Hausa Articles

Abubuwa 10 Dake Tayarwa Mata Sha’awa – You Need To Know Now

A Wannan Makalar Mun Kawo Muku Abubuwan Dake Tayarwa Mata Sha’awa Da Kuma Yadda Ake Motsawa Mace Sha’awa Cikin Sauki. Saboda Haka Zamuyi Bayani Ne Akan Abubuwa 10 Dake Motsa Sha’awar Mace Batare Da Ka Kusance Ta Ba Ko Kuma Ka Taba Jikinta Ba.

Akwai Wasu Maza Da Suke Korafi Sossai Kuma Suke Turo Mana Tambayoyi Akan Yadda Ake Motsawa Mace Sha’awa Taji Tana Bukatar Namiji. Domin Akwai Mata Dayawa Da Sunyi Aure Amma Gabadaya Basu Jin Sha’awa, Wasu Lokutan Ma Kawai Mazajen Suna Saduwa Dasu Ne Kawai Saboda Biyan Bukata. Amma Asalin Abinda Yake Faruwa Shine Wadannan Matan Basu Jin Wani Feeling Na Ra’ayi. Wasu Matan Ma Kawai Suna Yarda Ne Saboda Haka Addini Ya Fada Cewa Idan Mijinki Ya Nemeki a Kwanciya Dole Ki Amsa.

Dalilin Da Yasa Sha’awar Mace Baya Tashi

Beautiful African Woman - Tayarwa Mata Sha'awa (Motsa Sha'awar Mace)

Kafin Muje Ga Asalin Bayanin Namu Akan Sha’awar Mace, Yana Da Kyau Mu Tamabaya; Wai Meyasa Sha’awar Mace Baya Tashi Ko Kuma Bata Jin Dadin Jima’i. Hakan Na Faruwa Ga Mata Dayawa, Shiyasa Muka Duba Muka Kawo Muku Wasu Daga Cikin Dalilan Da Mace Take Rasa Sha’awarta.

Damuwa

Damuwa Na Daya Daga Cikin Manyan Abubuwan Dake Sanya Mace Taji Ta Rasa Sha’awarta. Mata Suna Iya Rasa Sha’awarsu Idan Suna Cikin Wata Damuwar Da Ta Addabi Rayuwarsu. Don Haka Yana Da Kyau a Matsayinka Namiji Ka Ringa Kula Da Dukkan Damuwan Ta Ka Kuma Taimaka Mata Wajen Magance Su.

Rashin Fahimta

Idan Ya Kasance Akwai Rashin Fahimta Tsakanin Ka Da Mace to Dole Baza Ta Ji Sha’awarta Yana Tashi Ba Idan Kuna Tare. Watakila Bata Jin Dadin Jima’i Da Kai, Kuma Tana Boye Maka. Ko Kuma Dai Akwai Wani Abu a Tattare Da Kai Wanda Kwata-kwata Baya Sanya Taji Tana Son Mu’amala Da Kai. Bugu Da Kari, Idan Ya Kasance Baka Da Tsafta Dole Ta Kyamace Ka, Shiyasa Tsafta Yana Da Kyau, Yana Daga Cikin Addini.

Gajiya

Gajiya Na Daya Daga Cikin Abubuwan Da Suke Sanya Mace Taji Ta Rasa Feelings Dinta. Dole Idan Mace Tayi Aiki Ta Gaji, To Ta Samu Hutu Koda Na Awa Daya Ne Kafinnan Aci Gaba Daga Inda Aka Tsaya. A Wani Bincike Da Masana Sukayi, Sun Gano Cewa Gajiya Na Kara Karfin Hormone Cortisol, Wanda Sanadin Haka Yake Sanya Mace Taji Bata Jin Sha’awar Namiji Ya Kusance Ta.

Cin Zarafi Ko Fyade

Daga Cikin Abubuwa Dake Sanya Mace Taji Bata Sha’war Namiji Shine; Idan Ya Kasance an Taba Cin Zarafinta Ko Kuma Anyi Mata Fyade. Cin Zarafin Ka Iya Kasancewa an Kusance Ta Da Karfin Tsiya Anyi Mata Ba Dadi. Fyade Kuma Kamar Yadda Kowa Ya Sani Ana Amfani Ne Da Karfi a Biya Bukata, Wanda Ba Da Yardar Mace Ake Wannan Ba. Saboda Haka Duka Wadannan Abubuwa Suna Sanya Sha’awar Mace Ya Kwanta.

