Hausa Novels

Heedayah Hausa Novel Complete Download – Khaleesat Haiyder

Download Heedayah Hausa Novel By Khaleesay Haiyder

Heedayah Hausa Novel

Heedayah is a fictional Hausa novel written in the Hausa language to entertain, motivate, and educate Hausa novel readers online.  And also, the novel was written by the professional Hausa novel writer Hauwa Bello Jidderh popularly known as Khaleesat Haiyder. Furthermore, the Heedayah Hausa novel is currently among the trending and popular Hausa novels. The number of readers (fans) is increasing every day.

As a result, Hausa Cinema Novels have provided a free Heedayah Hausa Novel by Khaleesat Haiyder document for you in PDF format. Thus, you can download the complete document of Heedayah complete in PDF format for free now. So, after downloading the novel, you can read it offline for free without data usage.

Name Heedayah By Khaleesat Hayder
Title Heedayah Hausa Novel
Author Khaleesat Haiyder
Group Hausa Cinema Writers
Genre Love
Language Hausa Language
Document Type PDF
Size 1.00MB
Words 115,071
Pages 167
Published Date September 2022
Keyword Heedaya, Hidaya Hausa Novel


Download

Download Heedayah Hausa Novel Complete

Heedayah Hausa novel story is written based on love and relationship. Furthermore, the novel is among the popular and trending Hausa novels added to our list. And also, the novel book was written in the Hausa language to entertain, motivate, educate, and inspire Hausa novel readers around the world (online). Everywhere you are, you can access this page and download it for free.

Hausa Cinema will help you get and download Heedayah Hausa Novel document in PDF format for free now.

Recommend: Kyawuna Jarabtata Hausa Novel Complete Download NowSaran Boye Hausa Novel Complete Document Download NowJihadi Hausa Novel Complete Download Now – Hausa Cinema.

How To Download Heedayah Hausa Novel

To download Heedayah Hausa’s novel complete document in PDF format, you need to follow these steps:

  1. Firstly, install a PDF reader on your device.
  2. Secondly, go to Hausa Cinema and search ‘Heedayah Hausa Novel’.
  3. Thirdly, click on the first result given by the results.
  4. Finally, proceed to the download page and hit on the download button.

Heedayah

Mumy Tace “Toh Ki Tafi Ki Hada Shayin, Kayan Shayin Na Can Kitchen, Bredi Kuma Na Parlona Su Rabi’ah Sun Bar Sa A Can” Cikin Rawan Jiki Karime Tace “Toh Ngdd Hajiya, Nagode” Mumy Ta Kuma Kai Idonta Kan Eye Drops Din Sannan Ta Fita Karime Ta Bi Bayanta Da Sauri Cike Da Jin Dadi, Main Parlor Mumy Ta Xauna Tana Girgixa Kafa, Karime Kuma Ta Wuce Bangarenta Dauko Bread.

Mumy Ta Bi Ta Da Kallo Har Ta Shiga Ciki, Dai Dai Nan Kuma Aka Bude Kofar Parlon Mumy Ta Juya Don Ganin Wanda Xai Shigo, Kaka Ce Ta Shigo Parlon Tana Sakale Da Wani Karamin Jaka Me Kama Da Handbag, Mai Gadi Na Biye Da Ita A Baya Rike Da Wani Tikeken Akwati, Mumy Ta Bude Baki Ta Mike Da Sauri Tace “Lafiya Kaka? Me Ya Faru??” Kaka Bata Ko Saurareta Ba Ta Nufi Wani Spare Room Dake Nan Cikin Parlon Tana Cewa “Ina Fa Lafiya? Meye Kuma Baxai Faru Ba? Sai Kace Dai Umaru Kadai Na Haifa A Duniya, Ga Dai Gidan Amadu Me Dakuna Ta Ko Ina….”

Har Ta Bude Kofar Sai Kuma Ta Dawo Tace “Wllh Maryam Wani Kwai Suka Soya Min Yau Xar Karni, To Ga Dai Albasa An Cika Amma Ni Dai Naji Yana Karni Na Bala’i, Ina Laifin Su D’an Yanyanka Min Yar Tafarnuwa Su Watsa A Ciki, Wnn Ba Alamomin An Gaji Da Kai Bane A Waje? Jiya Sai Bayan Magariba Suka Kawo Min Abincin Dare, Tuwo Da Wani Miya Sun Cika Naman Kasuwa, To Ca Masu Nayi Yunwan Nama Nake??

