Hausa Novels

Magajin Wilbafos Hausa Novel – Download Free Document Now

Magajin Wilbafos Na Daya Daga Cikin Litatafan Hausa Na Yaki Da Yakamata Ka Karanta. Wannan Littafin Magajin Wilbafos Littafi Na Biyu Ne, Zaka Iya Bincika Kashi Na Daya A Shafin Mu Na Hausa Cinema. Ana Samun Littafin Magajin Wilbafos Novel A Okadabook Wanda Fasihin Marubucinnan Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Ya Rubuta. Anan Zaka Iya Karanta Littafin Ko Kuma Ka Saukar Da Free PDF Document Ka Karanta.

TitleMagajin Wilbafos
AuthorDr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Published DateJune 2016
Published ByHausa Cinema Novels
Total Pages263
Total Words54,105
File Size1.09MB
RatingNot Available
Download Magajin Wilbafos Part 2 PDF

Littafin Magajin Wilbafos

Armad Najin Sunan Babara Hannunsa Yakai Kan Takobinsa, “Ina Babaran?” Amma Duk Su Biyun Babu Wadda Ta Iya Amsa Masa. Karkarwa Kawai Suke. Ana Cikin Wannan Hali Armad Yaji Muryar Babara Kamar Yadda Yasan Ta A Shekarun Baya Da Suka Gabata.

Armad Wilbafos! Barka Da Dawowa, Ina Fata Ka Dawo Min Da Abinda Mukai Alƙawari?” Armad Yai Duba Izuwa Ƙofar Tantin Nan Inda Wani Wada Mai Yawan Farin Gashi Ya Fito. Wannan Wada Ba Wani Bane Illa Sarkin Duba Abul-Babara. Mutumin Da Shekarun Da Suka Gabata Yayi Wa Armad Alƙawari Zai Samarwa Mahaifiyarsa Lafiya Zarar Ya Nemo Tarifil-Fakta.

Sai Dai Kuma Gashi Armad Ya Dawo Bayan Tsahon Lokaci Amma Ba Tare Da Tarifl-Fakta Ba. Koda Yake Duk Da Cewa Babara Bai Yiwa Mahaifiyarsa Tasa Magani Ba Yadda Armad Yaga Babaran Ya Ɗakko Ma’aikatan Lafiya Suna Kula Da Ita Yasa Ya Ɗan Rage Zargi Dake Cikin Ransa. Amma Hakan Bai Hana Armad Zare Takobi Ba Tare Da Tunkarar Babara.

“Zan Baka Dama Ɗaya Tak Kayi Wa Mahaifiya Ta Magani Ko Kuma Takobi Ta Tasha Jininka.” Babara Yai Murmushi Gami Da Girgiza Kai, “Idan Ka Kashe Ni Waye Zaiyi Maka Bayanin Ciwon Dake Damun Mahaifiyarka Kuma Waye Zai Gaya Maka Labarin Ƴar Uwarka Hidaya. Samu Waje Ka Zauna.” Babara Ya Tafa Hannayensa Inda Wasu Kujeru Suka Bayyana, Magajin Wilbafos Hausa Novel.

Babara Ya Zauna A Ɗaya Amma Armad Ya Tsaya Da Takobinsa A Hannu, Domin Ba Komai Babara Ya Gaya Masa Zai Yadda Ba. “Hidaya Kuma?” Armad Ya Haɗe Gira Cikin Mamaki. Shi Dai Dama Yana Ji A Jikinsa Yayar Tasa Na Nan Da Rai. Amma Da Kakansa Da Babarsa Sunƙi Gaya Masa Wani Abu Akanta. Babara Yayi Kyaran Murya Tare Da Fara Jawabi, “Sama Da Shekaru Dubu Da Suka Wuce Ƙungiyar Ƴan-Duba Ta Duniya Ta Daɗe Tana Rikici Da Jinsi Daban-Daban Na Aljanu, Magajin Wilbafos Hausa Novel.

Asalin Rigimar Aljanu Ne Suka Fara Zargin Ƴan Duba Da Keta Musu Haddi Su Kuma Ƴan Duba Suna Zargin Aljanu Dayi Musu Ƙarya. Rigima Ce Data Fara Ƙarama Amma Daga Baya Ta Zama Hamshaƙiya Wadda Ta Halaka Dubban Ƴan- Duba Da Aljanu. Shekaru Sittin Da Huɗu Da Suka Wuce Hidaya Ta Shiga Tsakani Ta Raba Wannan Rigima, Lamarinda Ya Kawo Zaman Lafiyar Da Ake Dashi A Yanzu.

A Sakamakon Haka A Matsayina Na Shugaban Yan Duba Nayi Alƙawari Zan Saka Mata Da Sak Irin Alkhairin Datai Mana Komai Daren Daɗewa. “A Wancan Lokaci Bazan Manta Ba Hidaya Ta Bugi Ƙirji Tana Cewa Bata Buƙatar Komai Daga Waje Na. Amma Sai Gashi Ko Shekara Ɗari Ba’ai Ba Yaƙi Ya Haɗa Da Ita A Tsakanin Aljanu Masu Biyayya Ga Ururu Da Kuma Sauran Sarakunan Aljanu, Magajin Wilbafos Hausa Novel.

