Hausa Novels

Abban Sojoji Takun Karshe Hausa Novel

You Can Read And Download Abban Sojoji Hausa Novel Takun Karshe By Boss Bature Complete.

TitleAbban Sojoji Takun Karshe
AuthorBoss Bature
GenreLove
File Size301KB
Total PagesUnknown
Date16 November
KeywordTakun Karshe

Kai tsaye sautin ringing ɗin wayar ya daki dodon kunnan Aunty babba dake baje saman gadonsu tana Bacci, a lokacin ko yatsanta bata jin xata iya motsawa saboda baccin dake a idanunta,yatsina fuska tayi alamar an takura mata.

Ishaq dake tsaye agaban mirror yana gyara jikinshi ya ɗan gyara murya tare da cewa”Madam ki daure ki tashi ki ɗaga kiran nan!da alama kira ne mai muhimmanci tun ɗazu wayar ke ta ringing,”

Uban tsoki Aunty babba ta buga tare da yunƙurawa daƙyar ta tashi daga zaune, jikinta na sanye da sleeping dress,riga da wando purple colour. Fuskar nan tayi suntum kamar wadda aka nausa,hannu takai tare da ɗaukar wayar dake ajiye saman bedside drawer, duba screen ɗin wayar tayi ganin sunan Hayaam ya bayyana yasa ta ƙara tamke fuska kamar ta shanu, ɗaga kiran tayi tare da kara wayar a kunnanta, rai a6ace tace “Meyasa kika kirani fitsararra! ko kin kira ne don ki ƙarasa yimun rashin kunyar taki don ubanki,” on the other hand hayam tace “haba aunty laila, ni harna manta da abunda ya faru atsakanin mu…..’

Tunkan hayaam ta ƙarasa maganar Aunty babba ta katse mata hanzarinta da cewa “Idan kin manta ae ni ban manta ba,Ki faɗamun uban miyasa kika kira ni, idan ba haka ba ni zan kashe wayar, Zuba mata ido Ishaq yayi yana kallonta aransa yace “Zagi kamar ƴar maguzawa,ko kunyata bata ji,sae faman ɗura ashar take yi,ni dae Allah ya haɗani da Guyaba.

Cike da damuwa hayaam ta sassauta muryarta, tare da cewa “Aunty laila, na shiga uku, ko ince mun shiga uku, Akwai gagarumar matsala, Gaba daya duk wani plan ɗinmu ya tashi aiki,’ Tunda Aunty babba taji hakan, gabanta ya faɗi rasss, ƙasa ƙasa da murya tayi tace “Hayaam meya faru? Wata irin matsala kike magana akai? “Aunty laila, Ashe yarinyar nan mai aikin gidansu, ɗiyar uncle ɗinsu ce Abusufyan!!!!!” tamkar saukar aradu haka aunty babba taji maganar Hayaam aikuwa a matuƙar gigice ta miƙe tsaye tana cewa “kutumar uba! inji ubanwa!yaushe Abusufyan ya ta6a aure.

Wlh ƙaryane koma wani ɗan ƙaniyar ne ya faɗi maki hakan babban maƙaryaci ne….’ Gaba daya hankalin ishaq ya dawo kanta,maganar dayaji tana fadi ta tsaya mashi aranshi, “Wani abusufyan din kuke magana akai”.

Firgit Aunty babba tayi tare da ware ido tana kallonshi sam ta manta da cewar yana acikin ɗakin, Hankali a matuƙar tashe ta miƙe tsaye da nufin ta fuce daga cikin ɗakin, Saboda tsabar ruɗu ta nufi hanyar shiga toilet.

Hausa Cinema

Hausa Cinema The Best Website In Africa Delivering The Latest News, Entertainment, Educational Articles And Many More About The Hausa People.

Leave a Reply

Related Articles