Hausa Articles

Sabbin Kalaman Soyayya Na Mata 2022

Kalli Sabbin Kalaman Soyayya Na Mata

Kalaman Soyayya Na Mata 2022

A Wannan Shafi Mun Kawo Kalaman Soyayya Na Mata Wadanda Zaka Turawa Budurwarka. Wadannan Kalaman So Masu Ratsa Zuciyar Mace Zasu Burgeka Masoyiyarka Idan Kana Rubuta Mata Cikin Sakwanni Messages Ko Kuma Cikin Wasika. Zaka Tura Mata Ta Facebook, WhatsApp Ko Kuma Ka Rubuta Mata A Takarda Kai Tsaye.

A Lokuta Dayawa Rashin Iya Tsara Kalaman Soyayya Kan Iya Jefa Masoya Cikin Matsalahar Ta Kai Ga Sun Rabu. Iya Tsara Kalaman Soyayya Masu Dadi Zasu Baka Damar Ka Mallake Zuciyar Mace Cikin Sauki. Haka Zalika Idan Kana Yinsu A Inda Suka Dace Zaka Ringa Shan Mamaki. Rashin Iya Tsara Kalaman Soyayya Ka Iya Jefa Ka Cikin Matsala Har Ka Iya Rasa Budurwarka, Domin Da Zaran Tana Samun Zafafan Kalamai Daga Wani To Shikenan Zata Iya Mantawa Da Kai Cikin Kankanin Lokaci. Sai Dai Kawai Taji Kana Gundurarta, Taji Ta Tsaneka Ba Tare Da Wani Dalili Ba.

Bisa Ga Wadannan Dalilan Ne Yasa Shafin Hausa Cinema Muka Shirya Muku Zafafan Kalaman Soyayya Na Maza 2022. Wadannan Kalaman Soyayya Zaka Iya Amfani Dasu A Kowane Lokaci, Ingantattu Ne Sa’annan Kuma Kalaman Soyayyane Na Musulunci Da Basu Da Laifi Ko Kuskure A Cikinsu.

Zafafan Kalaman Soyayya Na Mata

Sabbin Kalaman Soyayya Na Mata 2022

Na Yarda Dake Dari Bisa Dari, Saboda Haka Inaso Akoda Yaushe Ki Zamto Min Bango Abin Jingina, Ta Yadda Duk Lokacin Da Naji Zan Fadi Na Dafe Ki. Na Tabbata Da Soyayyarki Bazan Taba Faduwa Kasa Ba.

A Kowace Nasara Da Namiji Yayi To Tabbas Idan Ka Duba Zaka Kalli Mace A Kusa Dashi. Zuciyata, Gangar Jikina Harma Da Kwakwalwata Suna Fadamin Cewa Kece Nasarata. Ina Fata Zaki Cigaba Da Kasancewa Tare Dani Har Izuwa Lokacin Da Nasara Zata Riskemu A Tare?

Har Izuwa Yanzu Na Gagara Amsa Wannan Tambayar; Meyasa Nake Sonki? Dalili Kuwa Shine Na Kan Kwashe Sa’a (Awa) Ina Ta Tunanin Amsar Da Zan Baiwa Mutane. A Kullum Amsar Da Nake Karkarewa Dashi Shine Babu.

Hakika Soyayya Tana Da Dadi, A Baya Na Karyata Hakan, Kece Kika Tabbatar Min Da Hakan Kuma A Yanzu Na Gaskata. Tabbas Soyayya Tana Da Dadi, Dadin Da Bazai Taba Misaltuwa Ba.

Kinsan Idan Na Ganki Yaya Nakeji A Raina? A Duk Lokacin Da Na Hangoki Abu Na Farko Da Nake Tsintsar Kaina Kaina Ciki Shine Shauki, Daga Bisani Na Kanji Komai Ya Tsaya, Hatta Iska Nakan Daina Jinsa, Zuciyatace Kawai Take Bugawa.

