Hausa Novels

Abban Sojoji Hausa Novel Complete [Free Download Now]

Abban Sojoji Document And Audio Hausa Novel 2022

Abban Sojoji is a Hausa novel book written by Hafsat Bature popularly known as Boss Lady in 2022. The novel is among the most popular and top-rated Hausa novels in the world. Moreover, you can now download Abban Sojoji complete Hausa novel, Abban Sojoji Hausa Novel document in PDF and PDF format for free.

NameAbban Sojoji
AuthorHafsat Bature
GenreLove
PublisherHausa Cinema
Number Of Pages442
Book Size2.2MB
Date PublishedAugust 2022
LanguageHausa Language
Adult ContentNo
KeywordsAbban Sojoji Hausa Novel
Download Abban Sojoji Hausa Novel PDF

Download Abba Sojoji Hausa Novel

Abban Sojoji Hausa Novel

Abban Sojoji Hausa novel is here in PDF; you will just download the PDF to your phone and read it for free without any data charges. In addition, not only Abban Sojoji, you can also browse more of Hausa novels on Hausa Cinema and download them for free on your phone. You can check the list of Hausa Novels and choose the best one suited for you to download today. On the other hand, you can browse and read the hausa novel Online.

Abban Sojoji By Hafsat Bature

Hankali Motocin Nan Suka Shiga Dasu Zuwa Katafaren Gidan Goggonsu. Daga Ganin Yadda Motocin Nan Na Sojojin Nan Suka Zagaye Motar Da Suke Ciki Ko Shugaban Ƙasa Albarka.

Sunyi Shiru Cikin Motar,Ni’imtaccen Sanyin A.C Ne Kawai Ke Ratsa Sassan Jikinsu. Tsantsar Farin Ciki Ne A Fuskarsa. Ita Dai Jahad Sai Godiya Take Ma Allah Daya Kawo Musu Ƙarshen Wahalarsu Acikin Zuciyarta, Yayin Da Hosana Ke Ta Faman Zabga Murmushi Kamar Zautacciya.

A Tsakiyar Gidan Suka Tsaida Motocin, Da Sauri Major Ɗin Nan Dake Driving Ɗinsu, Ya Fito Tare Da Buɗe Musu Kopa, Riƙe Da Hannun Juna Suka Fito, Suna Bin Gidan Da Kallo Ya Haɗu Masha Allah,

 Major Ɗinne Ya Shiga Dasu Cikin Babban Falon, Saude Ce Ke Ta Faman Goge Goge, Tana Kakkabe Kujeru, Ɗagowa Tayi Jin Anyi Sallama.

Zuba Ma Yaran Ido Tayi Tana Kallonsu, Cikin Mamaki Ganin Tagwaye Kyawawan Gaske, Sam Ta Gaza Magana.

Sai Da Taji Muryar Major Ɗin Yana Cewa “Marshal Omar Ne Yace Akawo Su Nan, Shima Kuma Yana Nan Shigo Wa Da Anjima” Yana Gama Faɗan Hakan Ya Fice, Zuru Su Kayi Suna Tsoron Wata Irin Tarba Za’ayi Musu, Don Sun Lura Kamar Baƙin Jini Ne Dasu Kowa Baisan Su,

Ganin Matashiyar Ta Soma Sakin Murmushi A Fuskarta Yasa Su Suma Suka Ɗan Saki Fuska,

Cike Da Zumuɗi Takara Inda Suke Kamar Tasan Su, Ta Ruƙo Hannayen Su Tana Cewa “Masha Allah Ku Shigo Ciki Ku Zauna, Ku Saki Jikin Ki Ku”

Haka Saude Ta Ruƙo Hannunsu, Ta Zaunar Dasu Tare Da Cewa “Bari Na Kawo Muku Abunsha Ko”?

Cikin Sauri Hosana Tace “Ƴunwa Muke Ji…” Tunkan Taƙarasa Jahad Tasa Tafin Hannunta Ta Rufe Mata Baki, Tare Da Cewa “Hosana Banasan Wannan Abun, Daga Zuwa Gidan Mutane Kinsan Su Ne,”

Murmushi Saude Tayi Tare Da Cewa “Ba Yaya Omar Bane Yace Akawo Ku Nan Ba? Don Haka Ku Saki Jikin Ku Kamar Kuna Cikin Jirgi Mai Ya Ƙare”

Recommended: Jiddatul Khair Hausa Novel Complete.

