Hausa News

An Dakatar Da Yan Fim Daga Amfani Da Kayan Yan Sanda A Nigeria

Darektoci Sunyi Korafi Akan Wannan Sabon Doka

Dakatar Da Yan Fim Daga Amfani Da Kayan Yan Sanda A Najeria

Sanarwa Daga Babban Babban Sufeton Yan Sandan Nigeria Usman Baba Na Dakatar Da Yan Fim Daga Amfani Da Kayan Yan Sanda A Nigeria. Sufeton Ya Bada Umarnin Cewa Masu Shirya Fina-Finai Su Daina Amfani Da Kayan Yan Sanda Ko Na Sarakuna A Cikin Fina-Finansu Batare Da Izini Ba. Hakan Ya Farune A Jiya, 1 Ga Watan Augusta Bayan Wata Sanarwa Da Sufeton Ya Fitar.

Haka Zalika A Wata Sanarwa Ta Musamman Daga Kakakin Rundunar Yan Sanda Ta Kasa CSP Olumuyiwa Adejobi Ta Fitar Tace Kar Wani Dan Fim Ya Sake Bayyana Cewa Yan Sanda Basuda Mutunci Ko Makamancin Hakan, Don Haka Dole A Yanzu Duk Wanda Zai Shirya Fim Dinsa Ya Fara Neman Izini, Sai An Tantance Labarin Kafinnan Hukuma Su Bada Izini. Wanna Doka Kuwa Ba Iya Manyan Masana’antun Shirya Fim Ba Kamar Kannywood Ko Nollywood Ba. Hatta Kanananun Masana’antu Da Masu Shirya Comedy Sai Sun Nemi Umarni Kafinnan Su Gudanar Da Aikinsu.

Kamar Yadda Muka Sani Gabadaya Kungiyar Shirya Fina-Finan Kannywood A Nigeria Tana Amfani Da Wasu Saloli Daban-Daban Wajen Fadakar, Da Kuma Ilimantar Da Al’umma. Haka Zalika Kungiyar Tana Amfani Da Saloli Da Shiga Daban-Daban Wajen Wayar Da Kan Al’umma.

Koda Shike Tun Kafin Kafuwar Kannywood Din, Yan Wasan Hausa Na Shiga Daban-Daban Wajen Nishadantarwa, Fadakarwa Harma Da Ilimantarwa. Sukanyi Shiga Ta Kowane Irin Yare, Shiga Ta Jami’an Tsaro, Shiga Ta Masu Sarauta Da Sauransu Domin Inganta Ayyukansu.

Sai Dai Kuma A Wannan Karo,

Rahotanni Daga Nan Shafin BBC Hausa Na Nuni Da Yadda Yan Kannywood Din Sukayi Ta Cecekuce Akan Wannan Doka Ta Hanasu Yin Amafani Da Kakin Yan Sanda Da Akayi. Inda Manyan Darektocin Kannywood Kamarsu Aminu Saira Da Aminu S. Bono Suka Fito Suka Mayarda Martani Mai Zafi Akan Wannan Doka.

Menene Ra’ayinka Game Da Wannan Labarin? Zaka Iya Bayyana Mana Ra’ayinka A Wajen Comment.

An Dakatar Da Yan Fim Daga Amfani Da Kayan Yan Sanda A Nigeria

Kar Kuce Bamu Sanar Muku Ba, Zaku Iya Samun Zafafan Shirye-Shiryenmu A Shafin Hausa Cinema. Litattafan Hausa (Hausa Novels), Wakokin Hausa (Hausa Music), Fina-Finan Hausa (Hausa Videos), Hotunan Hausawa (Hausa Photos), Labaran Hausa (Hausa News), Dama Abubuwan Ilimantarwa Ga Mutanenmu Hausawa (Hausa Education).

5/5 - 3 Votes

Hausa Cinema

Hausa Cinema The Best Website In Africa Delivering The Latest News, Entertainment, Educational Articles And Many More About The Hausa People.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Related Articles