Hirar Soyayya – Yadda Ake Hira Tsakanin Saurayi Da Budurwa

Wannan wani darasi ne na musamman da muka kawo domin masoya da suke son sanin sirri akan yadda ake hirar soyayya mai burgewa, ban dariya da kuma ban sha’awa. Ta hanyar amfani da wadannan sirruka zaka iya burge budurwarka ko kuma saurayinki ta hanyar sanya shi nishadi.

Da farko masoya da yawa suna shiga cikin matsala har ta kai ga ana zargin juna sakamakon rashin samun Hira mai dadi a lokacin soyayya. Hakan zai sa masoyan su fara waswasi anya wannan yana kaunata kuwa? saboda kalaman nasu ko yadda suke hirar bata dauki hanya ba.

Wasu masoya suna hira batare da salo, ko burgewa ba, dolene a matsayinka na masoyi ko masoyiya, idan har ta tabbata kuna son juna; to ku nuna shi a bayyane. Domin daya daga cikin manyan alamomin soyayyar gaskiya itace kyawawan kalamai. Amma sai dai matsalarmu a yau wasu masoya basu iya wannan ba.

Hirar Masoya

Ga irin hirar da duk wasu masoya yakamata suyi tare da tambayoyin da zasu ringa jefawa cikin hirar tasu.

 • Kin taba yin soyayya?
 • Ki bani labari akan soyayyar ki ta farko
 • Idan zaki samu iko da kudi a duniyar nan, fada min menene zaki yi a rayuwarki.
 • Menene abubuwa biyar da idan babu su rayuwarki ba zatayi dadi ba?
 • Kin taba yiwa wani laifi daga baya kika yi da na sani har kika nemi gafarar sa?
 • Idan nace ki fada min, a wace manufa kika dauki rayuwarki, sa’annan kuma yaya kika dauke ta?
 • Kin taba yin kuka tunda kika mallaki hankalin ki?
 • Da menene kike ji kika fi burge kanki?
 • Da menene nake burge ki?
 • Kin taba batawa da wata kawar ki ko yar uwa?
 • Menene yake sanya ki cikin damuwa?
 • Idan aka baki zabi ki dawo da mutune biyu da suka bar duniya, su waye zaki dawo dasu?
 • Zaki iya fada min abinda kike jin dadinsa a tattare daku cikin rayuwar ki?
 • Wane abune a rayuwarki da kike kokawa dashi kuma baki jin dadinsa?

Farkon Soyayya

Asmi Wakili - Hirar Soyayya

Idan soyayyar ku bata yi nisa ba zaka iya amfani da wadannan kalaman wajen sanin da wa kake soyayya, Sa’annan zai taima maka wajen inganta hirar soyayyar ka cikin sauki.

 • Yaya akeyi kika gane cewa kina sona?
 • Yaya kike gani soyayyar mu dake zata kasance bayan munyi aure?
 • Ina kike ganin alakar mu dake zata tafi?
 • Menene aure yake nufi a rayuwarki?
 • Wane fim na soyayya kika gani da yafi burge ki?
 • Kin yarda da soyayya a farkon rayuwar ki?
 • Bayan bamu tare dake, wane abune babba da kike kewata dashi?
 • Menene idan kika tuna dangane dani kike jin dadi a ranki?

Hirar Ma’aurata

Wannan hira ce ta soyayya da ake yinta tsakanin ma’aurata. A wannan hirar tana dauke da kalamai masu nauyi. An yisu ne kawai saboda ma’aurata da komai zai iya shiga tsakaninsu, domin akwai kalaman motsa sha’awa (hirar batsa).

 • Wane bangare ne a jikina yafi burge ki?
 • Wani bangare na a jikina kike son kara sani sossai?
 • Wane lokaci kika fi jin dadin alakar mu (Saduwa)? Na dare ko ta safiya?
 • Menene abu mafi burgewa a kwanciyar mu?
 • Wani style na kwanciya kika fi so, kika fi jin dadinsa?
 • Wane wajene kika fi so mu kasance domin samun ingantacciyar alaka kowane lokaci?
 • Wane abune yafi tada miki hankali kiji kina bukatar alaka kwanciya dani?
 • Sau nawa kikafi so ki kwanta tare dani a kowace rana?
 • Idan kina kawo ruwa, kina iya tuna inda kike?
 • Zaki iya kwatanta min yadda kike ji idan kina kawo ruwa?
 • Wane bangare na jikin ki kika fi so a ringa shafa miki?

Karanta 👉 Gidan Uncle Hausa Novel Complete Chapters.

Tambayoyin Soyayya

A lokacin soyayya, ko kuma ince a rayuwar soyayya, akwai abubuwan da yakamata kowane masoyi ya sani. Zaka iya sanin da wa kake soyayya ta hanyar yin hirar soyayya mai fasali da ma’ana. Ba wai hirar da ake na wasu kaga maganganun shirme da wofi da karya. Wadannan tambayoyi yana da kyau kayi su a lokacin hira.

 • Kinason ki samu yara? (Idan eh, Yara nawa kike da burin haifa mana?)
 • Wane irin uwa kike son zama wajen yayanki da zaki haifa?
 • Yaya kike ji game da addinin ki?
 • Wani halinki kika fi jin dadinsa?
 • Wane halinki kika fi tsana da bashi da kyau a gareki?
 • Yaya kike son rayuwarki ta kasance nan da shekaru goma masu zuwa?
 • Wacece babbar kawarki? Sa’annan kuma menene yasa kike zabe ta a matsayin ta musamman?
 • Me kikeso a lokacin da kike fusace?
 • Kina da kishi? (Idan eh, Yaya kishin ki yake?)
 • Da gaske kishi yana da kyau a soyayya?
 • Wadanne abubuwa ne kikafi so a lokacin yaranta? (Idan ta baka amsa; har yanzu kina sonsu?)
 • A cikin tarihin rayuwarki wane abune yafi sanya ki farin ciki wane abune kuma yafi sanya ki bakin ciki?
 • Wane abune mafi girma, mafi muhimmanci da kike dubawa a tattare da wanda kike so?
 • Wane irin kyauta kika fi so?
 • Idan aka baki damar zuwa ko ina a fadin duniya kiyi rayuwa, ina zaki zaba?
 • Wane abune kika fi mutane su ringa tambayar ki akai?
 • Wane abune baki so a ringa tambayar ki akan sa?

Daga karshe anan zamu tsaya da wannan rubutu na Hirar kalaman soyayya. Zamuci gaba da kawo sabbi bayan wasu lokuta, ku kasance da shafin Hausa Cinema a shafinmu Na Facebook, Instagram, Twitter, YouTube, Da sauransu.

👉 Labarin Soyayya – Read Complete Hausa Love Story Now

👉 Sabbin Kalaman Soyayya Na Mata 2023

👉 Sani Ahmad Kalaman Soyayya Official Music

👉 Sakon Soyayya SMS Saurayi Da Budurwa 2023 – Read Now

👉 Zafafan Kalaman Soyayya 2023 – Read Now For Free

2 thoughts on “Hirar Soyayya – Yadda Ake Hira Tsakanin Saurayi Da Budurwa”

 1. Pingback: Yadda Ake Hira - Tsakanin Saurayi Da Budurwa - ArewaClassic

 2. Pingback: Zafafan Kalaman Soyayya Masu Dadi 2023

Leave a Comment

Scroll to Top