“Sannan Naji Kince Batasan Mu, Ae Musulmi Ɗan Uwan Musulmi Ne, Akwai Sanayya Da Ƴan Uwantaka Ta Addinin Musulunci, Sannan Kuma Baƙon Ka Annabin Ki, Ku Baƙi Ne Dan Haka Zan Karramaku Sosai,

Saude Ta Karasa Maganar Tare Da Sa Hannu Ta Shafa Kan Hosana Tace “Kada Ki Damu Ƙanwata, Yanzu Nan Zan Kawo Miki Abinci Lafiyayye Ki Ci,”

“Nima Zanci,” Jahad Ta Faɗi Tare Da Sunnar Da Kai, Murmushi Saudat Tayi Tare Da Cewa “Shikenan Bari Nazo Ga Tv Nan Kuyi Kallo,” Tayi Maganar Tana Nuna Musu Plasman Dakw Manna A Bango, Sannan Ta Wuce Kitchen,

 Ajiyar Zuciya Suka Saki Atare Suna Ƙare Wa Haɗaɗɗen Falon Kallo,

“Hosana Dan Allah Ki Daina Zuba, Kina Bani Kunya Sometimes, Kin Ci Ka Ɗumi Daga Zuwa Gidan Mutane Sai Ki Fara Tambayar Abinci Kamar Mayya”?

 Harara Hosana Ta Watsa Mata Tare Da Cewa “Bani Ce Mayya Ba Kaɗai Kema Mayyar Ce, Saboda Ke Ma Ae Kince Zaki Ci, ” Tayi Maganar Tana Murguɗa Mata Baki, Jinjina Kai Kawai Jahad Tayi, Ba Yadda Zatayi Da Ita,

Shigowa Saude Tayi Hannunta Ɗauke Da Tray Ta Aza Katuwar Kula Aciki, Sai Plate Wit 2 Spoon, Gefe Kuma Jug Ne Mai Ɗauke Da Juice.

 Tunkan Ta Ƙaraso Hosana, Ta Sauko Ƙasan Carpet Ɗin Ta Zauna Tana Washe Baki,

 Ajiye Musu Tayi Tare Da Cewa “Yakamata Ku Wanke Hannayen Ku, Bari Na Kawo Muku Wurin Da Zaku Wanke,” Ta Faɗi Kafin Ta Juya Izuwa Cikin Kitchen Ɗin,” .

Buɗe Kular Hosana Tayi, Zaro Ido Tayi Tare Da Cewa “Lahh Ha Ilah Jahad!! Shinkafa Kaza Ce Wlh, Hada Wasilla Masu Yawa Wayyo Daɗi,” Shiru Jahad Tayi Batace Mata Komai Ba, Saboda Yunwar Da Take Ji,

Ji Su Kayi Bazasu Iya Jiran Saude Ba, Takawo Musu Ruwan Da Zasu Wanke Hannu Ba, Ai Kafin Saude Ta Fito Daga Kitchen Ɗin Tuni Hosana Ta Ɗauke Jug Da Plate Ɗin Dake Saman Tray Ɗin Ta Ajiyesu On Carpet Ɗin , Ta Ɗauki Kular Ta Zazzage Musu Farar Shinkafar Da Miyar Duka Acikin Tray Ɗin, Gaba Ɗaya Suka Sa Hannu Suka Motse Ta Suka Shiga Zubawa Cikinsu, Hannu Baka Hannu Ƙurya Kamar Wani Yace Zai Kwace Musu Abincin.

Recommended: Abdulmaleek Bobo Complete Hausa Novel.

 Tsaye Saude Tayi Akansu Tana Kallon Ikon Allah, Gashi Har Ta Ɗauko Musu Bottle Water Da Bowl Ɗin Da Zasu Washing Hands Ɗinsu Aciki, Tausayinsu Ne Yakamata, Alamu Sun Nuna Cewa Yaran Na Cikin Mawuyacin Hali Na Ƴunwa,

Kamar Wasu Kuraye Haka Suka Dinga, Zuba Uwar Loma Suna Ci, Allah Sarki Anjima Ba’a Haɗu Ba, Kitchen Saude Ta Koma Cups Da Dauko Musu.

