naf Costmetics, Naf Closet, Da Kuma Larous Cafe.

A Kiyasin Da Mukayi (Hausa Cinema), Mun Gano Cewa Jaruma Nafisat Abdullahi Tana Da Kimanin Naira Miliyan 45. Wannan Dalili Ne Yasa Tazo Na Farko A Jerin Mata Masu Kudin Kannywood.

Rahama Sadau

Rahama Sadau Wiki Hausa Cinema

Jaruma Rahama Sadau Itace Jarumar Ta Biyu Cikin Jerin Matan Kannywood Masu Kudi. Ta Samu Wannan Yabo Ne Bisa La’akari Da Harkokinta, Fina-Finanta, Dama Rawar Da Take Takawa A Masana’antar Ta Kannywood. Ba Iya Wannan Ba, Jarumar Tana Daga Cikin Matan Hausawa Da Sukafi Samun Cigaba A Fadin Duniya Baki Daya.

Bugu Da Kari, Rahama Sadau, Ba Iya Kan Kannywood Take Fita Ba, Tana Fita A Fina-Finan Bollywood Dama Nollywood Baki Daya. Da Wannan Rahama Sadau Tana Da Kwatankwacin Naira Miliyan 37.

Hadiza Gabon

Hadiza Gabon

Hadiza Aliyu Gabon, Jarumar Da Ake Kiranta Da Baya Goya Marayu. Tana Daga Cikin Manyan Jaruman Kannywood Da Sukayi Suna Kuma Suke Daukaka A Fadin Duniya. Kamar Yadda Kowa Ya Sani Jarumar Tana Daga Cikin Jarumai Mata Da Suka Fito A Fina-Finai Da Yawa Na Hausa. Kuma Tana Bada Abinda Ake So A Duk Wani Matsayi Da Aka Ajiye Ta A Cikin Fim.

Ba Wannan Ba, Jaruma Hadiza Gabon Itace Mamallakin HAG Foundation Dake Taimakawa Yara Dama Marasa Karfi. Bugu Da Kari, Ta Kirkiri Shafin Gabon’s Talk Show Dake Gayyato Jarumai (Mawaka, Marubuta, Yan Fim) Da Kuma Tattaunawa Dasu Akan Harkokinsu.

A Yadda Shafin Hausa Cinema Ta Gano, Mun Gano Cewa Jaruma Hadiza Gabon Tana Da Kimanin Naira Miliyan 29.

Hafsat Idris

A Lamba Ta Hudu Mun Iske Jaruma Hafsat Ahmad Idris, Wacce Aka Fi Sani Da Hafsat Idris Barauniya. Hafsat Idris Tana Daga Cikin Manyan Kannywood Da Suke Tashe Kuma Suke Kasuwanci. Jarumar Ta Kannywood, Ta Fito A Finai-Finai Dayawa, Wadanda A Cikinsu Tayi Suna Sossai.

A Wannan Matakin, Jaruma Hafsat Idris Tana Da Kimannin Naira Miliyan 23. Wanda Hakanne Yasa Tazo Mataki Na Hudu A Jerin Sunayen Mata Masu Kudin Kannywood Na 2023.

Maryam Booth

Idan Mukayi Duba Izuwa Mataki Na Biyar, Zamuga Cewa Maryam Booth Tana Daga Cikin Matan Kannywood Masu Kudi Guda Goma. A Cikin Jerin Sunayen Itace Tazo Lamba Ta Biyar Bayan Hafsat Idris Da Hadiza Gabon.

Maryam Booth Tana Daga Cikin Manyan Jaruman Kannywood Da Sukayi Suna A Fadin Duniya. Domin Ta Tashi Ta Samu Sana’ar Kannywood A Gidansu, Wajen Mahaifiyar Ta (Marigayiyawa Hajiya Zainab Booth, Allah Ya Jikan Rai). Tana Wasa (Acting) Yadda Ya Dace A Duk Wani Wani Matakin Da Aka Bata Na Fim. Bugu Da Kari, Jarumar Ba Iyaka Kannywood Ta Tsaya Ba, Tana Yin Fina-Finai A Nollywood.

A Wannan Mataki Jarumar Tana Da Kwatankwacin Naira Miliyan 17. Wanda Hakanne Yasa Ta Zamo Na Biyar A Cikin Mata Masu Kudin Kannywood Na 2023.

Fati Washa

Cikin Lissafin Mu Mun Iske Fati Washa A Lamba Shida, Wanda Hakan Na Numa Mana Cewa Tana Daga Matan Kannywood Masu Kudi. Jarumar Tayi Suna Sossai, Sa’annan Ta Shahara Musamman Ma Wajen Yin Fina-Finan Soyayya. Yawanci Tafi Bayyana A Film Da Adam A Zango Fiye Da Kowane Jarumi Na Kannywood.

Ba Wannan Ba, Jaruma Fati Washa Tana Da Kimanin Naira Miliyan 15, Wanda Hakanne Yasa Ta Zama Na Shida A Cikin Lissafin Mata Masu Kudin Kannywood.

Teema Makamashi

Aisha Aliyu Tsamiya

Momme Gombe

Maryam Yahaya

In Conclusion – Matan Kannywood Masu Kudi

Daga Karshe Wadannan Sune Jerin Sunayen Matan Kannywood Masu Kudi Na 2023. Mun Kawo Muku Wadannan Sunaye Ne Bisa La’akari Da Harkokinsu Na Yau Da Kullum, Fina-Finasu, Da Kuma Sana’o’insu. Don Haka Duk Inda Muka Yi Kuskure Muna Maraba Da Gyara Ta Comment Section. Zamu Ci Gaba Da Kawo Bayanai Game Da Jaruman Na Kannywood Domin Sanin Asalin Sahihin Bayanai. Karanta: Hanyoyi 5 Da Zaka Gane An Taba Saduwa Da Mace.

5/5 - 1 Votes

Hausa Cinema

Hausa Cinema Language Is The Best Website In Africa Delivering The Latest News, Entertainment, Educational Articles And Many More About The Hausa People. Download Hausa Novels, Hausa Music, Hausa Videos, Mod Apks And Many More.

Leave a Reply

Related Articles