Doctor Eesha Hausa Novel – Download Complete PDF Now

Download Doctor Eesha Hausa Novel In PDF Format For Free On Hausa Cinema Novels Now.

TitleDoctor Eeesha Hausa Novel
AuthorJ Hajara
GenreLove, Romantic
PublisherHausa Cinema
GroupHausa Novels Cinema
Number Of Pages422 Pages
Number Of Words92,468
File Size1.9MB
PriceFree
Date PublishedNovember 2022
LanguageHausa Language
Adult ContentNo
KeywordsDoctor Eesha Hausa Novel

[button color=”primary” size=”medium” link=”https://hausacinema.com/doctor-eesha-hausa-novel/#Download_Doctor_Eesha_Hausa_Novel” icon=”” target=”false” nofollow=”false”]Download Gidan Dadi Complete Hausa Novel[/button]

Hausa Novel Doctor Eesha

Aliyu Ya Durkusa Da Kai Yace” Ki Yi Hakuri Mami Please”

Ciki tsawa tace” Dalla can rufe min baki, Sam bakason ji laifita , yariya ba tarbiya ko kadan.

Tayaya Ma Allah Zai Bari Mu Hada Zuri’a Da Tababaru Mutani Na? Tir Wlh….. Ta Sausauta Murya Ta Cigaba” Aliyu Ka Kwantar Da Hankali Ka, Allah Sai Ya Nunamusu Ikonsa, Tunda Har Gori Suke Ma. Yanzu Ina Ita Suhaima ?

Yace” tana gida Mami”

” Oho nasan yazun haka tana na tana shaidaci da ta saba ta Tara maza da mata ana ma shaidaici a gida. Wai Aliyu Mai ye ya Sha kan ka ne? Instead of ka gyarata Naga kamar ma tsorata ma kakeji”

Ta Kalli Ammi Tace” Ayya Ammi Mutani Ni Na a Haka Suka Bar Aliyu Kuwa? Dun in Zan Iya Tunawa Tun Ranar Biki Na Essha Ko Wata Ke Da Suna Daya Ke Kira Kamar Zai Zauce Akata , Itama Ya Manta Ta, Ko a Tambayeshi Ma Cewa Yake Bai Santa Ba.

Ama ana yata damu da Essha Essha ana daura aureshi da suhaima mukaji shiru, something is fishy, Kai mutani na Basu da kamshi gaskiya”

Aliyu naji Mami ta Kira suna Essha yaji gabashi ya fadi, ya tsaya shiru deep down yanason tuna Mai suna, ama yakasa tunawa kawai ya basar da zance.

Ammi ta kadai Kai tace” ko ma Mai ye akwai Allah, mu da Allah muka dogara”

Aliyu ya Mike yace” zan wuce, zan bin na duba fawaz a hospital”

Mami ta amsa da toh boy sai anjima, ka ci abinci fa?

Ya amsa da inshallah mamina”

Ya Fito Duk Jikishi a Sanyaye, Yana Isa Gaba Motoci Bodyguards Da Sauri Suka Bude Mishi Kofa Ya Shiga Suka Bar Gida Sai Hospital.Suna Isa Aka Bude Mai Ya Fito, Kai Tsaye Office Din Fawaz Ya Wuce, , Ya Tardashi Ya Na Hada Files, Yayi Sallama.

fawaz ya amsa yace” a buddy Kai ne da Rana haka?

Aliyu bai amsaba ya Mika mishi suka yi musaba ya nemi guri ya zauna ya lumshe Ido, fawaz ya aje files din.

ya karasa gefeshi yace” yadai buddy? Badai haryanzu kasa magana aranka bane?kayi hakuri ka rugume kaddara, ni na zanbaka Dana na har abada, kullum suna ka yake Kira uncle Mai dimple, ya matukar sabawa da kai.

Buddy kowa na alfahari da Kai, yara da manya, a yau Dina zanfi kowa fariciki ace Kai ne ka raini dana. Please Buddy Kar kasa damuwa aranka”

Aliyu ya dago Yana murmushi yace” Thanks buddy, nagode da kulawarka, ni basan damuwa komai a Raina ba dun nasa haka tawa kadara yake, bara ga dan cikina ba kaga kuwa dole na rugumeshi da hannu bibibbiyu na Kara gode Mai da ya bari ni a haka”

Fawaz yace” hmmm, toh naji buddy, yanzu Mai ke damuka?Naga Yana yika ya canza ne”

