Abban Sojoji Book 3 PDF – Free Download Now 2023

You Can Now Get And Download Abban Sojoji Book 3 PDF Complete Hausa Novel And Read. Hafsat Bature Popularly Known As Boss Lady Is One Of The Best And Most Popular Online Hausa Novel Writers In The Year 2022. Although She Is A New Writer, Boss Lady At One Time Gained Fame As A Result Of The Book Abban Sojoji.
Read And Download Abban Sojoji Book 3
Kam-Kame Ta Shiga Yi Hankali A Tashe Tana Wurwurga Ido, “Wannan D’an Daudun Daga Ina Kuma Aka Samo Shi?” Daya Daga Cikinsu Ya Tambaya Yana Kallon Ta, Hantar Cikinta Ce Ta Ji Ta Kad’a, Su Duka Sauraren Ta Suke Yi Su Ji Mai Zata Ce?

Motsi Ta Soma Yi Da Lips Dinta Alamar Tana So Ta Ce Wani Abu “Amm… Amm..” Duk Ta Bi Ta Dabarbarce. Jin Muryar Azumi Yasa Sehrish Sauke Ajiyar Zuciya, Karasowa Ta Yi Tana Fadin “Afuwan Y’an Samari Ban Yi Maku Bayani Game Da Sabon D’an Aikin Da Aka Kawo Domin Ya Rinka Taya Ni Aiki Ba.”
Kasa Kunne Suka Yi Suna Sauraron Ta, Dafa Kafadar Sehrish Ta Yi Tare Da Cewa “Sunan Shi Tukur Daga Yau Zai Rinka Taya Ni Aikace Aikacen Cikin Gidannan.
Ta Kare Maganar Tana Kallon Kowannan Su, Tabe Baki Yyi Ba Tare Da Sunce Komai Ba Dama Haka Ta Yi Tsammani, Don Haka Taci Gaba Da Cewa “Tukur Bari Na Gabatarka Maka Da Kowannan Su Saboda Ka Kiyayi Zama Dasu,”Ita Dai Ba Ta Ce Komai Ba Saboda A Rud’e Take,
Azumi Ta Soma Gabatar Mata Da Su Daga Na Farko “Wadannan Biyun Da Ka Ke Gani Sune Tagwaye In Ka Lura Komai Nasu Iri D’aya, Suna Da Son Zolaya Musamman Idan Abun Mugunta Ne Sun Fi Auki A Nan Na Farkon Sunansa Jahan Shine Babba Sai Twin Brother Dinsa Ayaan”
Tana Gama Wa Dasu Ta Matsa Na Kusa Dasu Tace “Wannan Kuma Sunan Shi Kanal Yusif Sarkin Tsafta, Bai Cika Son Surutu Ba Kuma Baya Son Kallo, Na Gefensa Kuma Shine Khaleed Bai Da Matsala Shi Indai Za Ayi Masa Abunda Ya Ke So Ba Tare Da Ya Tambaya Ba.
Duk Sehrish Na Sauraron Wannan Bayanin Na Azmi, Bayan Ta Kammala Da Na Hannun Damarta Ta Koma Other Side Din Taci Gaba Da Cewa “Wannan Junaid Kenan Sarkin Murmushi, Duk Yadda Za’a Bata Mai Rai Baya Fushi Sai In An Kuresa. Yana Da Son Wasa Faran Faran Da Jama’a, Burinsa A Bashi Kulawa A Bangaren Ci Kuwa Ba’a Magana” Karasa Maganar Tayi Tana Y’ar Dariya, Shima Dariyar Yake Yi Haka Zalika Wasu Daga Cikinsu Sun D’an Murmusa.
Sehrish Tagane Sa Shine Wanda Ta Fara Zuba Ma Abinci Mai Kyakkyawan Murmushin Nan “N6a Kusa Da Shi Kuma Fawan Kusan Halinsu Daya Da Junaid, Sai Jabir Da Irfan Basu Da Matsala In Dai Ba Tsokanarsu Akayi Ba”
Murmushi Sehrish Tayi Taji Dadin Wannan Gabatarwar, Sai Dai Ranta Na Bata Cewa Wadannan Kananun Ne, Akwai Sauran Mutun Goma Daga Cikin Sojojin Da Basa Nan, Su Kuma Koya Zasu Kasance?