Rashin Lafiya

Rashin Kuzari Da Rashin Lafiya Yana Daga Cikin Babban Dalilin Dake Sanya Mace Ta Rasa Sha’awarta Baya Motsawa. Idan Ya Kasance Mace Bata Da Lafiya Musamman Ma Cututtuka Irinsu Ciwon Sugar, Ciwon Arthritis, Ciwon Zuciya Da Sauransu. Zaka Iya Gain Mace Tana Da Lafiya Tana Gabatar Da Ayyuka Amma Kuma Bata Da Sha’awa.

Shaye-Shaye

Idan Mace Tana Shaye-shaye to Tana Iya Rasa Sha’awarta Cikin Sauki. Musamman Ma Mata Masu Maye, Shan Giya Da Wasu Abubuwan Dake Bugarwa Na Haddasa Mace Taji Ta Rasa Sha’awarta.

Kallon Batsa

Kar Kayi Tunani Nunawa Matarka Batsa Ko Kuma Sanar Mata Da Cewa Kana Kallon Batsa Zai Taimaka. Akwai Wasu Mazan Da Ida Suka Zo Kwanciya Sai Su Kunna Batsa Su Nunawa Matan Saboda Suji Dadin Abun Su Kara Jin Sha’awa, Wannan Lalata Al’amari Yake. Muddin Zaka Kalli Batsa Da Matarka to Ba Zata Ji Dadi Ba, Domin Gani Zatayi Ita Bazata Iya Gamsar Da Kai Ba. Asalima Kallon Batsar Na Ragewa Mace Ko Namiji Feeling Dinsu.

Abubuwan Dake Tayarwa Mata Sha’awa

Kamshin Turare

Kamshin Turare Yana Matukar Sanya Mace Taji Feeling Dinta Sun Mota, Musamman Ma Idan Ya Kasance in a Cool Condition. Shiyasa Yana Da Kyau Ma’arata Su Kullanci Abota Da Turare Domin Yana Kara Dandano Da Jin Dadin Jima’i Sossai.

Yabo Da Kirari

Idan Kana Yaba Mace Ko Kana Yi Mata Kirari Zai Iya Sanya Taji Tana Bukatarka. Wannan Yabon Yana Taimakawa Wajen Karin Kauna Da Shauki. Sa’annan Kuma Ba Kowane Irin Yabo Zakayi Ba, Ka Fadi Abinda Yake Gaskiya, Ko Da Zakayi Kari Karka Yi Yadda Zata Fahimci Kawai Dadin Baki Kake Mata. Karkayi Yawa Da Kalamanka, Kar Kuma Suyi Kadan.

Sutura

Idan Kanason Matarka Taji Tana Sha’awarka Har Ta Fara Jin Sha’awarta Ya Tashi, Dole Kaima Ka Fara Burge Kanka. Wato Ka Kawata Kanka Ta Hanyar Yin Ado Da Kwalliya, Ta Yadda Idan Mace Ta Kalle Ka Zata Ji Kamar Ta Rungume Ka. Mata Suna Son Namiji Mai Sanya Sutura Da Kwalliya Kamar Dawisu, Suna Saurin Fadawa Namiji. [Danna Nan Ka Kalli 👉 Sabbin Styles Na Dinkin Maza Hausawa 2023].

Gajeren Wando

Shima Gajeren Wando Na Tayarwa Mace Sha’awa. Amma Kamar Yadda Mukayi Bayani a Baya Ya Kasance Kana Da Tsafta, Ba Wai Ka Bar Gajeren Wando Haka Da Datti Babu Tulare Ba Kuma Kana Tunanin Zaka Burge Mace Har Tayi Ra’ayin Tana Sonka. A Takaice Dai Gajeren Wando Shima Yana Sanya Mace Taji Sha’awar Ta Ya Motsa Tana Bukatar Namiji.

Kalaman Soyayya

Akwai Kalaman Soyayya Da Suke Sanya Mace Taji Tana Bukatar Namiji a Tare Da Ita Wanda Daga Baya Zata Fara Jin Sha’awar Ta Ya Motsa. Yawanci Wadanan Kalaman Soyayya Ana Amfani Dasu Ne a Sakwanni Ko Whatsapp Da Sauransu. Ba Lallai Bane Ka Iya Fada Mata a Bayyane.