Yace” hmmm fawaz kasa dai Kai kadai nake gayama sirri na, kasan kuwa bai wuce matsala na da suhaima ba” ya dafa Kai ya cike da takaici yacigaba ” ni Sam suhaima Bata gamsar Dani, yaushe ma ta kullani , sai inhar ta ta bukatar ne ya taso, ni wlh am tired, ni Ina ni a jiki na ba haka abun yake ba, na suhaima ne dai……… .. da sauri fawaz ya sa hannu ya rufe Mai baki

yace” Buddy sirri kune fa ka da ita kayi hakuri, tayaya bara kaji daban baya ka taba Dana musu yariya mutani Essha”

Aliyu yasake ji gabashi ya fadi, ya Bata fuska yace” Wai ku Mai ke damukune? Ku bin ku dameni da zance wata Wai Essha , nace basantaba ku dai na hada ni da ita” ya Mike a fusace zai fita…

Fawaz yayi sauri ya rikoshi yasan buddy nashi da zafi Rai yace” Allah sarki, Koda jima ko ba Dade nasan gaskiya zatayi halinsa, mu dai mu yi iya kokari mu, mu nemanta bamungataba, mu bar ma Allah komai, Addu’a na a kullum shine duk wani mugu da ya asirce zuciya ka Allah ya tona asirisa, munsa komai bayanda mu ka’ iya ne”

Aliyu yakara hada fuska yace” mallam dakata , Wai Mai kake nufi da kalama na naka ne? Kasani a duhu”

Fawaz yayi murmushi yace” nasa baza ka ganeba ai, Kar kada mu ace komai nisa jefa kasa zai dawo da Allah muka dogara ba da mutum ba”

Aliyu yakasa gane idan fawaz ya nufa da waena kalamai sai binshi yake da kallo tuhuma, zai magana fawaz ya dakatar dashi yace” Da Allah buddy karike sallah da adduoin, sune makamin mummuni ga duk wani azzalumi dake so cutar dashi”

Aliyu Yayi Ajiya Zuciya Yace” Toh Naji,zauna Kasa Yanda Zakayi Dani, Maguguna Da Nakesha Na Mara Basamin Aiki Ko Kadan, Ka Rubuta Min Strong Ones, Buddy Nasha Lime Da Liptop Har Na Gaji, Yanzu Haka Jinake Kamar Marana Zata Fashe Dauriya Kawai Nake”

Fawaz Ya Sauke Ajiya Zuciya Cike Da Tausayawa Yace” Kayi Hakuri, Maganishi Kenan Ka Kara Aure, Zai Fi Maka Sauki” – Doctor Eesha Hausa Novel.

Aliyu yace” what! Aure! Ina bazan iya ba, bazaiyaba” Yana rufe baki idonshi ya sauka akan wani document yaga a rubuta Dr Aisha Ahmad, yaji gabashi ya fadi yace” Doctor Wana fa daga ina? Ya nuna document din dake kan table…

Fawaz Yayi Murmushi Yace” Document Din Dr Aisha Kenan Data Kware a Ko Wani Fanni Daya Dagaci Mata, Har Da Iri Matsaloli Iri Naka, India Su Riketa Ta Na Musu Aiki, Muna Bukatar Irisu Buddy Sun Dawo Gida Su Yi Aiki a Gida, Shiyasa Muka Dage Aka Subar Mana Ita Dakar Dai Suka Sake Mana Ita, Jibi Ma Zata Dawo Nigeria Zata Fara Aiki a National Hospital, Abun Mamaki Ma Fa She’s Just 24, Buddy Ya Kamata Kashirya Kaje Kai Da Suhaima Ta Dubaku, Buddy Kar Ka Cire Hope Kaje Gobe Zaka Fi Samu Ta Hankali a Kwance, Har Suhaima Ma Zata Magace Mata Ehhhh Kagane Ai”

Aliyu yayi murmushi yace” Ni fa na cire hope, na bar ma Allah komai, ina ne ba jeba, ama duk results din dayane am infertile , no buddy bari kawai ni ba inda zan Kara zuwa”

Fawaz daji haka baiyi kasa a gwiwa ba yata bashi baki da Karfi gwiwa har Aliyu ya Amince zashi”

“Ama ka shaida wannane na karshe , daga Wana Bara na Kara zuwa wani asibiti ba”

Fawaz yayi Jim jikishi yayi sanyi yasan halishi Sarai da kafiya bayada yaiya yace” eh Buddy, ama da Allah Kar ka gayama suhaima zaka india, ka bari sai ka Gama shiri sai ka gayama ta itama ta shirya”

Ya kalli fawaz fuska tuhuma yace” maiyasa?