Littafin Magajin Wilbafos Hausa Novel

Yaƙi Mai Tsananin Gaske Wanda Babu Yadda Zatai Ta Iya Barin Filin Daga Duk Da Kuwa Mahifiyarta Bata Da Lafiya, Kuma Ƙaninta Yana Buƙatar Taimako. “Ciwon Dake Damun Mahaifiyarka Ana Kiransa Da Cutar Izza. Ciwo Ne Wanda Ake Samu A Yayinda Ma’aboci Izza Yake Ƙoƙarin Ƙara Yawan Izzarsa. Duk Wata Hanya Da Ake Amfani Da Ita Wajen Ƙara Izza Zata Iya Jawo Wannan Cuta Amma Bansan Taƙamaimai Wacce Hanya Ce Ta Jawo Wa Mahaifiyarka Wannan Cuta Ba.

Read: Best War Novels Of All The Time.

Kai Sani Cewa Wannan Ciwo Ciwon Ajali Ne. Duk Wanda Ya Sameshi Ƙarshensa Kabari. Kuma Wannan Ciwo Shi Ne Yasa Zaka Ga Sama Da Kaso Casa’in Da Tara Na Mutane Sun Gwammace Su Haƙura Da Izzarsu A Iya Shekarunta, Domin Ko Yaya Aka Samu Matsala A Lokacin Da Mutun Yake Ƙoƙarin Ƙara Yawan Izzarsa To Lallai Ƙarshensa Kabari. Abu Guda Ɗaya Tak Dake Maganin Wannan Ciwo Shi Ne Idan Mutun Ya Karɓi Shekarun Izza Daga Wani. Wato A Misali Ka Ɗiba Daga Cikin Shekarunka Na Izza Ka Ƙarawa Wannan Mutumi, Magajin Wilbafos Hausa Novel.

Karanta: Jarababben Namiji Complete Hausa Novel.

“Kai Sani Cewa Kamar Yadda Ake Haifar Ƙabilar Ururu Da Baiwar Baƙaƙen Idanuwa Haka Ake Haifar Iyalan Wilbafos Da Baiwa Ta Musamman. Wannan Baiwa Ita Kaɗai Ce Abarda Zata Iya Maganin Wannan Ciwo.”
“Wannan Baiwa Kuwa Ba Wata Bace Illa Fasahar Dake Cikin Idanunku. Idanu Ruwan Ƙasa Masu Ratsin Toka. Duk Wanda Yake Da Irin Wannan Idanu Yana Da Wannna Baiwa, Kuma Iyalan Wilbafos Su Kaɗai Keda Wannan Idanu, Magajin Wilbafos Hausa Novel.

Karanta: Azima Da Aziza Macizai Ne Hausa Novel Complete.

“Da Wannan Idanu Zaku Iya Bayarda Izza, Za Kuma Ku Iya Karɓa Tamkar Yadda Ake Saka Kaya A Cire. Wannan Ita Ce Baiwar Ka A Matsayinka Na Ɗan Ƙabilar Wilbafos. Kayi Sani Cewa Turaka Da Nayi Ka Nemo Tarifil-Fakta Bashi Da Alaƙa Da Ciwon Mahaifiyarka. Sai Dai Kawai Na Jefi Tsuntsu Biyu Ne Da Tsakuwa Ɗaya. Kaga Tafiyar Ka Keda Wuya Na Ɗakko Waɗannan Ma’aikata Da Kake Gani Na Sasu Su Ringa Kula Da Mahaifiyarka, Ni Kuma Na Tafi Duniyar Aljanu Domin Sanarda Hidaya Abinda Ke Faruwa.

Nasan Duk Duniya Babu Wanda Zai Iya Yi Mata Magani Sai Ita, Domin Kuwa Kai Baka Ma San Komai Ba Acikin Alamuran Izza A Lokacin. To Amma Bansan Halin Da Zan Tarar Da Hidaya Ba, Wataƙila Ma Bata Raye, Saboda Haka Kaima Na Tura Ka Duniya Domin Kaga Yadda Duniya Take, Kayi Ƙarfi Ka Zama Ma’aboci Izza Tayadda Koda Ban Samu Hidaya Ba Kaima Zaka Iya Taimakon Mahaifiyarka. Amma Nasan Baza Ka Iya Nemo Tarifil-Fakta Ba, Magajin Wilbafos Hausa Novel.

Karanta: Yadda Ake Duba BVN Number A MTN, Airtel, GLO.