A Tare Da Azmi Suka Yi Saving Dinsu Abincin Har Suka Kammala Kowannnen Su Ya Kama Hanyar Makwancinsa, Tattara Plates Din Da Kulolin Sukayi A Tare Suka Kakkauda Komai Izuwa Ma’ajiyarsa. Daga Nan Sehrish Tayi Ma Azmi Sallama Ta Koma Bedroom Dinta. Tana Mai Jin Dadin Fara Kasancewarta A Wannan Awesome Family Din Babbar Damuwarta Shine. Da Tazo A Matsayin Namiji A Maimakon Mace Batasan Ya Abun Zai Kasance Ba Ranar Da Asirin Ta Ya Tonu.
Tunda Samu Gadon Nan Ta Haye Ta Soma Minshari Bata Kara Sanin Meke Wakana Ba Sai Da Tajiyo Kwankwasar Kopar Da Azumi Take Yi Mata. A Firgice Ta Farka Tana Neman Mayafin Da Take Nad’e Kanta Da Shi, Can Ta Hangosa Kasa Ashe Anan Tayi Wurgi Dashi, Daukowa Tayi Ta Hanzarta Daure Kanta Dashi. Sannan Ta Tashi Ta Nufi Kofan Ta Bude Mata, Fara’a Azmi Ta Sakar Mata “I am Sorry Na Katse Maka Bacci Ko Naga Ana Kiran Sallah Ne Raina Ya Bani Baka Yi Ba Nasan An Sha Gajiyar Tafiya Ga Aikin Da Mukayi Da Dare”
Cikin Y’ake Sehrish Tace “A’a Wlh Naji Dadi Da Ki Ka Tashe Ni Saboda Banyi Sallah Ba Amma Ynx Zanje Na Yi, Azumi Tace “Ok In Ka Kammala Karfe 7 Ka Fito Akwai Aikin Breakfast Na Jiran Mu” Reeshi Ta Amsa Da “Toh “Sa’annan Tajuya Ciki”
Cikin Sauri Ta Shiga Toilet, Sai Da Tafara Cire Gashin Bakin Da Aka Sa Mata Ta Tura Sa Cikin Aljihun Wandon Ta, Sannan Taje Bakin Fanfo Ta Daura Alwala, Ta Fito Tana Yarfa Hannun Ta, Hijabi Ta Dauko Ta Zura Sannan Ta Shimfid’a Kafet, Ta Soma Yin Sallar.
Bayan Ta Kammala Sallar Wata Irin Hamma Ta Rinka Ji, Ga Bacci Bai Ishe Ta Ba Ga Kuma Yunwa Don Jiya Da Daddare Bata Nemi Abincin Ba Gashi Available.
Recommended: Gidan Uncle Hausa Novel Complete Free Download Now
Agogon Dake Manne Jikin Bango Ta Kalla Akwai Sauran Lokaci Don Haka Sai Ta Baje Saman Sallayar Taci Gaba Sharar Bacci. Ba Ita Ta Tashi Ba Sai Wurin Karfe 9 Na Safe Hankali A Tashi Ta Wartsake, Ganin Cewa Wannan Ce Rana Ta Biyu Da Fara Aikinta Gashi Zata Fara Bada Matsala. Cikin Hanzari Ta Cire Hijab Dinta Ta Hada Da Kafet Din Sallan Ta Adana Su A Saman Gadonta, Sannan Ta Zaro Gashin Bakinta Da Take Likawa Ta Manna Sa A Fuskarta, Ta Gyara Nad’in Mayafin Kanta Ta Fi Ce.
Recommended: Azima Da Aziza Macizai Ne Hausa Novel Complete.