Fawaz yace” please kawai dai kayi yanda nace , da Allah buddy?

Aliyu ya daga kafada yace” badamuwa naji zanyi yanda kace”

Fawaz yace” yawwa tom yanzu zakira asibiti na shirya muku appointment na gani ita doctor din, yanda muka shirya zan kiraka na sanar da Kai, da Allah buddy ka tafi da safe irisu 5 to 6 Dina”
.

Aliyu yayi murmushi ya rugumeshi yace” inshallah, thanks buddy “

” No Haba Dm Yiwa Kaine” Fawaz Ya Fada Yana Murmushi… Doctor Eesha Hausa Novel.

Yace” Toh Ni Zantafi, Ka Gyada Madam Da Boy Dina”

Fawaz Yace” Inshallah Zasuji”

Suka Fito Fawaz Ya Rakashi Har Baki Motar , Ya Shiga Aka Tada Motoci, Ciki Motar Yasa P.a Nashi Ya Shirya Mishi Flight to India Gobe Da Safe.. Ya Amsa Da Toh Yallabai Ba Matsala, Suna. Isa Gida Ya Tarda Suhaima Da Kaweyenta Maza Da Mata , Kamar Yanda Mami Ta Fada Kuwa,rawa Suke Tirkawa Kamar a Club, Sun Cika Gida Da Kara, Aliyu Na Shiga Kowa Yakama Kanshi, Dun Suna Shakashi Sosai, Suhaima Maganishi Tazo Ta Rugumeshi, Kamar Soko Ya Saki Mata Murmushi Tajashi Suka Haura Sama.

New Delhi

Washe Gari, Gari Na Gama Wayewa, Sadik Ne Ya Sauko Daga Kan Gado Baki Shi Dauke Da Addu’a Bacci, Tun Baya Ya Idar Da Sallah Asuba Kenan Ya Kwanta Sai Yanzu Ya Farka.. Mummy Shi Yagani Tsaye a Kanshi Tana Mishi Murmushi, Da Hindi Yayi Sauri Yace ” Shubh Prabhat Mummy “( Ina Kwana Mummy)

Essha Bata Amsaba Ta Bata Fuska Ta Kama Kunnuwashi Duka Biyu Har Sanda Yasa Kara, Tace” Sau Nawa Zan Gayama Kariga Gaisuwa Da Hausa Eye? Ina Kwana Zakace, Ina Kwannnnnaaa ” Taja Kwana.. Ta Turaci Take Magana, Dun Sadik Yafita Ji Hindi Sosai

Yarike kunne yace” Maaf kijeyega mum “(sorry mom)

Tace” ba hakuri zaka bani ba, yi gaisuwa Kuma da hausa” ta fada da turanci

Sadik Yace” Aap Isse Kaise Bolenga Mum ?( How Do You Prounance That Mum?)

Ta Kara ja kunne tace” wato inama fada yare Hindi na shine ka Kara fada ko? Toh fada Ina kwana zakace, oya fada”

Sadik yayi murmushi yace” En kwanaa mum” ya fadashi a Hindi tune..

Essha batayi niyya dariya ba, sanda ta dara , tana dariya tace” repeat what you just said?

Sadik ya zata yayi gwanita har da gyara murya yace” En Kwanaa mummy”

Essha ta sake fashewa da dariya ta zugureshi a Kai ..

Sadik Yana dariya shima ya Mike harda buga kirji yace” Chit mat karo, main hausa padhunga mum“(mum Kar kidamu zan koyi hausa).

Essha Naji Ya Fadi Haka Tayi Murmushi Ta Jawo Shi Gefeta Ya Zauna Da Turanci Tace” Sadik Kafi Munkoma Kaiya Koda Gaisuwa Ne Kar Granny Ka Tama Ka Dariya, Learn It Fast” Bata Gama Rufe Baki Ba Sai Ga Arudhati Tashigo Da Gudu Da Karami Gift Box a Hannu Ta Yana Kyalli Taisa Gaba Sadik Taije Akan Ciyarshi.

Tana murmushi tace” Janam diwas Mubarak Sadik (Happy birthday sadik) ta fada Tana boye daya hannuta na hagu.

