Hausa Articles

Kalaman Soyayya Masu Dadi 2023

Wadannan Sabbin Kalaman Soyayya Masu Dadi Ne Muka Kawo Saboda Masoya Tare Da Labaran So Masu Dadi. Wasu Daga Cikin Kalaman Mun Samosu Ne Daga Wakokin 2023 Wadanda Mawakan Soyayya Sukayi Musamman Ma Hamisu Breaker Da Umar M Shareef.

Ka Sauka Kasa Domin Ka Karanta Kalaman Soyayya Masu Dadi Da Ratsa Zuciyar Masoya Cikin Kankanin Lokaci. Let’s Get Started…

Na Kurbi Zumar Kaunar Da Mutane Ke Bayaninsa Tun Zuwan Kakanmu Annabi Adam. Kuma Alhamdulillah Na Dace Tunda Allah Ya Bani Ke A Matsayin Abokiyar Rayuwa, Nagode Allah. Zanci Gaba Da Kasancewa Tare Dake Har Izuwa Karshen Rayuwata.

Tunanina Daya Ne Shine Soyayyarki, Dana Manta Sai Na Tuna Babu Kamarki A Rayuwata, Ki Kalli Irin Kyawun Fuskarki Da Ubangiji Ya Baki, Sa’annan Ki Hada Da Kyawawan Dabi’unki.

Karanta 👉 Zafafan Kalaman Soyayya Na Maza Da Mata 2023.

Ki Rike Min Alkawarin Cewa Bazaki Taba Barina Ba Komai Tsananin Wuya Da Dai Masoyiya Ta. Nima Na Rike Rike Miki Alkawarin Cewa Duk Tsananin Rayuwa Ina Tare Dake.

Ke Kika Farfado Da Gangan Jikina, Tunanina Da Kuma Ruhina Daga Wani Yanayi. A Baya Ni Mai Jinya Ne, Amma Yanzu Sanadinki Na Warke. Idan Dake A Tare Dani Babu Cuta Da Zata Same Ni. Ina Sonki.

Gashi Na Dauko Soyayya Ta Na Mika Miki, Ki Karba Hannu Bibbiyu Ki Adana Min Sirrina. Kece Kadai Zaki Iya Bude Min Kuma Ki Rufe Min Ita. Amma Ina Da Tabbacin Ke Mai Amana Ce.

Idan Da Raina, Da Kuma Lafiyata, To Bazan Taba Daina Sonki Ba. Saboda Haka Idan Kika Ga Na Daina Sonki To Bani Da Raine Ko Lafiya.

Komai Nesanta Da Mukayi Da Juna, A Kullum Sai Na Rika Ji Kamar Muna Tare Dake A Kusa. Tasirin Da Kikayi A Cikin Zuciyata Baya Sanya Naji Kinyi Nisa Dani Koda Kuwa Baki Kusa Dani Din.

Karki Barni Sahibata, Duk Wani Abinda Nakeyi Domin Na Faranta Miki Rai Ne Nakeyi. Dan Adam Ne Ni Ina Kuskure, Don Haka Idan Na Bata Miki Rai Ki Yafe Min.

Zuciyata Ce Ta Zabeki A Matsayin Abokiyar Rayuwa, Domin Tana Da Tabbacin Kece Zaki Gina Ta, Ki Raya Ta, Sannan Kuma Ki Ringa Sanyata Cikin Farin Ciki Akoda Yaushe.

Karanta: Sakon Soyayya SMS Saurayi Da Budurwa 2023.

Kace Kike Da Ikon Sauya Zuciyata, Kece Kika Da Ikon Yankewa Zuciyata Hukunci, Inma Farin Ciki Inma Na Bakin Ciki, Domin Linzamin Zuciyata A Hannunki Take. Roko Na A Gareki Shine Kada Ki Yanke Mata Hukuncin Da Zatayi Dana Sani.

Tunda Na Baki Raina Da Kuma Zuciyata, Kome Kike So Idan Kika Bukata Zanyi Miki. Ina Matukar Kaunar Ki, Ina Sonki.

Zamu Cigaba Da Inganta Muku Wannan Shafi Ta Hanyar Kawo Muku Zafafan Kalaman Soyayya Masu Dadi Akoda Yaushe.

5/5 - 1 Votes

Hausa Cinema

Hausa Cinema Language Is The Best Website In Africa Delivering The Latest News, Entertainment, Educational Articles And Many More About The Hausa People. Download Hausa Novels, Hausa Music, Hausa Videos, Mod Apks And Many More.

Leave a Reply

Related Articles