A Kitchen Ta Sami Azmi Ta Kammala Shirya Komai Na Kalacin Safen, Duk Sai Taji Ba Dadi Sukuku Ta Isa Gare Ta Ta Ce “Barka Da Safiya Nayi Laifi Dan Allah Ayimun Uziri” Babu Alamun Bacin Rai A Fuskar Azmi Ta Ce ” Karka Damu Tukur, Ba Wani Abu Nan Gaba Dae Aguji Yin Hakan”
Sehrish Ta Amsa Da Toh Insha Allah Yanzu Wani Aiki Zan Yi?
Recommended: Deen Hausa Novel Complete Document [Download PDF Now].
Ba Wani Aiki Kawai Abunda Ya Rage Ynx Kabi Bedrooms Din Kowannan Su Ka Sanar Dasu Su Fito Su Yi Breakfast Ya Kammalu,” Azmi Ta Karashe Maganarta Ta Tana Kallon Ta.
Cikin Zullumi Sehrish Ta Fita Ta Tunkari Jerin Dakunan Dake A Downstairs, Na Farko Ta Fara Kwankwasa Wa Shiru Ba’a Bude Ba, Kara Knocking Tayi Da Karfi. Har Sai Da Ya Isarwa Mai Dakin, Muryarsa Tajiyo Ashake Yana Cewa “Who’s Trying To Disturb Me? D’aga Murya Tayi Tare Da Cewa “Tukur Ne Sabon Mai Aiki”
Recommended: Lalata Hausa Novel Complete.
“Shigo Ciki” Ya Ba Ta Izni, Turo Kofar Tayi Tare Da Kutsa Kai Ciki. Har Cikin Ranta Dakin Ya Yi Mata Kyau Bedroom Kamar Na Mace Saboda Kyau Ga Tsafta Sabanin Wasu Mazan Da Idan Ka Shiga Dakunansu Kamar Wurin Safkar Y’an Gudun Hijra Saboda Tsaban Tarkace Da Har Mutsi.
“Idan Ka Kammala Kalle Kallen Naka Sai Ka Sanar Dani Abunda Ya Kawo Ka” Muryarsa Ce Ta Dirar Mata A Kunne Sai Lokacin Ta Mayar Da Idonta Akansa, Kwance Yake A Baje Saman Katafaren Gadonsa Rabin Jikinsa Yayi Covering Dinsa Da Lallausan Blanket, Yusif Kenan .
Cikin En Ina Sehrish Ta Ce “Am… Emm Dama An Kammala Breakfast Ne Shine Aunty Azmi Tace Nazo Na Sanar Daku.”
Ta Kammala Maganarta Ta Tana Wasa Da Yatsun Hannunta, Jin Shirun Bai Ce Komai Ba Ya Sa Ta Dagowa Ta Saci Kallonsa, Samun Shin Tayi Yana Yamutsa Fuska Alamar An Takura Masa Cikin Lallausar Muryarsa Ya Ce “Idan Ina Jin Yunwa Ai Ba Sai Anzo An Tayar Dani Ba Ni Zanzo Da Kaina Ciki Na Ne Ko Cikin Wani? Ya Tambaya Yana Kallon Ta.
Cikin Sauri Tace “Cikin Ka Ne” OK Fi Ce Ka Ban Wuri, Ya Fada Tare Da Jan Bargonsa Ya Idasa Rufe Face Dinsa. Kamar Wacce Kwai Ya Fashe Mawa A Kai Haka Ta Fita Salalau Salalau. A Cikin Ranta Kuwa Tana Jinjina Ma Isa Irin Tasa “Tab Aiki Y Ganni Ni Sehrish Daga Abun Arziki, Wannan Shi Ake Kira Da Samun Wuri Tusar Asuba. Allah Sarki Mukam Ya’yan Talakawa Don Uban Mutun Kar Allah Yasa Ya Nemi Abinci Har Rana Ta Fadi Ya Ga In Za’a A Damu Dashi Kasha Iya Barcinka Yunwa Ta Taso Ka, Ka Lallaba Ka Je Neman Kason Ka Wani Sa’in Ma An Manta Dakai, Su Kam Wadandannan Genius Din Bibiyarsu Akeyi Suzo Suci Suna Make Wa”
Recommended: Yadda Ake Duba BVN Number A MTN, Airtel, GLO 2023
Ta Karasa Tunanin Nata A Dai Dai Lokacin Da Tazo Kofar Dakin The Next Person, Knocking Tyi Bugu D’aya Taji Ance “Come In” Turo Kofan Tayi Ta Bude Samun Shi Tayi Zaune Saman Sallaya Jikinsa Sanye Da Jallabiya Ga Kur’ani Yana Karantawa Gwanin Burge W, Da Alama Wannan Zaiyi Saukin Kai A Cewarta.