Essha ta dafa Kai Tace”dole inakoma gida nasha fada da Daddy, gabadaya yaro baiji yareshi ni dai na banu, shame on me nasan duk laifi nane”

Sadik bai amsa Taya murna da Arundh tamishi ba ya Mike yana leka hannuta data boye a baya yace” woh Kai hai? (Mai kike boyewa)

Arudh Tayi Murmushi Tajashi Gefe Tasomishi Magana Kasa Kasa a Kunne Da Yare Tace” Sadik Yau Holi(Ranar Biki Kaloli) Kuma Mummyka Batason Yi Wasan Holi, Shine Nakawo Colours, Here Are the Colours” Ta Fitar Da Leda Da Ta Boye, Ta Bude Leda Tacigaba” Here Are Colours, Neela(Blue), Hara(Green), Gulabi (Pink) and Laal (Red) So Sadik Let’s Surprise Her With Holi Colours

Suka Nufo Essha Da Hankalita Na Kan Wayata, Guri Aiki Ne Aka Kirata Ta Amsa Kenan Bata Gamaji Abunda Zasu Fada Ba Taji Anzuba Mata Gari Colours a Jiki, Suka Hada Baki Guri Cewa” Happy Holi Festival Dr. Essha ” Suna Gama Fadi Haka Suka Fice a Guje..

Essha Takaici Duk Yakamata Ta Mike Ta Kalli Kanta a Mirror Taga Yanda Jikita Da Fuskata Ya Baci Da Colours Harda Wayata , Bama Iya Gane Fuskata Taja Tsaki, a Fusace Ta Bin Bayasu, Tana Fitar Taji Drums Ne Kawai Ke Tashi , Duk Abanta Street Da Gari Colours Kowa Sai Bidiri Akayi Saboda Murna Holi.

Ta Kara Ja Tsaki Zata Koma Ciki Kenan Ta Hango Sadik Can Tsakiy Titi, Duk Jikishi Da Rabin Fuskarshi Yabatashi Da Colours Ga Kuma Motar Na Ta Sharoro Gudu Zatayi Kanshi Da Sauri Essha Ta Karasa Ta Jayesh.

Dai dai lokaci da Aliyu dake cike motar ya zuge glass dayaga yaro da driver shi yakusa kadewa, isowarsu kenan sufito daga Airport, ba hanya a babba titituna duk yayi cikoso, shine suka biyo ta street dinsu Essha.

Aliyu Yadaga Kai Ya Kalli Sadik Kenan Sai Ga Arundh Tazo Da Guduta Ta Kara Watsa Musu Colours a Fuskokisu Har Ba’iya Gane Kamanisu.. Aliyu Sai Binsu Yake Da Kallo Gabashi Na Faduwa Yasa Hannu Zai Bude Motar, Suhaima Tayi Sauri Rike Handle Din Ta Tareshi Cike Da Gadara Tace” Haba Darling Ka Cika Tausayi Da Yawa, Kaga Fa Yaro Ba Abunda Yasameshi, Wasanshi Ma Yakeyi.

Kuma kasan hali indiyawana Basu da yarda” ta Kara ja murfi motar ta rufe..

Driver yace” yallabai kayi hakuri, sha’ani hanyoyi kenan a Delhi na sai hakuri”

Suhaima Taja Tsaki Tana Tsuke Fuskar Don Haushi Tafiyar Takeji , Tafiyar Yazomata a Bazata Bahakatasoba Dun Bata Shiryaba… Aliyu Har Suka Bar Layi Bai Bar Kallo Su Essha Ba, Yaso Ace Ya Sauka Kodan Yagasu, Baisan Maiyasa Ganisu Yasashi Ji Faduwar Gaba Ba.

Bada jimawaba suka isa haraba asibiti , babba tarba aka musu zuwa office din babba Doctor, su samu tarba cike da girmamawa, Essha kadai ake jira , bakita su karaso, sukira layi kanta duka baya shiga, babba Doctor yaba su hakuri na Rashi zuwa Doctor da zuka zo wurinta, yace shi zai dubasu”
Aliyu ya amsa badamuwa ” Babba doctor ya dubasu da kanshi, su Sha gwanje gwanje, suhaima hankalita duk a Tashe yake, tsora ya cika ranta fal, kamar zatayi kuka dun tasa asiri ta ya kusa tonuwa, tarasa sukuni kanta har wani zufa takeyi duk ssnyi Ac daya cika office din, baya likita yagama gwanje gwanje shi yace musu suyi hakuri su dawo gobe , dun karba results duk abunda yanuna zasuyi kokari sumusu aiki akai.

Suhaima taji haka taji wani sanyi aranta, ta shaida ma kanta cewa sai tayi abun da zai sa bara su dawo asibiti na ba gobe, dun dagani likita ya mata kwarjini bai da wasa gashi ya Soma tsufa , suka mike zasu fita kenan, Pooja tashigo rike da files a hannuta, tana gani Aliyu ta ware Ido mamaki da tsoro yasata zubar da files a kasa Hannu ta na Bari, dun mamaki ma kasam magana tayi.