Abinda Mu Xamaninmu Karfe Biyar Duk Mun Ci Abincin Dare Munyi Wanke Wanke Kowa Ya Manta, Mata Kawai Suna Neman Kashe Ni Kuma Sai In Xauna Kamar Uwata Tace Min Je Ki Kya Gani, A’a Wllh, To Me Gidan Amadu Yake Da Baxan Lallaba In Dawo Ba??”

Mumy Da Ta Ji Kamar Ta Kurma Ihu Cike Da Karfin Hali Tace “Haba Kaka, Haba Kaka, Haba Kaka, Wllh Hakuri Ake A Ko Ina, Ko Ina Mutum Yake Sai Yyi Hakuri, Rayuwar Ma Gaba Daya D’an Hakuri Ne, Ni Ba Gashi An Min Kishiya Ba Nayi Hakuri Muna Xaune Lafiya? Me Yyi Xafi Xaki Tattaro Kayanki Ki Dawo Nan Ai Baxa Su Ji Dadi Ba Kaka, Gaskiya Bari In Dauko Makullin Mota Mu Koma, Baxa Su Ji Dadi Ba Wllh Barin Baffa, Gani Xai Kamar Baki Gode Kokarinsa A Kanki” Kaka Tace “Koh??” Mumy Tace “Wllh Tllh, Ai Ba Xamansu Kike Ba Da Xa Ki Bar Masu Gidan Kaka, Sun Ma Ci Riba Kenan, Bari In Dauko Makullin Mota”

Kaka Tace “Toh, Idan Fita Xa Ki Yi Ga Mai Adaidaita Can Ki Biyasa Dari Biyunsa Kar Ya Mana Ihun 6arayi A Unguwa Yana Can Yana Jira Ban Basa Ko Sisi Na Ba, Dama Kuma Ban Masu Sallama Ba Ta Baya Na Bar Masu Gidansu, Kya Iya Xuwa Ynxu Ki Ce Masu Na Dawo Nan Da Xama, Duk Me Nemana Ina Nan Gidan D’ana Amadu….” Kaka Na Kai Wa Nan Ta Shige Daki…

Mumy Ta Xauna Saman Kujera Tayi Tagumi Tana Furta Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un A Xuciyarta, Mai Gadi Da Ya Ajiye Kayan Kaka A Parlan Har Ya Tafi Ya Dawo Yace “Hajiya D’an Sahu Na Can Yana Jira Fa….” Cikin Bacin Rai Hajiya Tace “Kai Da D’an Sahun Sai Na Ci Kaza Kazanku Idan Baka Fita Idona Ba, Na Hau Adaidaita Ne Da Xa Ka Xo Kace Min D’an Sahu Na Jirana???”

Mai Gadin Ya Juya Ya Bar Bakin Kofar… Shuraim Da Ya Dawo Daga Kai Abba Office Yana Kallon Mai Adaidaitan Da Ya Gyara Parking Don Basa Hanya Ya Sauke Glass Yace “Wa Kake Jira Malam?” Mai Adaidaitan Yace “Wata Tsohuwa Na Kawo Nan Ta Shiga Wai Xa A Kawo Min Kudi To Har Yanxu Dai Ina Ta Jira” Shuraim Yace “Nawa Ne?” Yace “Dari Biyu Ne Kudin” Shuraim Ya Ciro Dubu Daya Ya Mika Masa, D’an Sahun Yace “Amma Bani Da Canji Wllh” Shuraim Yace “To Je Ka” D’an Sahun Ya Dinga Yi Masa Godiya, Shuraim Ya Gyada Masa Kai Kawai Ya Ja Motarsa Xuwa Ciki Don Mai Gadi Ya Bude Masa Gate, Parking Yyi Ya Sauka Ya Rufe Motarsa Ya Wuce Ciki…

Mumy Ya Tadda A Parlor Tayi Tagumi Ga Tashin Hankali Karara A Fuskarta, Ya Isa Kusa Da Ita Ya Xauna A Hankali Yace “Mumy Lafiya” Mumy Tace “Ina Fa Lafiya Aliyu, Don Allah Ka Shiga Ka Lallaba Tsohuwar Nan Ka Mayar Da Ita Gida, Kalli Uban Akwatin Da Ta Kawo Wai Ta Dawo Nan, Ta Dawo Wajen Wa? Ta Dawo Tayi Mana Me?