Soyayyarki Ta Koyar Min Da Abubuwa Da Yawa; Babban Abinda Soyayyarki Ta Koya Min Shine Sanin Amfanin Rayuwa. Shiyasa Nake Kara Daraja Da Kaina A Duk Lokacin Da Na Tuna Cewa Ina Dake.

Tabbas So Lalura Ne, Kuma Duk Wanda Ya Fadi Cikinta Baya Jin Kira. Nayi Nisa A Sonki Wadda A Yanzu Bani Da Wata Manufa Data Wuce Na Kyautata Miki, Na Tabbata Idan Muna Tare Zaki Samu Kyakkyawar Kulawa.

Allah Ya Halicci Rana Ne Ba Don Komai Ba Sai Domin Muyi Aiki A Cikinta. Rana Tana Taimaka Mana Wajen Yin Aikace-Aikace Da Zamu Kula Da Kawunanmu Har Lokacin Mutuwarmu. Kinsan Menene? Kece Wannan Rana A Cikin Duniyata, A Duk Lokacin Da Babu Ke Rayuwata Zata Koma Mara Amfani.

Kowane Mai Numfashi Yana Bukatar Abinci, Ruwa Da Kuma Iska Domin Yayi Rayuwa. Amma A Cikinsu Kafi Bukatar Iska Akan Ruwa, Sa’annan Kafi Bukatar Ruwa Akan Abinci Akai-Akai. Haka Kike A Gareni, Ina Bukatarki Fiye Da Iskar Da Nake Shaka.

A Tarihin Masoyan Da Suka Gabata Sunyi Sadaukarwa, Cikin Sadaukarwar Harda Rayuwarsu Da Kuma Kadarorinsu Na Rayuwarsu Gabadaya. Akoda Yaushe Nima A Shirye Nake Domin Sadaukar Da Kaina Da Kuma Kadarorina Domin Ki.

Na Yarda Dake Masoyiyata, Na Kuma Amince Dake, Hakanne Yasa Akoda Yaushe Soyayyarki Take Kara Karuwa Cikin Zuciyata. Ina Fata Bazaki Ci Amanata Ba Har Abada?

A Kullum Ina Kara Godewa Allah Ubangiji Da Na Sameki, Matukar Muna Tare Dake Babu Wata Matsalata Da Zata Addabi Rayuwata. Domin Da Zaran Na Shiga Matsala, Idan Na Tunaki Na Kanji Sukuni A Raina, Da Zaran Kuma Na Ganki Na Kanji Dukkan Matsalata Ta Yaye.

Kinsan Meyasa Wasu Mutanen Suke Fadawa Shaye-Shaye? Saboda Rashin Samun Ingantatticiyar Soyayya, Shiyasa A Kullum Nake Kara Godiya Ga Allah Da Ya Bani Ke A Matsayin Masoyiya, Kuma Abokiyar Rayuwa Nan Gaba.

Download: Umar M Shareef Farin Jini Album 2022 Video, Songs, And Lyrics.

Kammalawa

Wadannan Sune Kalaman Soyayya Na Mata 2022 Da Muka Kawo Muku A Wannan Shafin Na Hausa Cinema. Akwai Kalaman Soyayya Na Maza Da Muka Kawo Da Zaku Iya Karantawa A Wannan Shafin Da Muke Kawowa Akoda Yaushe Domin Jin Dadin Masoya. Idan Wadannan Kalaman Sun Burgeka, Kayi Mana Comment Da Alamar Godiya. Kuci Gaba Da Kasancewa Tare Da Shafinmu Domin Samun Sabbin Kalaman Soyayya Na Maza Da Mata.

4.7/5 - 78 Votes

Hausa Cinema

Hausa Cinema Language Is The Best Website In Africa Delivering The Latest News, Entertainment, Educational Articles And Many More About The Hausa People. Download Hausa Novels, Hausa Music, Hausa Videos, Mod Apks And Many More.

Leave a Reply

Related Articles