Hausa Articles

100+ Maganin Karfin Maza (Free Man Power) 2023

Kana bukatar sanin ingantaccen maganin karfin maza na shafawa, ko sha, ko kuma na asibiti? Watakila kana fama da matsalar rashin kuzari ko kankacewar gaba wanda hakan baya barinka ka gamsar da mace. A wannan makala munyi dogon bincike inda mukayi bayani akan matsalolin dake kawowa, yadda ake maganin karfin mazakuta, da yadda ake kiyayewa. Idan ka bada lokaci ka karanta Insha Allahu zaka samu waraka…

Abubuwan Dake Kashe Karfin Namiji (Mazakuta)

Abu na farko da zamu fara dubawa shine, menene dalilin da yasa namiji yake rasa karfin sa, ko kuma baya iya gamsar da iyalinsa. Kowanne zai iya rasawa ta hanya daban, saboda haka matakin farko shine ka fara duba menene ya janyo maka matsalar kafinnnan ka san matakin da zaka dauka na magani da kiyayewa. Akwai matsaloli da yawa, wadanda suka hada da:

 • Ciwon Sanyi
 • Hawan Jini (Hypertension)
 • Ciwon Sugar
 • Basir
 • Shaye-Shaye (Taba, Giya Ko Miyagun Kwayoyi)
 • Kallon Blue Fim (Fina-finan Batsa)
 • Cin Abinci Mara Inganci
 • Hatsari (Ciwo)
 • Gado
 • Rashin Motsa Jiki
 • Yawan Shiga Damuwa Da Tunani

Wadannan sune abubuwan dake haifar da rashin karfin mazakuta, ba sai mun tsaya dogon bayani ba saboda a bayyane suke. Sai ka fara dubawa a cikin wadannan abubuwa menene ya janyo maka naka matsalar? Matakin farko kenan na maganin kowane matsala. Ba wai kaje kana shan magani haka kawai ba tare da sanin ka’ida ko dokokin likita ba.

Karanta: Maganin Girman Nono Budurwa Da Matan Aure Cikin Sati Daya.

Maganin Karfin Mazakuta

Akwai magangunna da yawa na kara karfin mazakuta, kamar yadda muka fada a farkon rubutun cewa; Akwai maganin karfin maza na gargajiya da na bature. Wanda duk suna aikine daban-daban, ko su kara wa mazakutar ka karfi da kuma tsawo, sa’annan kaima karan kanka kaji kana da karfi sossai.

Abu na farko, neman maganin karfin maza, kamar yadda mukayi bayani a baya yana da kyau ka fara sanin menene ya janyo maka. Sanin matsalar itace hanyar magancewa ta farko, idan misali rashin motsa jikine, kaga yakamata ka sa himma wajen ganin kana motsa jiki. Idan kuma shaye-shaye ne, shima yana da kyau ka janye shaye-shayen.

Idan kuwa kallon fina-finan batsa ne, ko wasu abubuwan da muka lissafo, yana da kyau a kiyayesu. Amma gado, idan gado ne to gaskiya ba lallai bane koda ka sha magani yayi maka aiki. Saboda akwai wadanda haka Allah ya halicce su. Wadansu koda gado ne, suna iya samun waraka, amma wadansu kuma gaskiya haka halittar take ba sauyi. Idan aka matsa kuma sai a haifar da wata matsala ta daban. Allah yasa mu dace.

 Maganin Karfin Maza Da Namijin Goro

Namijin goro na taimakawa maza sosai wajen kara musu karfin mazakuta. Mutane da yawa sun san shi suna aiki dashi, amma ba kowa bane ya sani. Kuma ana amfani dashine a gargajiyance. Shi namijin goro baya bukatar wani hadi, kawai abinda ake bukata shine, mutum ya samu yaci namijin goron koda biyu zuwa uku ne a rana. Bincike ya nuna cewa namijin goro yana da tasiri sosai ga sassan namiji dake alaka da jima’i.

Kankana

Ko ka san cewa kankana yana karawa namijin karfin mazakuta? Idan baka sani ba to ka jarraba, kankana shima nau’in abincine da yake karawa namiji power wajen jima’i. Kamar yadda masana suka binciko, sun bayyana cewa kankana dai-dai yake da maganin karfin maza na asibiti mai suna ‘Sildenafil’. Don haka idan kana fama da wannan matsalar, ka kulla abota da shan kankana, in sha Allahu za’a dace.

Dabino

Ana yin maganin karfin maza da dabino. Saboda shi dabino dama yana dauke da sinadarai masu yawan gaske a cikinsa. Daga cikinsu akwai sinadaran dake taimakawa namiji wajen kara masa karfin mazantakarsa. Yadda ake hadawa shine; idan ka samo dabino kamar 10 zuwa 15, sai ka zuba su a cikin kwano, sa’annan ka zuba ruwa a ciki yadda zaka iya sha wadatacce. Zaka barshi yayi awanni uku, kafinnnan ka sha. Ana hadawa da safe da kuma yamma.

Sa’annan ka’idarsa shine, ba’a so ka sha lokacin da ka gama cin abinci. Anfi so kaci lokacin da kakejin yunwa, kafin kaci abinci da mintuna 10 zuwa ashirin.

Maganin Karfin Maza Da Hadin Kwai (Egg)

Kwai yana taimakawa namiji wajen kara maza karfi wajen saduwa da iyalinsa. Shima an tabbatar yana maganin karfin maza idan aka hada shi da garin habbatus sauda. Yadda ake hadawa shine; za’a samu kwan kaza guda 2, da babban cokalin garin habbatus sauda guda daya. Za’a fasa kwan a danyensa, a cakudasu waje guda, sa’annan a soya sama-sama ba tare da ya kone ba. Gabadaya mutum zai cinye, In sha Allahu idan anayi na wani lokaci za’a dace.

Kanumfari

Kanumfari na taka muhimmin rawa wajen inganta rayuwar aure, harma da lafiyar jikin dan adam. Shi kanumfari na daga cikin maganin karfin maza na shafawa wanda idan aka samu man kanumfari, wanda bashida hadi to an gama komai. Yadda ake amfani dashi shine; kafin jima’I da kamar mintuna 30, namiji zai shafa man kanunfarin a azzakarinsa.

Reodo

Wannan magani ne na musamman da ake sayar dashi ga mazajen da suka rasa kuzarins, ko kuma basa iya gamsar da iyalinsu. Magani ne da aka jaraba kuma aka tabbatar da ingancinsa, ba iya karfin maza yake karawa ba, maganin yana karawa namiji karfin da zai jima yana saduwa da matarsa.

Wadannan kadan kenan daga cikin magungunan karfin namiji wanda suke karawa namiji karfi wato man power. Akwai na kwayoyi da hadi wadanda amfani dasu zai kara taimakawa sosai. Ana iya samunsu a asibitoci, kuma ana shan su, ta taimakon likitoci.

Gargadi: Yana da kyau ka guji shan maganin da baka san yaya asalinsa yake ba, maganin da aka hada kuma ake amfani dashi ba tare da sanin ingancinsa ba. Allah yasa mu dace.

5/5 - 4 Votes

Hausa Cinema

Hausa Cinema The Best Website In Africa Delivering The Latest News, Entertainment, Educational Articles And Many More About The Hausa People.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Related Articles