Hausa Novels

Bakar Inuwa Complete Hausa Novel – Download Now

Bakar Inuwa Hausa Novel Is A New Complete And Free Hausa Novel Which Is Written By Bilyn Abdul. You Can Now Download Bakar Inuwa Complete Free Hausa Novel Which Is Written In Zafafa Biyar Novel Series 2023. Furthermore, The File Are Of Two Formats PDF And TXT Files…

File NameBakar Inuwa Hausa Novel
TitleBakar Inuwa
Novel AuthorKhaleesat Haiydar
Novel GroupZafafa Biyar Novels
Novel GenreLove, Relationship
LanguageHausa
File TypePDF, TXT
File Size2.86MB
Total Words203,760
Total Pages758 Pages
Published DateJanuary 2023
KeywordsDownload Bakar Inuwa Complete Hausa Novel
Bakar Inuwa PDF Bakar Inuwa TXT 

Bakar Inuwa

Download Bakar Inuwa Hausa Novel Complete

A Ɓangaren Ramadhan Ma Da Duk Ƴan Gidansu Sunga Hirar Da Akai Da Alhaji Andi Ƙaura, Hakan Kuma Yasa Gimbiya Su’adah Jin Wa Ɗanta Zai Aura. Dan Tayi-Tayi Pa Ya Sanar Mata Dama Yaƙi. Sai Gashi Yau Taji A Shanun Ƴan Talla.

Cikin Lokaci Ƙanƙani Ta Birkice, Su Lubnah Na Tambayarta Amma Bata Sauraresu Ba. Da Suka Cigaba Da Damunta Ma Tsawa Ta Daka Musu Tai Wurgi Da Wayar Da Take Neman Fulani Taƙi Shiga Ta Fice Zuwa Sashen Pa Duk Da Yau Ba Itace Da Girki Ba. Zaune Ta Iskesa Shi Da Hajiya Mufida Sunata Hirarsu. A Kallo Ɗaya Da Sukai Mata Suka Fahimci Babu Lafiya. Dan Kowa A Gidan Yasan Shegen Girman Kai Da Isar Gimbiya Su’adah. Duk Da Tanada Tsananin Kishi Kishiya Bata Isa Fahimtar Komai Daga Garetaba.

Dan Batayin Wani Abu Da Za’a Samu Kafar Rainata, Ko Kallon Banza Bata Amince Zamanyi Da Kishiyaba Dan Tace Zubar Da Mutunci Ne. Hakan Kuwa Da Takeyi Yayi Tasiri, Dan Kame Kan Nata Yasa Ko Shirmensu Suke Yakan Tsayane Iya Su Biyu, Ballema Suma Ɗin Kowa Ji Take Da Kanta Abunka Da Kowa Ubanta Ya Tara Kuma Akwai Ilimi, Dama Hayaniyar Tasu Bata Wuce Ta Harara Ko Rainin Wayo Anama Juna Yatsine-Yatsine Ko Ɗaukar Kai.

Tsam Hajiya Mufida Ta Miƙe Tana Tattare Wayoyinta, Cike Da Kulawa Ta Dubi Pa. “Bara Nayo Shirin Barci Kafin Ku Kammala”.

 Kansa Kawai Ya Ɗaga Mata Idonsa Akan Gimbiya Su’adah Datai Zaman Ƙasaita A Gefensa Fuskarta Tamkar Zatayo Aman Wuta. Sai Da Ta Tabbatar Hajiya Mufida Ta Bar Sashen Saboda Akwai Cctv Da Ake Ganin Shiga Da Fitar Kowa Daga Nan Falon Sannan Ta Dubi Pa. Kafinma Tai Magana Yace, “Lafiya?”.

 Idanunta Da Suka Kaɗa Zuwa Ja Ta Zuba Masa, Cikin Son Nuna Isar Tata Tace, “Abban Ramadhan Ban Yarda Da Wannan Auren Na Ramadhan Ba”.

 Kansa Ya Ɗan Girgiza Ya Ɗauke Ya Maida Ga Tv. Sai Da Yaja Numfashi Ya Fesar Kafin Yace, “Komi Yasa?” Batare Da Ya Sake Kallonta Ba.

Bata Damu Da Yanda Yay Ɗin Ba, Cikin Kaushi Da Nuna A Wuya Take Tace, “Saboda Bata Dace Da Shi Ba. Taya Za’ace Duk Ƴaƴan Sarakunan Ƙasar Nan Dana Attajirai Da Masu Mulki Arasa Matar Da Za’a Bashi Ya Aura Sai Wannan?! Wad……”

  1. Aljanar Fatima Hausa Novel Complete PDF – Download 2023
  2. Download Masarautarmu Ce Hausa Novel
  3. Yan Harka Hausa Novel Complete [Free Download Now]
  4. Lalata Hausa Novel Complete Document [PDF Download Now]
  5. Gidan Dadi Hausa Novel Complete Document
  6. Gidan Uncle Hausa Novel Complete

Cikin Sauri Ya Dakatar Da Ita Ta Hanyar Ɗaga Mata Hannu. “Su’adah Bana Son Hayaniyar Banza. Shin Ɗanki Aure Bautar ALLAH Zaiyi? Ko Auren Kuɗi Ko Mulki?. Sannan Ma Ina Zuwa, Kina Nufin Bappi Bai Isa Zartar Da Hukunci Bane A Kan Ɗayanmu? Ita Yarinyar Kuma Kinsan Ƴar Waye Da Kike Wannan Hanƙoron.”