Don Allah Ka Shiga Ka Lallaba Ta Ka Maida Ta Inda Ta Fito….” Shuraim Dake Ta Kallon Mahaifiyar Tasa Yace “Mumy Amma Ai Ba Laifi Bane Don Ta Xo Nan, Kuma Ai….” A Mugun Fusace Mumy Tace “Rufe Min Baki Gantalalle Kawai, Dama Ina Kuwa Xaka San Laifi Ne Dawowarta Nan???” Lkci Daya Mumy Tayi Tsit Ganin Kaka Ta Fito Har Ta Cire Hijabin Ta, Kaka Tace “Kin Sallami D’an Sahun Ko Kuwa Kin Barsa Yana Can Yana Min Kallon Macuciya Barauniya??”

Shuraim Ya Mike Yace “Na Sallamesa” Kaka Tace “Atoh, Kai Baka Je Aikin Bane Yau?” Yace “Sai Da Yamma, Ina Kwana?” Tace “Lafiya Lau, Shureen Ni Dai Na Dawo Nan Gaskiya, Matan Umaru Kasheni Suka So Yi Allah Bai Yi Ba, Yau Wani Kwai Suka Ban Da Ya Kusa Kai Ni Lahira, Shayin Kuma Sun Cika Masa Kayan Kamshi Kamar Dai Buzaye… To Ina Dalili Ga Dai Gidan Amadu” Shuraim Dai Bai Ce Komai Ba, Kaka Tace “Ka Shigar Min Da Akwatina Daki Dukiya Ne A Ciki, Jama’ah Ina Deedayah, Ga Bredi Na Taho Mata Da Shi Da Kwai….”

Shuraim Ya Dau Akwatin Nata Ya Shigar Da Shi Ciki, Mumy Dai Karfin Hali Kawai Take Don Kiris Ya Rage Hawaye Ya Xubo Mata, Kaka Tace “Maryam Tambaya Nake Ina Deedayah?” Mumy Ta Dake Tace “Wacece Kuma Deedayah?” Kaka Tace “Sabuwar ‘Yar Amadu Mana….” Mumy Ta Wani Tabe Baki Tace “Ayyo Makauniya Wai?” Kaka Tace “Aa Wannan Kuma Isgilanci Kike Ma Ubangiji Ba Ruwana, Ke Kika Halicceta Da Xaki Kirata Da Makauniya, Meye Kuma Makauniya Idan Ba Isgilanci Ba, Ko Ita Ta Xabar Ma Kanta Makantar? Ni Yanxu Ina Take??”

Duk Wannan Abun Karime Na Tsaye Sai Kallon Kaka Take, Mumy Ta Nuna Mata Karime Tace “Ga Me Kula Da Ita Can” Kaka Ta Kalli Karime Tace “Wacece Kuma Wnn Sai Naso Take, Ta Kula Da Ita Ko Ta Sa Mata Cuta, Bakya Wanka Ne Baiwar Allah?” Karime Ta Kasa Cewa Komai, Shuraim Dai Yyi Murmushi Ya Nufi Dakinsa, Kaka Na Kallon Karime Tace “Wa Ya Daukeki Ki Dinga Kula Da Ita, Amadu Ko Wa? Tunda Ita Uwar Rikon Tata Na Samu Labarin Har Ta Fara Fita Aiki, Amadu Ya Fita Ita Ma Ta Fita….” Karime Ta Girgixa Kai Tace “Aa, Hajiyar Ce Ta Daukeni…”

Kaka Tace “Toh Kuma Sai Kiyi Ta Kazanta Kina Naso, Ba Kya Tashi Da Safe Ki Sa Ruwa Kiyi Wanka Ki Dauko Yar Atamfar Ki Ko Da Kodadde Ne Ki Saka Kiyi Fess Da Ke.. Yanxu Ina Yarinyar Take?” Karime Tace “Tana Can Daki Kwance,”

