Hausa Articles

Maganin Girman Nono Budurwa Da Matan Aure Cikin Sati Daya 2023

Kina budurwa amma kuma kina fuskantar matsalar girman nono. Watakila nonon naki baya girma ko kuwa nonon basu tsaya ba. Haka zalika da yawa daga cikin matan aure bayan sun haihu suna so kara girman nono. Hakane ma yasa suke shiga da fita wajen neman ingantaccen maganin girman nono, wanda zai sa cikowar nono.

Akwai magangunan kara girman nono da kuma cikowar nonuwa daban-daban, kama daga shafawa, hadiya, da sauransu. Sai dai mafi inganci shine maganin girman nono na shafawa da ake amfani dashi a sati daya. Cikin sati daya zaki kara girman nono da hips (duwawu) da yardar Allah, sai ki karanta wannan a nitse.

Yadda Ake Kara Girman Nono

Maganin Girman Nono Budurwa Da Matan Aure Cikin Sati Daya

Akwai hanyoyi dayawa da ake kara girman nono wadanda yakamata ace kowane mace ta san wannan. Budurwa da matan aure, ko bazawara zasu iya amfani da wannan hanyoyi wajen kara girman nono cikin sati daya In Sha Allah.

Motsa Jiki

Daga cikin manyan abubuwan dake karawa mace girman nono a wannan zamani shine motsa jiki. Duk macen da take motsa jikin ta to tabbas zaka sameta kullum da manyan nonuwa sun cika kirjinta kuma sunyi kyau. Ta yadda kowane namiji idan ya gani zai ji kanshi ya motsa.

Matan mu na hausawa da yawa basu damu da motsa jiki ba, musamman ma mazauna cikin gari. Zakaga mace ta kai mace amma babu ruwanta da motsa jiki. Hakama matar aure ko bazawara. Ki sani, shafa magani ko shan wani maganin girman nono na asibiti ba zai taimaka miki ba. Idan kina son kara girman nonuwanki naturally dole sai kin hada da motsa jiki wato excersise a turance.

Bugu da kari, bakowane kalan motsa jiki bane yake kara girman nono akwai nau’in motsa jiki na musamman da suke karawa mace nonuwa. Ga wasu daga cikinsu;

Wall Press (Dafa Bwango)

Shi wannan nau’i na motsa jiki ana yinsa ne a tsaye, inda za’a samu gini mai kyau sai a dafa shi. Kar na cika da bayani ga bidiyon yadda ake motsa jikin ki kalla yana da sauki.

Body Push Up

Wannan nau’i na motsa jiki da ake kiransa da body push up yana da sauki. Kuma yana daga cikin manyan motsa jiki da suke karawa mace girman nonuwa cikin sauki, kuma naturally ba tare da maganin gargajiya ba. Mace zata dafe hannunta a kasa tare da mikewa gabadaya, sai ta ringa amfani da hannun nata tana tashi da sauka, ga yadda yake.

Chest Press

Chest press (Danna kirji) yana daga cikin manyan motsa jiki da suke kara girman nonuwa. Idan kina yin wannan to tabbas zaki ga canji wajen girman nonuwanki cikin kankanin lokaci.

Idan zakiyi chest press ya kasance kin tanadi abu mai nauyi kamar turmi. Ko wani abu wanda zaki iya dagawa a kwance. Amma idan da hali zaki ya sayan dumbbell, shi wannan karfene da ake amfani dashi wajen motsa jiki, ana samunsu a gidajen motsa jiki wato gym.

Zaki samu waje mai kyau ki kwanta da baya kina kallon sama, kamar kan bench ko kan gado. Sai ki daga wannan abu mai nauyi kina saukar dashi a hankali. Kalli misalin yadda ake motsa jikin;

Cobra Pose

Shima nau’i ne na motsa jiki da mace zata ringa yi domin kara girman nonuwanta cikin sauki. Shi wannan motsa jiki na Cobra Pose ana yinsa ne kamar yadda zaki kalla a wannan bidiyo.

Karanta: Abubuwa 10 Dake Tayarwa Mata Sha’awa.

Maganin Girman Nono Na Shafawa

Bayan motsa jiki kuma mace zata iya amfani da magani na shafawa ko sha domin kara girman nonuwanta. Amma yawanci wannan hanya ba fiya tasiri ba. Koda mace tayi amfani dasu baya wuce kwana daya biyu sai nononta su koma gidan jiya ko su lalace.

Akwai maganguna da yawa na maganin girman nono da ake shafawa domin kara girman nono. Ga hanyar da zaki kara girman nonuwanki cikin sauki;

Abubuwan Da Zaki Tanada;

  1. Ganyen Tatarida (Gwanwani 1)
  2. Gujjiya (Gwangwani 2)
  3. Wake (Gwangwani 1)
  4. Alkama (Gwangwani 2)

Bayan kin hada wadannan abubuwa sai ki nika su a inji suyi laushi. Sa’annan ki samu nono kindirmo wanda bai yi tsami ba kina saka garin maganin cokali biyu kina sha. In sha Allahu cikin sati zaki ga sauyi da yardar Allah.

4.6/5 - 19 Votes

Hausa Cinema

Hausa Cinema The Best Website In Africa Delivering The Latest News, Entertainment, Educational Articles And Many More About The Hausa People.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Related Articles