Bidiyon Yadda Wani Matashi Ya Hau Kan Kabari Yana Zagi

‘Yan Sanda Sun Kama Matashin Da Ya Tsaya Kan Kabari Yana Ashariya A Kano

Rundunar Yan sanda a Jihar Kano sun Kama matashin Nan da ya raba kafa kan kabari Yana surfawa wata dattijuwa zagi sabida sunyi fada da Yar data Haifa Kuma Yana dauka a bidiyo.

A yau Lahadi ne a ka tashi da ganin wani faifan bidiyo a kafafen sadarwa na wani matashi da ya raba ƙafa s kan wani labari ya an ta surfa ashariya a waya, ya na kuma dauka a bidiyo.

Sai dai kuma tuni Abdullahi Ƴar-dubu ya shiga hannun ƴan sandan Caji-ofis ɗin Sharada, inda yanzu haka an tusa keyar sa zuwa shalkwatar ƴan sanda da ke Bompai.

Kakakin rundunar ƴan sanda ta Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da kama matashin, inda ya ce, tuni Mukaddashin Kwamishinan Ƴan Sanda,  DCP Abubakar Zubairu ya bawa DPO na Sharada, SP Abdulrahim Adamu umarnin a kamo wannan matashi.

Ya ƙara da cewa yanzu haka an kamoshi kuma an mikashi babbar shelkwatar rundunar yan sanda da ke bompai.

SP Kiyawa ya ce nan gaba kaɗan za a sanar wa da al’umma halin da a ke ciki.

Tuni dai al’umma su ka fara shi wa rundunar ƴan sandan albarka bisa tashi tsaye da ya ta kamo wannan matashin cikin ƙanƙanin lokaci, inda kuma su ka riƙa yi masa tofin alla-tsine.

Allah ubangiji yayi mana tsariu da dukkan sharrin shaidan da sharrin zuciya. Muna rokon Allah ya tsaremu daga sharrin duk wani abin ki da tozarci, Amin ya Allah.

Kar Kuce Bamu Fada Muku Ba, Zaku Iya Samun Zafafan Shirye-Shiryenmu A Shafin Hausa CinemaLitattafan Hausa (Hausa Novels), Wakokin Hausa (Hausa Music), Fina-Finan Hausa (Hausa Videos), Hotunan Hausawa (Hausa Photos), Labaran Hausa (Hausa News), Dama Abubuwan Ilimantarwa Ga Mutanenmu Hausawa (Hausa Education). Also, Like Our Page On Facebook Now.

2 thoughts on “Bidiyon Yadda Wani Matashi Ya Hau Kan Kabari Yana Zagi”

  1. Pingback: Na Yarda Ka Turo Pi A Matsayin Kudin Aurena – Budurwa – Hausa Cinema

  2. Pingback: Doctor Eesha Hausa Novel – Download Complete PDF Now

Leave a Comment

Scroll to Top