 Zatai Magana Ya Sake Dakatar Da Ita. “Karma Ki Ɓata Lokacinki A Banza. Babu Abinda Zai Hana Wannan Auren Sai Idan Ramadhan Ne Ya Mutu, Ko Ita Yarinyar Insha ALLAH”.

“To Ashe Kuwa Lallai Zata Mutun”.

Ta Faɗa A Harzuƙe Tana Miƙewa Zata Fice Batare Data San Katoɓara Da Suɓutar Bakin Da Tayiba. Wadda Ta Saka Pa Binta Da Kallo Ƙirjinsa Na Bugawa. (Gimbiya Su’adah Ta Manta Har Yanzu Akan Binciken Wanda Ya Kashe Matar Ramadhan Da Ƴarsa Akeyi, Tun Kuma A Wancan Lokacin An Tabbatar Musu Wanda Ya Ajiye Gubar Suka Sha Sai Dai Idan Yanada Alaƙa Dasu Ne Tunda Duk Wanda Yazo Birthday Ɗin Haseenah Makusancinsu Ne. Sannan Kafin Wancan Auren Ma Ta Nuna Borenta Na Ƙin Amnah Saboda Tanada Sikila).

“Ya ALLAH Mi Su’adah Keson Faɗa Ne?”.

Pa Ya Faɗa A Razane Yana Miƙewa Zaune Sosai. Zuciyarsa Fal Fargaban Kar Dai Su’adah Nada Alaƙa Da Kisan Amnah. Da Sauri Ya Girgiza Kansa. Dan A Halayenta Babu Mai Kamanceceniya Da Iya Kisan Rai. Barta Dai Da Gadara Da Girman Kai Wannan Kuma Ya Tabbatar Jinin Mulki Ne Ke Yawo A Jikinta. To Amma Miye Ma’anar Furucinta Na Yanzu? Anya Kuwa Babu Lauje Cikin Naɗi.

Hankalinsa Ya Tashi Matuƙa Da Wannan Tunane-Tunanen, Harta Kaisa Ga Fitowa Daga Sashen Zuwa Sashen Iyayensa. A Falo Ya Iske Su Harda Ƙannen Kakannin Nasa Su Inna Sunata Hira Hankalinau Kwance. Yanayinsa Ne Ya Saka Yafendo Tambayarsa Ko Lafiya?.

Da Ƙyar Ya Iya Haɗiye Kaso Sittin Cikin Ɗari Na Tashin Hankalin Daya Shigo Da Shi, Ya Ƙirƙiri Murmushin Dole Ya Aza A Fuska Yana Girgiza Kansa. “Ba Komai Yafendo, Dama Nazone Akan Batun Ramadhan”.

Bappi Ya Sauke Ajiyar Zuciya A Hankali, “Dama Muma Shi Muke Tattaunawa Anan, Dan Munga Dukan Hirar Da Akai Da Alhaji Andi Ƙaura, Nasan Kuma Itace Kaima Ta Hargitsoka. Karka Wani Damu, Dama Wannan Itace Siyasar, Duk Wani Abu Da Zasu Masa Yarfe Damu Kanmu Yanzu Bazasu Gajiya Wajen Bincikosa Ba. Sai Dai Mu Mun Riga Munsan Kanmu, Addu’a Kawai Za’a Dage Da Ita. Insha ALLAH A Cikin Satin Nan Za’a Kai Kuɗi A Tsaida Magana, Sai A Ɗaura Auran Bayan An Gama Zaɓe Hankalinmu Ya Kwanta.”

“Bappi Haka Shine Dai-Dai Amma Idan Son Samune Dama A Ɗaura Auren Kawai Yanzu, Sai Ta Cigaba Da Zama A Gidan Nasu Bayan Zaɓen Sai Ta Tare Ɗin”.

Ɗan Jimm Bappi Yay Yana Tunani, Kafin Yay Magana Anne Tace, “Ya Kamata Ku Fara Jin Ta Bakin Iyayenta Dai, Ku Basu Haƙƙinsu Har Sai Sun Yanke Muku Lokacin Da Sukaga Ya Dace Da Su. Da Campaign Da Zaɓe Har Zuwa Rantsarwa Inaga Watanni Uku Ne Zuwa Huɗu Ai. To Idan Kunji Ta Bakinsu Kunga Yayi Nisa Sai Ku Roƙi Alfarma. Kokuma Shi Uban Gayyar Ku Tuntuɓesa Ko Yanada Wani Lokaci Daya Tsara”.

Bappi Yace, “Masha ALLAH Hakan Yayi Kuwa. Insha ALLAH Zanyi Magana Da Ramadhan Ɗin Da Safe Idan ALLAH Ya Kaimu, Na Tabbatar Yanzu Yay Barci. Ni Bammasan Yanda Za’a Kwashe Da Shi Akan Wannan Barcin Wurin Ba Yanzun. Dan Kuwa Ba Nasa Bane Ba Barci Inhar Da Gaske Ƙasar NAYA Zai Riƙe Da Ƙyau”. Ƴar Dariya Suka Ɗanyi Su Duka.

Download Hausa Novels – Bakar Inuwa Bilyn Abdul Complete 2023.

Hausa Cinema

Hausa Cinema The Best Website In Africa Delivering The Latest News, Entertainment, Educational Articles And Many More About The Hausa People.

Related Articles