Aliyu yatsaya Yana kallo ikon Allah yanda ta sare musu hanya ta Kuma kafeshi da Ido, baidamu ba don mata dayawa su Saba mishi haka, suhaima ta ja hannushi cike da kishi ta buge Pooja suka fice.

Pooja Kuwa Kamar Ankafata Kasan Motsi Tayi Tana Kallosu Suka Fice, Suna Fita Da Daddewa Ta Dawo Hayacita Tabin Bayasu Da Sauri, Kash Bata Ci Musu Ba, Koina Ta Duba Na Asibiti Basu , Ta Tsaya Shiru Ta Kasa Gasgata Abunda Tagani, Mai Kama Da Sadik Sak, Bambaci Kawai Daya Ne Shi Wana Babba Ne, Sadik Kuma Yaro Ne, Ai Da Sauri Ta Juya Ta Koma Office Din Babba Doctor Da Ya Dubasu Ta Tara Shima Bashi Har Ya Fice, Ta Bugi Table, Ta Kalli Gefe Daya Tana Tunani” Aya Wana Danagani Ba Maihafi Sadik Bane, Kai Ima Ba Papishi Bane Su Hada Dangi.

Kai Let Me Call Doctor” Ta Ciro Waya a Pocket Din Labcoat Ta , Ta Dialing Number Essha Yana Ta Ringing Ba’a Dauka Ba Tace” Oops Na Tuna Yau Birthday Din Sadik” Ta Fice Da Sauri Har Tana Tuntube Ta Isa Guri Motar Tajashi Zuwa Gida, Kafi Taisa Go Slow Ya Tare, Kamar Ace Ta Daga Kai Ta Hango Aliyu Ciki Motar, Pooja Ba Hali Taje Gurisu, Dun Har Suyi U_turn Zuwa Daya Titi, Saba Rudewa Ta Fitar Da Kai Tana Ta Kwala Mishi Da Suna Sadik , Sai Binta Ake Da Kallo, Aliyu Kam Ko Harka Gabashi Yakeyi Baimasan Tana Yi Ba Saboda Akwai Da Tazara a Tsakani Su.

Tana Kallo Motarsu Aliyu Ya Tashi Za Subar Wuri, Da Sauri Ta Bude Murfi Motar Zata Fito, Watar Motar Ta Kara Parker a Gefeta, Ba Hali Fitar Tana Kallo Motarsu Aliyu Ya Wuce… Pooja Kamar Tayi Kuka Tsabar Takaici , Hanya Su Na Budewa Da Sauri Tayi U_turn Tabi Baya Su, Haryanzu Ba Sa’a Dun Bata Cimasuba, Jiki a Sanyaye Taja Motar Ta Zuwa Gida.

Download Doctor Eesha Hausa Novel

[ads1]

[button color=”purple ” size=”medium” link=”https://hausacinema.com/wp-content/uploads/2022/11/doctor-eeshat-hausa-novel-by-hausa-cinema.txt” icon=”” target=”false” nofollow=”false”]Download TXT[/button] [button color=”green” size=”medium” link=”https://hausacinema.com/wp-content/uploads/2022/11/doctor-eeshat-hausa-novel-by-hausa-cinema.pdf” icon=”” target=”false” nofollow=”false”]Download PDF[/button]

[ads1]

Hausa Novels

Doctor Eesha Hausa Novel

Download Free Hausa Novels From Hausa Cinema.

 1. Jiddatul Khair Hausa Novel Complete
 2. Abdulmaleek Bobo Complete Hausa Novel
 3. Gidan Dadi Hausa Novel Complete Document
 4. Jihadi Hausa Novel Complete
 5. Yar Dandi Ce Hausa Novel Complete Document
 6. Gidan Uncle Return Hausa Novel [Sabon Salo]
 7. Fuska Uku Hausa Novel
 8. Kyawuna Jarabtata Hausa Novel
 9. Abban Sojoji Hausa Novel Complete
 10. Macijine Shi Complete Hausa Novel

4 thoughts on “Doctor Eesha Hausa Novel – Download Complete PDF Now”

 1. Pingback: Tsantsar Butulci Hausa Novel – Free Download Now - Hausa Cinema

 2. Pingback: Idan Bake Hausa Novel Complete Document – Download Now

 3. Pingback: Farrah Hausa Novel Complete Document – Free Download Now

 4. Pingback: Azima Da Aziza Macizai Ne Hausa Novel Complete - Get Now

Leave a Comment

Scroll to Top