“Barka Da Safiya Yallabai An Tashi Lafiya” Sai Da Ya Kai Aya Sannan Ya Juyo Ya Kalle Ta Ya Ce “Da Ban Tashi Lpy Ba Zaka Ganni Ina Karatun Qur’ani Ne? To Fah Ta Ambata Acikin Zuciyarta, Shin Mai Ya Kawo Ka Ma Tukunna ? Ya Tambaya Yana Kallon Ta A Matsayin Namiji.
Muryarta Na Rawa Tace “Dama An Kammala Breakfast Ne Shine…..” Interrupting Dinta Yayi Tare Da Cewa “Shine Me? Kai Shashashan Ina Ne Da Zaka Fadowa Mutun Haka Kawai Tunda Sanyin Safiya, Kama Hanya Ka Fi Ce Tunkan Nayi Football Dakai” (Jahan).
Jiki Na Rawa Sehrish Ta Fi Ce Zuciyarta Na Bugawa Saboda Tsananin Tsoro, Dafe Kirjinta Tayi Domin Ta Samu Natsuwar Karasawa Ga Daki Na Gaba. Zullumin Ta Kar Asamu Wanda Zai Kai Mata Duka Don Ta Lura Cewa Fusatattu Ne, Ba Mai Sauki A Cikinsu Farawa Da Iyawa Ta Fara Fuskantar Haka Nan Gaba Batasan Mezai Biyu Baya Ba.
Next Room Kwankwasa Tayi Tana Jira Taji An Bata Iznin Shiga Amma Shiru, Sake Buga Kofan Tayi Da D’an Karfi Da Alama Kowanane Mamallakin Dakin Nan Ya Datse Kofar Ne. Jin Alamar Ana Tunkaro Kofar Yasa Ta Natsuwa, Bude Kofar Yayi Fuskar Nan A Daure Kamar Alkubus “Lafiya”? Ya Ambata Rai A Bace.
Har Ta Bud’e Baki Zata Yi Magana Tajiyo Muryar Wani Daga Can Cikin Ɗakin Yana Cewa “Wai Wane Ne”?
“Wannan Shashashan Sabon Mai Aikin Ne” Wanda Ke Tsaye A Gabanta Ne Ya Basa Amsa, Sai Lokacin Ta Gane Cewa Dakin Twins Ne Wato Kamar Yadda Suke Y’an Biyu Haka Ma Wurin Kwanansu D’aya” Tuni Taji Zufa Ta Ke To Mata Ganin Wancan Dake Daga Ciki Ya Taso, Dukkan Su Sleeping Dress Ne Riga Da Wando Ajikinsu Kala Daya Milk Colour Masu Kyan Gaske.

Read And Download Hausa Novels PDF
- Fansar Budurcina Hausa Novel Complete PDF Document
- Yan Harka Hausa Novel Complete [Free Download Now]
- List Of Hausa Novels And Websites To Download For Free 2023
- Download Best And Complete Hausa Novels 2023
- Takun Saka Hausa Novel Complete Document By Bilyn Abdull
- Saran Boye Hausa Novel Complete
- Heedayah Hausa Novel Complete Download – Khaleesat Haiyder
- Tsintacciya Hausa Novel Complete Document [Download Now]
- Macijine Shi Complete Hausa Novel Download Now
- Yadda Ake Rubuta Wasika Da Hausa
One Comment