👉 Idan Bake Hausa Novel Complete Document Download Now

 Ta Dawo Ta Zukunna Inda Suke, Tana Tsiyaya Musu Ruwan Bottle Ɗin Hannunta Mai Sanyi, Tunkan Ta Gama Hosana Ke Miƙa Mata Hannu Tana Cewa “Ruwa! Ruwa!!’ Wato Taci Taci Harya Shaƙe Mata Makoshinta,

Miƙa Mata Saude Tayi Cikin Sauri Ta Kar6e, Ta Kai Baki Tana Sha, Har Wani Sauti Throat Ɗin Ta Ke Badawa “Ƙut Ƙut Kut,

 “Hosana Nima Zan Sha In Kin Gama,” Jahad Ce Tayi Maganar Tana Yarfa Hannayenta, Cikin Sauri Saude Ta Zuba Mata Itama A Ɗayan Cup Ɗin Ta Miƙa Mata, Karba Tayi Tana Faɗin “Mungode”

 Zama Saude Tayi Kamar Ta Samu Tv Tana Kallonsu, Yadda Hosana Ta Dauki Cinyar Kaza, Ta Tura Acikin Baki Kamar Kura Ta Bata Tsoro, Amma Abun Mamaki Hada Ƙashin Ta Haɗa Duka Ta Taune, Zaro Ido Saude Tayi Cikin Tsoro Tana Cewa “Ki Ci A Hankali Dan Allah”

“Bazaki Gane Ba Aunty, Wlh Yunwa Muke Ji, Dan Allah In Akwai Sauran Abincin Ma Akwaso Mana Shi Duka Hada Ƙanzoma”

 Hosana Ce Tayi Maganar, Tana Ta Fama Lashe La66a, Mouth Ɗinta Yayi Dama Dama Da Jar Miya, Kamar Mayyar Dai”

 Jahad Dai Ba Baka Sai Kunne, Sam Bata Gane Da Wane Yare Suke Magana, Bata Ankare Ba Hosana Ta Ɗauke Tray Ɗin Duka Tasanya Harshenta Tana Lasa.

Recommended: Azima Da Aziza Macizai Ne Complete Hausa Novel.

 Ita Kanta Saude Batasan Time Ɗin Da Ta, Fashe Da Dariya Ba Hada Dafe Ciki, Sam Tagaza Stopping Kanta, Sae Da Tayi Mai Isarta, Sannan Ta Tashi Daker Tana Ci Gaba Da Dariyar Ta Amshi Tray Ɗin Dake Hannun Hosana Tana Cewa “Bari Na Zubo Muku Alkubus Da Miya Kuna So,”? Tayi Maganar Tana Kallonsu, Ae Har Haɗa Baki Suke Yi Wurin Cewa “Eh Komai Ma In Akwai Hada Ƙanzo Ma Azubo Mana Muna Ci Please , Mu Ko Ciyawa Ce In Dai Za’a Sama Ta Miya Muna So,”

 Dariya Kamar Zata Kashe Saude, Haka Ta Ɗauki Tray Ɗin Ta Wuce Dashi Kitchen, Duk Wannan Budirin Da Akeyi Goggon Katsina Bata Sani Ba, Tana Can Haye Saman Gadonta,Daga Sauraron Radio Bacci Ya Kwashe Ta,

 Sai Da Jahad Da Hosana Su Kayi Kulu Wash Rabu Hani’an , Sannan Suka Dawo Hayyacinsu, Sun Ƙarar Da Abincin Gidan Duka, Dole Saude Ta Ɗaura Wani Girkin,

 Bedroom Ɗinta Ta Shigar Dasu,Bin Ɗakin Su Kayi Da Kallo Komae Tsaf Ba Tarkacen Hauka, Sai Ƙamshi Ke Tashi, Daga Bed Sae Wardrobe, Ƴar Bedside Loka Da Sauransu,

 Toilet Ta Nuna Musu Tare Da Cewa “Nasan Zaku Buƙaci Yin Wanka, Ga Toilet Nan, Ku Cire Kayan Jikin Ku Naga Sun Tsufa Kuma Sunyi Datti, Kusanya Munsu Acikin Laudry Basket Ɗincan,” Tayi Maganar Tana Nuna Inda Basket Ɗin Yake Gefen Wardrobe Ɗinta.

Recommended: List Of Hausa Novels And Websites To Download For Free 2022.