Kaka Tace “Wannan Xama Da Ke Ai Sai Cuta Ya Kama ‘Yar Mutane…” Daga Haka Kaka Ta Nufi Part Din Mami Tana Cewa “Ita Kuma Mata Daga Tarewa Sai Fara Fita Aiki Kamar Auren Banxa Aka Daura Mata, Ni Ba Ruwana” Zaune Kaka Ta Ga Heedayah Saman Gado Ta Tashi Tana Mitsika Ido, Kaka Ta Washe Baki Tace “Deedayah… Kin Tashi” Heedayah Ta Juya Da Sauri Tana Duban Inda Ta Ji Muryarta Tace “Kaka” Kaka Ta Karaso Tace “Ehh Ni Ce Deedayah, Kin Ga Na Dawo Nan Yanxu, Kwai Suka Bani Duk Karni, Kinji Dalilin Barin Gidansu Da Nayi”

Sakko Mu Je Ga Bredi Da Kwan Na Kawo Maki Kema Ki Ci Ki Ji, Heedayah Ta Sauka Saman Gadon Kaka Ta Kama Hannunta Suka Fita Tana Cewa “Ita Dama Ashe Ba Don Ta Kula Da Ke Aka Aurota Ba, Xata Barma Katuwar Mata Kazama Ta Sa Maki Wani Cutan Amadu Ya Shiga Uku….” Heedayah Tace “Kaka Tafiya Xa Ki Yi Da Ni Can Gidanku?”

Kaka Tace “Wani Gida? Ai Na Dawo Nan Sai Kuma Wani Ikon Allah, Abincin Banxa Fa Suke Bani A Can Gidan Wllh Deedayah….” Mumy Ta Bi Su Da Kallon Gefen Ido, Kaka Ta Tsaya Tana Rike Da Hannun Heedayah Tace “Maryam Ban Fa Karya Ba, Kuma Ni Ba Shayi Xan Sha Ba Gaskiya, Ko Me Aka Samu Ni Dai A Bani In Ci Fisabilillahi” Daga Haka Ta Shige Dakin Da Ta Sauka Tare Da Heedayah, Mumy Ta Mike Ta Wuce Bangarenta Da Sauri Ta Dau Wayarta Ta Shiga Kiran Hajiya Sadiya.

Hajiya Sadiya Na Dagawa Mumy Ta Sakar Mata Kuka Tace “Sadiya Wllh Shirinmu Na Ta Rugujewa, Yau Dai Ga Wnn Tsohuwa Ta Diro Da Katon Akwati, Ynxu Haka Ta Dauke Yarinyar Ta Shige Da Ita Dakin Da Ta Sauka, Wato Bbu Ma Ranan Komawarta Ne Don Sai Kinga Akwatin Da Ta Kawo.

Ni Dai Wllh Sadiya Hakurina Ya Fara Karewa Ji Nake Kamar In Kashe Yarinyar Nan A Gaban Kowa A Daureni Kawai In Huta, Wnn Yarinya Har In Mutu Xan Mance Da Ita Kuwa A Rayuwata, Ta Janyo Min Dariya A Duniya, Duk Fa Dariya Ake Min A Boye Sadiya” Sadiya Tace “Ki Kasheta Kuma A Daure Ki Maryam, Me Aka Yi Kenan?

Ke Ina Gaya Maki Gaggawa Na Shaidan Ne Kin Kasa Fahimta Ko, Meye Na Gaggawa Abinda Dai Ana Tare….” Mumy Tace “Toh Ke Kina Ga Wnn Tsohuwar Da Ta Diro Mana Gida Ynxu Baxata Kawo Mana Wani Cikas Ba?” Hajiya Sadiya Tace “To Ke Meye Ruwanki Da Ita? Wajenta Yarinyar Take Da Xai Dame Ki, Kinga Xa Mu Yi Waya Anjima Nayi Bakuwa”

Daga Haka Ta Katse Wayar, Mumy Ta Xauna Gefen Gado Tayi Tagumi Hawaye Na Sauka Idonta…. Karime Da Sajida Tasa Suka Girka Ma Kaka Shinkafa Da Miya Ko Damuwa Da Ynda Suka Yi Girkin Bata Yi Ba… Kaka Na Kallon Heedayah Dake Kwance Gefenta Tace “Toh Sai Kuma A Siya Maki?” Heedayah Tace “Ehh Mana, Har Kitso Ina Yi Ma Gashin Babyn Nawa….” Kaka Ta Rike Ha6a Tace “A Makancen?” Heedayah Tace “Na’am”

Download PDF Document Book


Download

4.3/5 - 49 Votes

Hausa Cinema

Hausa Cinema The Best Website In Africa Delivering The Latest News, Entertainment, Educational Articles And Many More About The Hausa People.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Related Articles