Misali; Ina Wadannan Lallausan Lebanki? Zanso Ace Na Sumbace Su, Zanzo Ace Nida Ke Mun Kwanta Muna Hirar… Da Sauransu. Hira Na Ma’aurata, Ka Ringa Amfani Da Kalaman Soyayya Na Ma’aurata Wadanda Zasu Sanya Taji Tana Bukatar Ka. [Danna Nan Ka Karanta – Zafafan Kalaman Soyayya Na Ma’aurata 2023].

Kalaman Batsa

Generally Kalaman Batsa Ba Sai Mun Tsaya Bayani Ba. Kalaman Batsa Na Sanya Mace Taji Ta Rikice Ta Gigice Tana Bukatar Namiji. Ba Iya Mata Ba, Hatta Baza Idan Sukaji Kalaman Batsa Hankalin Su Tashi Yake Su Rikice Suji Suna Sha’awar Mace Ko Su Kwanta Da Mace. Amma Amfani Da Kalaman Batsa Wajen Tayarwa Mace Sha’awa Bashi Bane. Zakayi Amfani Da Wannan Hanya Ne Idan Ka Gagara Shawo Kanta, Sai Ka Fara Yi Mata Maganganu Kana Hadawa Da Kalaman Batsa. [Danna Nan Ka Karanta: Zafafan 👉 Litattafan Batsa Domin Karin Ilimin Jima’i].

Kifta Idanu

Ko Kasan Cewa Kifta Idanu Na Daga Cikin Body Language Dake Nuna Alamar Sha’wa. Ba Iya Mace Zaka Tayarwa Sha’awa Ba, Idan Mace Ta Kiftawa Namiji Idanu Shima Zai Ji Sha’awarsa Ta Tashi. To Haka Itama Mace, Zaka Iya Tayar Mata Da Sha’awa Ta Hanyar Kifta Mata Idanu Cikin Salo Mai Kyau.

Murmushi

Shima Murmushi Yana Sanya Mace Taji Tana Ra’ayin Namiji. Ta Hanyar Yiwa Matarka Murmushi Zata Ji Jikinta Na Kai Mata Sakon Yanayi Mai Dadi. Wanda Zai Iya Sanyawa Taji Sha’awarta Na Yana Tashi.

Kallo

Daga Cikin Abubuwan Da Suke Tayarwa Mace Sha’awa Akwai Kallo. Shima Kallo Yana Sanya Mace Taji Tana Bukatar Namiji. Amma Wasu Lokutan Kallo Yakan Zama Abun Haushi a Garesu, Musamman Idan Ya Kasance Bata Cikin Yanayi Mai Dadi.

Gashi

Gashi Yana Tayarwa Mace Sha’awa Ba Kadan Ba. Musamman Ma Gashin Kirji Da Saje (Beard). Wadansu Mata Suna Iya Fadawa Namiji Da Suka Lura Da Cewa Yana Da Baiwar Gashi. A Duk Lokacin Da Matarka Bata Cikin Sha’awa Kana Iya Bayyanar Mata Da Kyawawan Halittar Ka Na Gashi Domin Tayar Mata Da Sha’awa.

Kammalawa – Abubuwa 10 Dake Tayarwa Mata Sha’awa

Alhamdulillah, Da Fatan Bayanin Namu Ya Gamsar Da Mai Karatu Gamda Motsawar Shaawar Mace. Idan Kana Son Karin Bayani Ko Kana Da Tambaya Game Da Abubuwan Dake Tayarwa Mata Sha’awa Zaka Iya Yi Ta Comment Box Kai Tsaye. Kaci Gaba Da Ziyartar Shafin Hausa Cinema Domin Samun Litattafan Hausa, Labaran Hausa, Wakokin Hausa, Sirrin Ma’aurata, Kalaman Soyaya Da Kuma Ilimi Dangane Da Yanar Gizo.

4.7/5 - 12 Votes

Hausa Cinema

Hausa Cinema The Best Website In Africa Delivering The Latest News, Entertainment, Educational Articles And Many More About The Hausa People.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Related Articles