 Sannan Tace ” Duk Abinda Baku Gane Ba Kuyi Mun Magana, Just Feel Free,”

“Mun Gode Sosai Aunty,” Acewar Jahad, Murmushi Saude Tasaki Tace “Kada Ku Samu Damuwa, Ni Zan Shiga Ciki,” Tayi Maganar Tare Da Fice Wa Daga Ɗakin,

“Wai !! Allah Hosana Kin Ga Yadda Allah Ke Ikonsa Ko? Mun Fita Daga Wancen Kurkukun Kaddarar (Next Novel) Ynx Gashi Zamu Fara Sabuwar Rayuwa Mai Kyau,”

Murmushi Kawai Hosana Ke Saki, Gaba Ɗaya Hankalinta Nakan Marshal Omar Duk In Ta Tuna Yadda Lamarin Ɗazu Ya Wakana Sai Taga Abun Kamar A Mafarki”

Sun Jima Suna Shiririta, Kafin Jahad Tafara Shiga Wanka, Komai Na Toilet Ɗin A Tsaftace, Ya Ji Tiles Har Jikin Bango, Shower Ce Ta Tsaye, Sai Kwandon Wanka, Mai Ɗauke Da Sabulu Mai Ƙamshi Da Lallausan Soso,

Bakomai Ya Burgeta Ba A Cikin Toilet Ɗinba Sai Shampoo Da Tagani Jere, Saman Mirror, Saboda Gashinsu Yayi Dauɗa, Duku-Duku Sai Uban Wari, Ga Ƙura, Murmushi Tasaki Cikin Sauri Ta Tu6e Rigar Jikinta Kamar Tsumma, Ta Yi Hanging Ɗinta Jikin Towel Holder.

Karanta: Labarin Soyayya – Read Complete Hausa Love Story Now

Baƙaramin Dauɗa Jahad Ta Fidda Ajikinta Ba, Sai Da Ta Wanke Ko’ina Tayi Shaving Gashin Under Ɗinta Dana Armpit Ɗinta Da Shaving Cream, Dogon Gashin Kanta Ma Yasha Wanki Da Shampoo,

 Zanso Ku Ga Yadda Jahad Ta Fito Daga Toilet Ɗinnan, Fesss Fesss Kamar Wadda Tayi Wanka Da Ruwan Zam Zam, Da Daurin Gaba Ta Fito, Towel Tasanya Ajikinta, Hannunta Kuma Na Riƙe Da Rigarta, Cikin Laundry Basket Tasanya Rigar Kamar Yadda Saude Ta Basu Umarnin,

 Sakin Baki Jahad Tayi Ganin Hosana Nata Faman Sharar Bacci A Tsakiyar Shimfidaɗen Gadon Saude, Girgiza Kai Tayi Tare Da Faɗin “Basa Ban Ba, Gida Babu Makwabta Babu Gidan Miji Ba Tabbas”

 (This Reminds Me Our Class Mates Allah Sarki, Wannan Sararsu Ce, Wato Daga Anyi Abu Sai Suce Gida Babu Makwabta Babu Gidan Miji Ba Tabbas).

Allah Sarki Hosana Dole Kiyi Bacci Baiwar Allah, Munyi Rayuwar Ƙunci Sosai, Yanzu Lokaci Ne Da Allah Ya Amshi Addu’armu, Zamuyi Rayuwa Ta Jin Daɗi Da Walwala,” Jahad Ce Tayi Wannan Maganar Sannan Ta Ƙarasa, Inda Hosanar Take, Ta Ɗan Russina Tare Da Sa Hannu Da Bubbuga Ta, ” Get Up Hosana, Bacci Bazai Yi Maki Daɗi Ba, Da Datti Ajikin Ki, Ki Tashi Please,” A Hankali Hosana Ke Buɗe Dara Daran Idanuwanta, Tana Lullumshe Su, Cikin Kasalalliyar Murya Tace ” Meyasa Kika Tashe Ni Dan Allah ! Bakiji Yadda Nake Ji Ba’

Recommended: Kyawuna Jarabtata Hausa Novel Complete.

“Sorry Hosana, Nasan Ba Daɗi Amma Ki Tashi Kije Ki Cire Dattin Dake Jikin Ki, Wlh Zakiji Wata Irin Ni’ima Mai Daɗin Gaske Na Shigarki, Ba Ki Ga Yadda Nayi Fess Ba”? Tayi Maganar Tana Jujjuya Mata Jikinta Don Tagani Dakyau,’

 Murmushi Hosana Tayi Daga Kwancen Da Take Tana Kallonta, Miƙa Mata Hannunta Tayi Tare Da Cewa “Please Taimakamin Na Tashi Kasala Nake Ji.

 

Hausa Cinema

Hausa Cinema The Best Website In Africa Delivering The Latest News, Entertainment, Educational Articles And Many More About The Hausa People.

9 Comments

  1. Great write-up, I’m normal visitor of one’s website, maintain up the excellent operate, and It is going to be a regular visitor for a lengthy time.

Leave a Reply

Related Articles