Kada Ka Manta Hatta Ururu Sun Kasa Nemo Shi. “Sai Da Na Ɗauki Shekaru Biyu Ina Bilayin Yadda Zan Shiga Filin Yaƙin Da Hidaya Ke Ciki Amma Ban Samu Damar Shiga Ba, Domin Kuwa Naji Aljanu Suna Cewa Hatta Mutuwa Tayi Hijira Daga Wannan Fili. Wasu Aljanun Ma Suna Cewa Shi Yasa Yaƙin Yaƙi Ƙarewa Saboda Babu Mutuwar Da Zata Ci Gaba Da Ɗaukar Rai A Wajen. Kai Daga Ƙarshe Dakyar Na Samu Wani Tsohon Aljani Ya Shigar Dani Filin Yaƙin. Amma Muna Shiga Wannan Aljani Ya Rasa Ransa.

Nima Allah Ne Ya Taimake Ni Na Tsira Dakyar Amma Duk Da Haka Saida Nayi Asarar Shekarun Izza Ɗari Biyar Kafin Na Fito Daga Wannan Fagen-Daga. Tun Daga Nan Nasan Cewa Ganin Hidaya Ba Abu Ne Mai Yiwuwa Ba. Kuma Lallai Babu Wanda Ƴa Rage Dazai Ceto Mahaifiyarka Sai Dai Kai. Saboda Haka Na Dawo Na Aiko Maka Da Saƙon Daka Gani Na Wata Bakwai. “Naso Na Gaya Maka Haƙiƙanin Mai Ake Ciki Acikin Saƙon Amma Na Ƙara Baka Lokaci Naga Ko Zaka Iya Farkar Da Jininka Na Wilbafos, Magajin Wilbafos Hausa Novel.

Karanta: Hanyoyi 5 Da Zaka Gane An Taba Saduwa Da Mace.

Kai Sani Cewa Nayi Farin Ciki Kwanakin Baya Da Naga Hasken Farin-Wata Ya Canja Kala. Domin Nasan Cewa Lokaci Yayi Dazan Biya Hidaya Bashin Da Take Bin Ƙungiyar Ƴan-Duba Ta Duniya. “Amma Fa Kai Sani Wani Hanzari Ba Gudu Ba….” Armad Ya Katse Babara Ta Hanyar Yin Ƙaraji Ya Zare Takobinsa Yana Huci, “Wai Kana Nufin Duk Wahalar Dana Sha Ta Nemo Tarifil-Fakta A Banza!!” Armad Bai San Lokacin Daya Kaiwa Babara Wani Sara Ba Cikin Ɓacin Rai. Babara Yai Tsalle Gefe Guda Yana Murmushi, “To Yanzu Da Ban Tura Kaba Zaka Farkar Da Jininka? Kasha Wahala, Amma Yanzu Zaka Ga Amfaninta, Magajin Wilbafos Hausa Novel.

Karanta: Hanyoyin Sada Zumunta Na Zamani.

Sannan Kuma Indai Hanyar Izza Zaka Bi Wannan Baka Ga Komai Ba A Fannin Wahala. Yanzu Duniya Tasan Dakai, Idanun Kowa Zai Dawo Kanka. Idan Bakai Da Wuri Ba Ka Farka Lallai Yanzu Ne Zaka San Wahala.” Babara Yana Magana Amma Armad Kawai Huci Yake Yana Kallonsa A Fusace. Bayan Ɗan Lokaci Babara Yaci Gaba Da Jawabi, “Sai Ansha Wuya Ake Samu Izza. Kuma Lallai Indai Kana So Ka Zama Ma’aboci Izza Yanzu Ka Fara.

Karanta: Download Masarautarmu Ce Hausa Novel.

Saboda Yayarka Hidaya Nayi Alƙawari Zan Koya Maka Yadda Zakai Amfani Da Idanuwanka Wanda Ita Kaɗai Ce Hanyar Da Zaka Zama Ma’aboci Izza Na Gaskiya Ka Iya Tsayawa A Gaban Ururu Sannan Kuma Ka Ceto Mahaifiyarka Ta Hanyar Bata Shekarun Izza. Amma Kai Sani Cewa Hatta Yayarka Hidaya Wadda Hatta A Duniyar Aljanu Ana Labarin Ƙarfin Kwakwalwarta Da Gane Abubuwanta Saida Tayi Shekaru Uku Tana Koyar Yadda Zatai Amfani Da Idanuwanta.

Read: 10 Best Personal Financial Novels Of All The Time.

Lallai Zaka Iya Yin Shekaru Goma Kana Koya Wanda Kuma Mahaifiyarka Baza Takai Wannan Lokaci Ba. “Naji Daɗin Ganinka Da Wannan Zoben Domin Zai Taimaka Mana Wajen Ajiye Mahaiyarka Aciki.” Babara Yai Nuni Da Zoben Da Nostaljiya Ta Bawa Armad, Magajin Wilbafos Hausa Novel.

5/5 - 8 Votes

Hausa Cinema

Hausa Cinema The Best Website In Africa Delivering The Latest News, Entertainment, Educational Articles And Many More About The Hausa People.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Related Articles